← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 172

Sashe 18

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta unkura zata tashi ta ji ba zata iya ba, hakan yasa ta koma ta kwanta a kasan ta rike kunnuwanta tana wani irin kuka mai shiga zuciya. Tumba ta nufi inda take ta rika tana kuka kamar ba ita ta kitsa komai ba, kokarin dagata take amman Falmata ta kasa tashi sai kuka take. Mutane wasu na bata hakuri sai dai mafi yawa sun girgiza da jin dalilin dukan da mahaifinta yai mata, domin Falmata yarinya ce mai natsuwa da kamun kai wacce ake ganin kamar wata yarinyar matashi irinta a unguwar, wasu cewa suke sai dai idan saurayin ne yake son lalata amman Falmata ba halinta ba ne, wasu kuma sun yarda wanda hakan bacin suna a gareta da kuma tarbiyarta, a yadda kowa yakr ganin Tumba tana rikon Falmata tana mata gatan da bata yi wa Naja ma da take yarta sai suka yarda da abunda ta fada a ganinsu ba zata mata sheri ba.

Har aka ci aka shude Falmata na kwance a gurin tana kuka, bata jin abunda mutanen suke fada har sai idan sun yi da karfi, fuskarta ya kumbura sosai kafarta sai ciwo yake kamar an cire mata shi, sai da dare ya raba sannan ta rarafa daker ta shige dakinsu bata ko karasa kan shimfidarta ba ta kwanta a gurin a kasa tana kuka a hankali, babu komai a ranta sai kewar mahaifiyar ta kalaman da tai mata na bankwana.

“Zan tafi na barki ciki taradadi Fulani, Allah ya zama gatanki, na san za ki sha wahala kuma za ki ga banbanci da kiyayya, amman ki rike Allah shi sai miki gata, kuma kar ki yi wasa da addu'a�

Mama..... Ta kiran sunan mahaifiyarta a hankali tana jin kamar ace tana kusa da ita, sai kuma ta fashe da matsanaicin kuka.

__________

Falmata baiwar Allah Iya ta ja miki wahala yau 😭
Nana yar...... 🤔
03/12/2021, 08:09 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄*

By Khadeeja Candy

*8*

Da wani irin zazzabi Falmata ta farka, fuskarta ta kumbura gaba daya jikinta sai ciwo yake idonta ma ya kumbura sosai sakamakon kukan da ta kwana tana yi.
Babu abunda ta fasa daga cikin aikin gidan da ta saba, ta sani sarai idan ta saka kuiya ko tace ba zata iya ba wani karin wahalar ne. Tana aikin tana kukan zuci har ta yi ta gama, ta dawo dakinsu ta zauna ta gefe daya dan bata iya zama daidai.

Tumba ce ta shigo dakin tana kare mata kallo.

“Ba za ki tashi ki je gurin aikin ba?�

Kallon Tumba tai kamar zata fasa kuka, bata jin abunda ta ce sai dai tana ganin bakinta na motsi.

“Ban ji komai ba Umma�

Ta fada muryarta na rawa kamar yadda jikinta ma yake rawa dan ganin take kamar dukanta Tumba za tai ko ta sake mata wani mugun sherin. Wani kallo Tumba tai mata.

“Ni za ki fara yi wani sabon siyasa?�

Ganin Tumba ta nuna kanta da yatsa yasa ta nemi duk inda wani kuzari yake ta tattaro shi ta saka a jikinta ta mike tsaye ta karasa kusa da Tumba dan jin abunda take fada.

“Wallahi ban ji me kika ce ba Umma bana ji sosai�

Ta fada kamar zata fasa kuka, Tumba ta san Falmata ba zata mata karya ba, ba zata mata haka da gangan ba, yanayinta kadai ya isa ya sanar da gaskiyarta.

Tumba ta dan tabe baki, sai a lokacin ne take girmama marin domin ba marin wasa Baba yai ma Falmata ta ba, gashi fuskarta har ya kumbura.

“Cewar nai ki tashi ki tafi aikin�

Tumba ta fada cikin daga murya ta maimaita mata ta yadda za ta ji. A take Falmata ta fara murza yatsun hannunta so take ta sake tuna mata cewar sun koreta amman sanin waye Tumba yasa dole tai shiru ta sauke kanta kasa.

“Ba za ki je, ki ba su hakuri ba?�

Wannan karon ta ji domin Tumba da karfi tai maganar.

“To�

Amsa tana motsa jikinta daker domin ba karamin tsami yai mata ba. Tumba ta juya ta fice daga dakin. Falmata ta nufi gurin da Hijabinta yake ta dauka ta saka ta fito. Da gangan Tumba ta kira ta karbi dumamenta ganin Baba na tsaye yana shirin tafiya.
Falmata ta nufi inda Tumba take da zimmar karba ba dan ta ji abunda tace ba sai dan ganin tana miko mata kwanonta. Ba dan tana jin yunwa ba domin komai ya fitar mata a rai, kan ta karasa Baba ya daka mata tsawa.

“Kar ki karbi abincin nan, ba za ki sake cin abincin gidana ba, tun da kika zabi iskanci....�

Cak Falmata ta tsaya ta kasa karasawa gurin da Tumba take zaune taka miko mata dumamen, ta ji abunda Baba yace saboda yanayin muryarsa irin mazajen nan da idan suna magana daga murya suke, balle kuma ita da baya iya yi mata magana a hankali.

“Haba Malam ba a horo da yunwa, na san Falmata ta yi laifi amman ka dubi girman Allah ka yi hakuri, ba a biye ta yaro�

“Ni dai na fada miki ban yafe a bata abincin gidana ba, ba zan ciyar da karuwa ba�

Ya fada kai tsaye sannan ya nufi kofar fita ko inda Falmata take be kalla ba. Baki sake Falmata ta bishi da kallo hawaye na sauko mata zuciyarta na mugun kuna, kamin ta kalli Tumba wacce ke kukan karya.

“Wallahi da na san haka abun zai zama da ban fada maka ba, wannan abu be min dadi ba ni Ramatu�

Bata iya ji yo komai amman tana gani ganin yadda bakinta ke motsi ta san da kuma kukan murnafurcin da take, ta san ta shirya komai ne. Daker Falmata ta hade abun da ya tsaya mata a wuya sannan ta nufi kofar fita tana jin kamar ta mutu a yau ta huta, taya zata rayu a idan ubanta kuma ace ba zata ci abincin gidan ba? Miyasa Tumba zata mata haka? Me tai mata? Saboda ta fadi gaskiya? Mi ya kaita fada mata gaskiyar? Miyasa ma yasa ta aikata tun farko? Tana tafiya tana tambayar kanta tambayar da bata da amsa hawaye sai aikinsu suke a fuskarta.
Gidansu kawarta Khadija ta nufa, sa same a tsakar gidan tana wanki kasancewar yau assabar babu school, Khadija na ganin Falmata hankalinta yai mugun tashin.

“Innalillahi ke lafiya me ya same ki?�

Bata ji abunda Khadija tace ba amman tabbas ta ga bakinta na motsi. Hakan yasa Falmata ta fashe da kuka, ta sani an nakasata kenan.

“Khadija Umma ta min shari ta ce Baba ta ga namiji yana taba ni, Baba ya min mari biyu kuma ya doke ni, ya ce kar a sake bani abincinsa, Khadija bana iya ji yanzu sai an yi magana da karfi na shiga uku�

Wani irin rirrike Khadijar take tana fadin kukan kan ya samu hanyarsa, a take Khadija ita ma ta fashe da kuka ita da kawarta aka rasa nai rarrashi wani. Mahaifiyar Khadija ta saki tsintsiyar hannunta tana hawaye.

“Wai me kika tarewa matar nan ne? Wani irin zallumci ne wannan?�

“Allah ya isar miki Falmata Allah ya saka miki�

Khadija ta fada cikin kuka, kamin ta kama kawar tata su nufi baranda su zauna. A gidan Falmata tai wuni Maman Khadija da Khadija suka kitsa mata idan ta koma ta ce wa Falmata taje gurin aikin ta ba su hakuri sun maida ta.

“Kullun idan ta tura ki aiki ki dawo nan ki zauna sai lokacin komawarki gida yayi sannan ki koma, abinci kuma ki zo nan ki rika ci kullum�

Maman Khadija ta fada mata a kunne cike da tausayawa, domin idan bata mata rada ba ba zata ji abunda tace ba. Falmata ta gyada kai.

“Na gode�

“Babu komai ai yiwa kaine, wannan rashin imani na Tumba yayi yawa, ko dan tana ganin bata haifa ba ne take haka? Wannan wace irin zuciyata ce?�

“Allah zai saka mata In-Sha-Allah�

Khadija ta fada tana sharewa Falmata hawayenta. Sai da Falmata ta auna lokacin komawarta sannan ta fita daga gidansu Khadija ta kama hanyar gida tana ta jin tsoro domin gani take kamar asirinta zai tonu Umma ta gano bata je aikin ba.

AA POV.

Tun shekaranjiya da yai hadari da Nana be sake fita aiki ba, ba dan kuma baya iya fitar ba, sai yai amfanin da accident din da yai yace musu ba shi da lafiya zai dauki sati yana jinya, tsoro ya cika masa ciki yana ganin kamar idan yaje zai iya haduwa da Nana ta kira wani tace gashi nan a kama shi wata kila ma Babanta Soja ne ko Alkali a masa daurin goro. Anti Rabi kam ba a magana domin ko kofar gidan aka taba sai ta ji kamar zuwa za ayi a tafi da ita da AA.

“Babu irin gargadin da ban maka ba, amman baka ji ba, gashi nan ka je ka kwaso mana abu kai baka cikin natsuwa ni bana ciki�

Kallon Anty Rabi yai yana murmushi, duk irin tsoro da fargabar da yake idan ya tuna Nana da yadda take wasu dabi'un sai ya samu kansa da annashuwa, ba laifi tana da wauta and he likes that ko dan kudin da take sake masa.

“Babu fa wani abu Anti, da za su kamamu ai da ba za su kai yanzu ba a nemo inda nake ba, ina tunanin bata fada ba ne saboda ita ma bata da gaskiya ai�

“Hmm ka sani ko ana can ana nemanka?�

“Idan nemana ake ai ta san gidan nan, kuma ta san inda na ke aiki�

Ya fada har lokacin murmushi yake.

“Maybe yar farin ce tana da wauta sosai�
Chapter 18 · 0% Book details