Sashe 170
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Ta bishi da kallo tana jin haushinsa daman tun da cikin ya tsofa take ta jin haushin mutane, ko ido aka kura mata sai ya zama laifi, sai kuma takalar cikin take idan bata ji motsinsa ba sai ta hannu ta rika laguda tana takalarsa, idan kuma ya motsa mata da karfi sai tace ya taba mata hanji ta fara kuka tana cewa ciwo.
Haka dai Shattima yai ta fama har ta wuce kwanakin haihuwarta da kwana biyu sannan ta fara nakuda, a nan ta gane ashe wacan ciwon duk sharar fage tai yanzu ne na gaske yake tafe, idan marar ta murda mata sai ta ji kamar ba a duniya take ba, tun kamin ta shiga watan haihuwarta Shattima ya shirya mata komai na haihuwa a gida, har sai idan abun ya garara tukuna ya tafi da ita asibiti, sai dai baya barinta ita kadai idan zai fita hadimai za su zauna da ita saboda bukatu na yau da gobe da kuma gudun wata matsalar.
Ihu babu kalar wanda batai ba tun tana da kuzarin ihun har ta koma ta na ambaton Allah, tana fadin ba zata sake haihuwa ba.
“Ba zan sake haihuwa ba har abada, har abada ba zan sake haihuwa ba�
Shattima ya zo kusa da ita ya kwanto yana shafa kanta
“Pushhhhh�
Sai ta buge masa kai.
“Ba zan yi ba, pushing din ba, ai duk kai ne kai yi kai ka ja min, wayyo uwata wayyo ubana, Wallahi ba zan sake haihuwa ba�
Ya tsorata sosai a lokacin da ya ga ta daina unkurin yin nishin gudun kar ta kashe masa abun da ke cikin cikinta. Sai da yai da gaske sannan ta ni wani karfi ya zo mata daga gurin Allah yai nishi dai yunkuri sai ga kai ya fara fitowa, tanayin na biyu sai Shattima ya saka hannunsa ya janyo baby yana murmushi da hawaye a lokaci daya, ya saka alkamshi ya yanke cibiyar, ita ma a lokacin ne ta samu damar yin kuka mai hawaye domin a can da kukan kawai take ba hawaye, sai ta ji wani shauki yana ratsata babyn dake hannun Shattima sai kuka take tana jin kuka har cikin ranta, Shattima ya lullube ta da zane sannan ya sumbance ta ya kwantar mata da ita a jikinta.
“I love you so much�
Ya fada yana kissing din Fadime, hawaye na sauko masa, ita ma hawayen take tana murmushin da bata san ta ina yake zuwa mata ba, saboda joyful na uwa.
“Wa ta biyo? Mace ce ko Namiji?�
“Mace�
Ya fada yana shafa fuskarta, a tunaninta shikenan tun da ta haihu duk zancen da Shattima yake mata cewar yan biyu ne bata yarda ba a tunaninta yana mata wasa ne saboda ya san tana son yan biyu, sai da ta ji wata nakudar ta taso mata ta musamman, sannan Shattima ya fita ya bada Babyn wa mutanen da suke falo aka fara karba karba ana yabawa, shi kuma ya shiga wani sabon aikin, da taimakon Allah ta sake santalo danta yana kuka kamar yadda mace take. Za ku ga murna gurin Shattima kamar yanzu ne ya fara samun haihuwa.
Sai da ya gyara matarsa ya kwashe komai sannan ya shiga bandakin da ita ta gyara jikinsa ya fito ita kuma Jekadiya ta shiga yi mata nata aikin na kula da jikinta.
Da kansa ya buga ya fadawa Ammy da Inna cewar Fadime ta sauka, Inna sai ta ji kamar tai tsalle ta tafi, tana ta mamakin yadda akai Fadime tai iya karfin halin haihuwa domin ta san yarta da raki, gashi bata da halin zuwa domin Fadime kamar yar fari take a gurinta kuma kunya da al'adarsu ta fulani ba zata bari ta tafi ba, sai dai kenanta aka tura da wata yar uwar Bappa.
  Hankalinta be kwanta ba har sai da ta ji muryar yarta a waya tana labarta yadda akai ta haihu.
“Inna da kaina na haihu Wallahi, amman akwai wuya ba zan sake ba, Inna haka kika ji kema�
Inna ta yi murmushi idonta na cika da kwalla. Sai kuma Fadime ta fashe da kuka farinciki.
“Inna na zama uwa... Nima na zama uwa....�
Inna ta lumshe ido hawaye na sauko mata.
“Allah ya baki ikon tarbiyantarwa, ya raya miki su yasa masu jinkanki ne�
“Amin Inna, ke ma Allah ya saka miki da alheri dawainiyar da kika yi da ni da rashin da na yi miki Allah ya biyaki da aljanna�
“Ameen�
Shattima ya shafa fuskar matarsa yana jin kamar ya hadeye ta tsabar kaunarta da yake. Gurin ba da nono sai ido ya raina fata ashe a nan ma akwai wani zafin ba haka nan kurun ake bawa yaro nono ba, sai an yi da gaske sannan take shayar da yaran.
 Wani irin kula da tarairaiya ake bata kamar akanta kadai aka fara samun jika a masarautar, domin kwananta daya aka rabota da gidan Shattima aka dawo da ita masarautar, duk yadda Inna ta so ta ki zuwa bata samu hakan ba domin Ammy ta matsa mata kuma ta aika musu da komai na zuwa, ganin Ammy an wuce wannan karnin da ake cewa uwa tana kunya sosai da har zai hanata zuwa bikin yarta, bayan kuma babu abun da ya tafi so a wannan lokacin kamar gatan mahaifiyarta.
 Irin wulakancin da akai ma nera a ranar suna sai ka rantse da Allah daga sama ake jefo musu kudi, domin bidi'ar da kai a gurin sunan ba ayi irinta ba a gurin aurensu, namijin aka saka masa sunan Mai Martaba Abdallah, mace kuma ta ci sunan Inna Aisha, sai dai dukansu ana musu lakani da Ameer da Ameera.
ZAINAB POV.