← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 172

Sashe 132

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya fada idonsa cike da hawaye domin har ga Allah ya san ya saka mahaifiyarsa a damuwa. Haka ya gaji da rokomta ya gaji da magiya ya mike tsaye ya fice tana ta innalillahi.
Cikin motarsa ya koma ya zauna ya dafe kansa ya rasa abun da zai yi, ya rasa inda zai saka ransa ya ji, ya rasa abun da zai yi ya samu sassauci. Kunna motar yai ya juya kanta ya fice daga gidan gaba daya.

Sai da ya fita sannan Hajiya Babba ta tashi ta fito daga dakinta ta zauna a falo, ta maida hankalinta gurin tv tana kallo, ba dan babu plasma a dakinta ba, sai dan jin da tai dakin ma ta fita daga kanta gaba daya, gashi ta kasa cire talkaminta ta kasa aje jakar balle kuma mayafi komai da ta fita da shi yana nan jikinta.
Plasma take kallo sai dai ina damuwar da take ciki ta hana ta gane mutane ne a tv ko aljanu ko kuma cartoon? Kallo kawai take saboda ta gusar da abun da ya tsaya mata a zuciya, amman ta kasa abun ya shiga zuciyarta sosai ya danne mata komai ciki har da kalamai da take jin kamar ta kai wa'adinsu.

“Hajiya ga ruwa�

Kausar ta mika mata ruwa a kofi cike da damuwa. Hannu Hajiya ya mika ta karbi ruwan ta kai bakinta kwarara ruwan tai cikin bakinta da zimmar sha sai ta gagara hadewa tana zubawa a bakin suna dawo mata suna jika tufafinta.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Anty Karima zo..�

Kausar ta fada tana fashewa da kuka. Sai Hajiya ta kalleta irin duban nan na me ya faru? Is like kamar bata san ta yi ba. Karima ta karaso gurin da sauri tana kallon Hajiya.

“Me ya faru?�

“Ruwa na bata ta sha yadda ta sha haka yake dawowa a jikinta�

Kausar ta fada cikin kuka da tashin hankali.

“Innalillahi Hajiya�

Hajiya ta kalli Karima amman ta kasa amsawa.

“Taso mu je daki�

Karima ta rika hannunta sai Hajiya Babba ta mike tsaye kamar wata yar yarinya ta bi Karima zuwa dakinta, Karima ta zaunar da ita saman gadonta ta cire mata takalmin yayinda Kausar ta karbi jakarta ta da mayafinta ta aje a muhallinsu.

“Hajiya ki kwanta�

Da sauri Hajiya ta kwanta kamar mai jiran umarni. Karima ya fito cikin tashin hankali ta nufi dakinta ta dauko wayarta ta kira yar'uwarta Jurry ta fada mata abun da ya faru, cikin mintunan da ba su fi talatin ba Jurry ta iso gidan sai wani huci take tama fusata tana karawa.

“Haba ai dole Hajiya ki shiga wannan yanayin, yanzu fisabillahi Ya Sirleem da kansa zai dauki wuka ya daba miki? Da kansa zai jefe ki a wannan halin�

Jurry ta fada tana zaune kusa da Hajiya, Kausar kam sai rusar kuka take, Karima ce mai gaya ta ita ma tana hawaye.

“Wallahi Ya Sirleem be kyauta ba, yanzu ai ya ji dadi mahaifiyarsa tana cikin damuwa, ban san abun da suka gani a jikin yarinyar ba, kuma ko zai aureta ai ya kamata ya fadawa Hajiya ni na san ba zata hana shi ba�

Jurry ta juya ta kalli mahaifiyarta.

“Hajiya ta shi ki ji�

Hajiya ta tashi zaune kamar mai jiran umarni. Hakan da tai ba karamin mamaki ya ba yayanta ba.

“Hajiya karki sa wannan abun a ranki, ki kyale shi ki cire shi daga jerin yayanki, ki manta da rayuwarsa, ki na da mu kuma mun isheki da yardar Allah, na san dole za ki shiga damuwa ace danka ne zai maka haka�

Jurry ta fada hawaye na cika idonta, Hajiya ta kalleta har lokacin bata iya cewa komai bakin ya mata nauyi a gurin kalami, ko numfashi da ace ta baki take yinsa da bata samu damar fitar da shi ba.

FALMATA POV.

Karasawa tai gaban hoton ta kai hannu ta ta shafa fuskar matar da ke jikin hoton idanuwanta na cika da kwalla, sai kuma ta juyo tama karewa dakin kallo, can kuma ta sake maida dubanta gurin hoton hawaye na sauko mata, miya kawo hoton mahaifiyarta a nan? Ta tambayi kanta tambayar da bata da amsar ta, mikewa tai tsaye wanda hakan yai daidai da shigowar Momy a dakin cike da tunani kala, domin ta kasa natsuwa tana son ta ji abun da yake faruwa, hakan yasa ta zabi tambayar Falmata, domin zuciyarta na raya mata ba a daura auren ba Sirleem. Maida kofar dakin tai ta rufe da makulli. Falmata ta juyo tana kallonta hawaye na mata zuba.

“Wai me ya faru ne? Su waye za su zo da Sirleem yace idan sun zo kar na bada ke?�

Falmata ta nuna hoton mahaifiyarta tana hawaye.

“Waye kawo hoton nan a nan?�

Momy ta dan leka bayan Falmata ta hango hoton.

“Me ya faru?�

“Mahaifiyata ce�

“Ma ma..ma...Mahaifiyarki?�

“Mahaifiyarki?�

Momy ta sake maimaitawa.

“Duba hoton dai da kyau ki gani�

“Mama ta ce Momy, babu inda zan ga mahaifiyata ban gane ta ba, ni ma ina da irin hoto�

“Anya dai? Mahaifiyarki Falmata ko dai kamanni? Wannan ai Safiyya ce�

Falmata ta daga kai tana hawaye.

“Eh ita ce... Mamata ce�

Momy ta sake kallon Falmata da duba na mamaki da al'ajab.

“Wannan fa mahaifiyar Ameer ce... Dan mijina, wannna matar mijina ce ta biyu wanda ya aura tun da dadewa su ka rabu....�

Falmata ta lumshe ido hawaye na sauko mata. Momy ta karaso kusa da ita ta da fa kafadunta tana girgiza ta.

“Ta ya zan yarda da ke? Ta ya zan yarda mahaifiyarki ce?�

“Sunan da kika fadi sunanta ne, kuma ina da irin wacan hoton, mahaifiyata ta ce ta ba ni, ta ce tun tana budurwa ta dauki hoton, a lokacin da samari su ke bawa yan mata kudi su ce su je su yi hoto, ta fada min hoton guda gudu ne wanda ya saka ta dauki hoton mijinta ne na farko ya rike biyu ya bata biyu, kuma tabbas mahaifiyata ta auri wani namijin kamin ta auri Babana, har ta haifi yara biyu da shi mace da namiji macen Maryam da sai namijin Usman wanda ya bata, Maryam din kuma ta rasu...�

Falmata ta fada idonta a rufe cikin kuka mai karfi, lokaci daya Momy ta dauke hannayenta daga jikin Falmata tai baya baya tana kallonta kamar wanda tai arba da wani abun tsoro, tabbas abubuwan da Falmata ta fada haka ne, domin mijinta ya fada mata ya haifi yara biyu da ita dayar ta rasu kuma sunanta Maryam kuma ya fadawa Ameer yadda aka dauki hoton a lokacin da Ameer yake tambayarsa wacece ta jikin hoton da mahaifinsa ya ba Momy yace ta aje masa, sanadin hakan yai kai aka kara gyara masa hoton aka maida shi babba ya saka a dakinsa.

“Hakan na nufin ke da Ameer ....�

Momy ta kasa karasawa sai nuna Falmata take, jin hakan ya sa Falmata ta bude idonta da su kai ja saboda kuka ta kalli Momy.

“Wane Ameer din?�

“Dan...dan...mijina... Allah sarki Ameer... Ashe baka da rabon ganin mahaifiyarka a fili?�

Falmata ta dafa zuciyarta tana tuna waye Ameer din, the first thing da ya fara zuwa mata after tuna shi shi ne lokacin da zai je makaranta ita kuma Sirleem ya shigo da ita cikin gidan, irin maganar da yai mata da kuma yadda ya labarta mata batan mahaifiyarsa da fatan ganinta da yake. Sauri daga kai tai tana kallon katon hotonsa da ke manne a bango ta saka dayan hannu ta rufe bakinta da sauri hawaye na sauko mata. Momy ma hawayen take sai ta juya dafe da zuciyarta ta fice daga dakin, Falmata kan kurawa hotonsa ido tai sosai yayi murmushi yana sanye da suit red, sai a yanzu take ganin kamanin mahaifiyarta a fuskarsa da bakin fatarsa wanda ita ma shi ya haska fatarta.

Tana tsaye a dakin Sirleem ya shigo, yadda yake tafiya kadai da yanayin fuskarsa ya isa ya sanar maka cewar a yau kam ya amsa sunansa na maraya. Karaso yai kusa da Falmata ya saka hannayensa ya jata jikinsa ya rumgume, sai ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi jikinta na karkarwa, abubuwa biyu sun zo mata a lokaci daya, shi ma lumshe ido yai yana maida numfashi a hankali sai hawaye masu zafi suka sauko masa.

IYA POV.

Ganin tai kamar be kamata ta aikatawar da wannan aikin a yanzu ba, bata da tabbacin burinta zai cika ko aa, idan har Shattima be auri Zainab ba ko da ya zama sarki aikin banza ne a gurinta domin ba zata mori komai ba gashi yanzu ma ta bar gidan.
Daukar zare tai ta nade kurwar ta dukawa ta maida kurwar cikin kwaryar ta sannan ta maida kwaryar karkashin gado, ta gyara komai yadda yake, kana ta dauki kuwarwar Maijidda ta fito da ita daga dakin, kicin ta shiga ta dauko wata robar ta saka ta tabarar a ciki ta fara fige gashin jikin tantabarar da hanunta, bayan ta gama ta kunna risho domin ta fi gane yin girki da shi sama da gas.
Sai da ta yanka naman tantabarar sannan ta zuba shi a tukunya ta zuba mai kadan ta dora tukunyar a risho, bayan yayi zafi ta soma soyawa, sai da ta soye abun ta rumus yadda take son naman sannan ta kwashe ta sauke tukunyar ta kashe rishon ta dauko namanta ta zuba a wata kula ta rufe ta dawo dakinta ta boyeshi a karkashin gado. Sannan ta koma kicin din ta juye man da tai soyar da shi a wani karamin roba ta gyara kicin din ta wanke komai kamar bata taba ba. Kwankwasar kofar falon da ta ji ana yi ne yasa tai saurin fitowa daga kicin din ta je dakinta ta boye man sannan ta fito ta bude kofar, ganin Zainab ba karamin mamaki tai ba.

“Kin dawo kuma?�

Zainab bata ce mata komai ba ta raba gefenta ta wuce cikin falon, Iya ta rufe kofar ta juyo tana fadin.

“Ya akai wai miyasa ya aka rike ki?�

Sai da Zainab ta isa bakin kofar dakinta sannan ta juyo ta kalli Iya a jigace.
Chapter 132 · 0% Book details