← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 172

Sashe 145

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta dade a bandakin tana tabe tabe sannan ta yi alwalar ta fito. Kalle kalle ta fara yi ko zata ga hijab da abun sallah, sai ta ji kamar an jefo dutse a window dakin, da farko dan tsoro ta ji sai dai ba sosai ba, kadan kadan ta taka ta isa gurin window ta daga lalulen ta leka bata ga komai ba. Sai manyan motoci da garden.

“Kai ashe gidan sama na da dadi hmm, sai ka hango komai a kasa�

Tana rufe bakin ana saka hannu a rufe mata bakin da karfi ta yadda ihunta ba zai fita ba, kamar wanda ya rufe mata bakin ya san za ta yi ihu sai ta fara kokuwar juyowa tana ihun da sautinsa ya ki fita, juyowa yai ya ita ta fuskance shi. Bude ido tai kamar za su fito wani irin farinciki ya lullubeta da kuma dan tsoro a lokaci daya, a hankali ya dauke hannunsa daga bakinta yana kallonta fuskarsa da murmushi idonsa kuma cike da kwalla.

“Ya akai ka zo nan? Waya fada maka ina nan? Yaushe ka shigo?�

Be ce mata komai ba ya kai hannunsa yana shafa fuskarta, sai ta lumshe ido ta saka hannunta biyu ta rike hannunsa, tana jin wani irin farinciki kamar ta rumgume shi.

_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Khadeeja Candy*

Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Ammy ta dawo gida cike da tunani kala kala, domin babu abun da Hajiya Babba bata labarta mata ba na abun da ta aika, a lokacin ne Ammy ta kara gasgata abun da Fadime ta fada, Shattima kadai ta labarwa abun da ya faru, sai Jekadiya ba ta sanarwa kowa ba saboda bata son ta sanarwa Baba Waziri a yanzu da yake cikin alhinin mutuwar yarsa. Sai dai ta kwana da tunanin abun a ranta tunanin sai ya zame mata kala biyu, ga na Iya ga na Hajiya Babba, sai ta ji tausayin Mai Martaba ya kara kamata da kuma yaranta da ake son ganin bayansu saboda abun duniya da za a mutu a bari. Haka ta kwana bangaren Mai Martaba da tunani kala kala a ranta,sai da ta gama azkar dinta sannan ta dawo bangarenta domin hada masa abun karyawa, ko da ta shigo sai ta samu Shattima zaune a dakinta yana latsa wayarsa, ganinta yasa ya dago yana mika mata gaisuwa. Sai ta amsa da murmushi tana kara jin son danta a ranta, lallai ta yarda idan ba kai cuta ba Allah ba zai bari a cutar da kai ba, idan an samu nasara to kadan ne wanda zata zo da jarabawa.

“Tun da sassafe haka ko nan ka kwana?�

“Aa yanzu na iso�

“Lafiya Kalau�

Ya amsa yana murmushi, sai ta zauna tana kallonsa.

“Shattima ka dage da addu'a, na san kana yi amman ka kara�

“Inshallah, mi ya faru?�

“Komai ai ya faru, lamarin na Iya kadai abun mamaki wanda na san ba dan addu'a ba da a yau ba mu kai haka ba, kuma bayan lamarin Hajiya Babba abun mamaki ne matuka�

“Me ya faru da ita?�

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta labarta masa abun da ya faru da kuma irin kalaman da Hajiya Babba take ta fada mata a lokacin da ta je ganinta.

“Hajiya Babba ba ta ba ni mamaki ba kamar Jurry, mahaifinta? Kuma ni ma dan'uwanta ne, wace irin zuciya ne wannan?�

Ta fada cikin tsananin mamaki marar misaltuwa. Ammy da idonta ya cika da kwalla ta ce.

“Shiyasa ake son addu'a kana rokon Allah ya baka zuri'a ta gari mai tausayinka da kaunarka kuma wanda zata amfani al'ummar musulmi kuma Annabi yai alfahari da ita�

“Allah sarki Mai Martaba bayan duk dawainiyar da yai da ita tana jin ta kai matsayin da take ganin ya kamata a kawar da shi? Ai ko ba amana bata kama su yanzu ba, ba za su taba samun salama a cikin rayuwarsu ba, ko da ko abun da suke da buri ya kasance�

Cewar Shattima yana jinjina lamarin da yake jinsa kamar ba gaske ba. At the same time ya ji wani irin kaunar Fadime ta kara shiga ransa, domin dukan abubuwan da ta fada sun tabba hakan na nufi ba karya tai ba, kuma ta taimaki rayuwarsu, a lokacin da yan'uwa na jini da kuma irin su Iya suke so ganin bayansu. Samun kansa yai da murmushi duk da irin hali yake ciki na mamaki da alajabin abun da Ammy ta fada masa.

“Smiling...?�

Ammy ta tambaya tana kallonsa da dan mamaki, sai yai sauri kallonta domin be san yana murmushin a fili a tunaninsa iya cikin zuciyarsa ne yake.

“Ah Amman Mai Martaba ya san da wannan magana?�

“Bana son tada masa da hankali, ya zai ji ace matarka da Yarka suna kokarin ganin bayanka? Ga kuma Iya a gefe?�

“Yeah amman dole ne zai sani, and the most important thing is komai ya bayyana a yanzu, and Inshallah zan sake sakawa a yi masa saukar kur'ane duk da an sha yi masa a baya, amman hakan ba zai haka mu kara ba, Ammy kuma ki kara tunatar da shi addu'a ya rike ta sosai�

“Shattima kenan, ni zan baka wannan shaidar da baya addu'a wata kila ta yanzu an manta da labarinsa, kuma duk da hakan zan saka a rubuta masa bismillah guda dubu ya sha, domin ita ma tsari ce sosai daga komai�

“Allah ya kara tsarewa, ni fa daman ina tunanin Sirleem ba son Nana yake ba kamar hadinta ne...�

Shattima na kai Aya Nana na turo kofar dakin ta shigo.

“Ammy ina kwana, Ya Shattima Good morning�

“Morning dear�

Shattima ya amsa mata Ammy kuma ta sakar mata murmushi.

“Ammy har yanzu shiru�

Nana ta fada tana zaunawa kusa da ita, sai Ammy ta kai hannu tana shafa kanta murmushi kwance a fuskarta ko bata fada ba ta san abun da take nufi.

“Already na yi magana da wanda zai masa komai, so idan ya gama zai neme ni ni kuma zan masa magana, ai ni na ce zan yi ko?�

“To maganar gidan fa?�

“Hankalinmu ne ba a kwance ba, kwana biyun nan kin sani, bana son na yi ma Mai Martaba magana shi kuma yai ma Waziri da maganar a yanzu, ki bari nan da sati daya idan komai ya daidaita sai mu ga abun da Allah zai yi�

“Okay Ammy wace makarantar kike ce a sama mishi?�

“Ban sani ba tukunan, ya fada min dai engineering yake son yi, kuma na fadawa Prof a sama masa makaranta mai kyau mai tsada�

Wata kalar dariyar jindadi Nana tai.

“Thank Youuu Ammy...�

“Ki karbi account dinsa a saka masa 1million ya siye tufafin tafiya�

Shattima ya fada, sai Nana ta ware ido da karfi ta dawo kusa da shi ta rumgume shi tana murna.

“Thank Youuu so much Yaya wow....�

Sai kuma ta dawo gurin Ammy.

“Ammy ara phone din pls�

Bata ko tsaya jiran umarni ba ta dauki wayar ta fice da sauri tana murna. Bayan fitar Ammy ma ta kintse ta nufi kicin domin ita da kanta take shiryawa Mai Martaba abun da zai ci. Kamar fitarta Shattima ke jira ya aikawa Ra'ees da kira. Sai da tai ringing tana daf da tsinkewa sannan yai picking da muryar da ke nuna yanzu ya tashi daga bachi.

“Ra'ees�

“Na'am barka da asuba�

“Gida na ke son a nemo min within Katsina and Kaita gida mai kyau�

“Kai zaka zauna?�

“No kyauta zan yi�

Raees yayi hamma sannan ya karasa tashi zaune.

“Okay amman wanda zaka bawa kyauta babba mutum ne ko karami�

Shattima ya san dalilin tambayarsa da yake saboda ya san irin gidan da zai samo masa ne.

“A samo mai kyau dai karka damu da ko nawa yake, ina sonsa cikin kwana biyun nan pls�

“Okay�

Ya amsa sannan ya kashe wayar, Shattima ya jingina da kujerar da yake zaune yana murmushi tunawa da lokacin da ya taba kade Fadime.
Chapter 145 · 0% Book details