← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 172

Sashe 155

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana cikin fadin haka wayar ta sake ringing, tashi tai da sauri tana kallo red da green din toch din dayan ansa saka received dayan kuma hang up sai ta taba green din tana kallon yadda call din ya fara tafiya sannan ta kai a kunnenta.

“Hello�

Inna ta kura mata ido tana ta kallonta cike da burgewa. Ita kuma ta nufi gurin da aka daure shannun tana ta hello hello ba a amsa mata ba, sai ta sauke wayar ta kalli kiran ta ga yana tafiya sai ta maida wayar a kunnenta.

“Hello Wasim....�

Ta fada tana fatar ta ji muryarsa ya amsa mata, sai ta ji muryar Shattima.

“Wasim ya ce zai kira ki ne?�

“Aa ni ban ma sake ganinsa ba, amman ai zai iya ganin an ba ni waya ya kirani tun da yana tsafi�

“Wato ba ki cire shi a ranki ba ko?�

Ta yi shiru idonta na cika da kwalla.

“Ina son Wasim, ba zan iya cire shi a raina ba, yana da kirki sosai�

Shattima ya katse kiran gaba daya yana jin kamar ta soma masa mashi a kirji, kiran da yai mata na albishir ne sai dai abun da ta fada masa yasa ya ji baya bukatar cigaba da waya da ita, tsaye tai da wayar a kunne hawaye na sauko mata.

“Hello.... Hello... Assalamu Alaikum....�

Tun tana hello har ta gaji ta fara sallama, jin shiru yasa ta sauke wayar tana kallon awarwaron da ya saka mata, sai kawai ta fashe da kuka.

ZAINAB POV.

Tsaye take gaban wani karamun zafi dake ta kwarar da ruwa, lokaci lokaci take kai hannu ta share hawayen da suke cika mata ido tana rumgume da hannayenta, sai kallon ruwa take. Duk abun da take Wasim na zaune saman wani dutse yana kallonta, tausayinta ya cika masa zuciya sosai, he know how hard it's ka bar komai na ka ka dawo rayuwa inda baka saba ba, kuma da mutanen da baka saba ba, cikin wani addini na dabam da al'adar da baka saba gani ba, saukowa yai ya ta ko zuwa inda take tsaye ya tsaya gefenta yana kallon ruwan da take kallo.

“Akwai ciwo ko? Kina jin wani yanayi na dabam, hmm haka na ke ji saboda rabuwa da Fatime, amman na fi jin tausayanki, saboda ke kin rasa komai ni kuwa wanda na ke kawai na rasa�

Ta kalleshi shi kuma yana ta kallon ruwa, ya cigaba ba tare da ya kalleta ba.

“Wani lokacin be kama mu dauki komai mu rike shi a rai ba, komai mai wucewa ne, ina jin yadda kike ji saboda ina jin kamar wani bangare na rayuwata, kuma ina jin kamar zan iya zama silar farincikin idan kin ba ni dama�

Ta sauke kai kasa a yayinda shi kuma yake kallon fuskarta.

“Za mu bar garin nan saboda ki samu farinciki kuma ki sake, ki cigaba da rayuwa kamar yadda kike saba�

Ta kalleshi tana murmushi idonta kuma na zub da hawaye.

“Har da kai?�

“Eh, to me zan yi idan na zauna a garin? A duk lokacin da na tuna abun da suka min akan Fatime zai na ji bana bukatar zama garin, kamar yadda ke ma na san garin ba dadi yake miki ba�

“Bana jindadi, amman ina kokarin kafa rayuwata a nan ne saboda mahaifiyata tana nan, babu inda ya fi min dangina�

“Ba tafiya zaki yi ki barsu har a bada ba, zaki rika zuwa kina dubasu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, ko ba komai za ki fi jindadin rayuwa a inda nutane masu irin addininki suke rayuwa sama da nan, maganar mahaifiyarta ki kuma ki barta�

“Saboda me?�

Shiru yai yana kallonta kamar mai fargabar abun da zai fada mata, sai ya mika mata hannunsa.

“Ina son ki yarda da ni Zainab, ina son ki aminta da ni, ki ba ni dama kuma ki sake jikinki da ni, ta yadda zan iya yakar kucin dake zuciyarki, ina son na shimfida miki wata sabuwar rayuwa wanda ni da ke zamu manta da komai mu yi farinciki kamar kowa...�

Hannunsa ta kalla sannan ta kalleshi gabanta na bugawa da mugun karfi da kuma sauri a lokaci daya.

“Me ya faru da Iya?�

Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya ce.

“Iya ta mutu tun a ranar da na rabo ta da ke, cikinta ya kumbura sosai muna isowa nan sai ya fashe saboda kankarun maitar dake ciki�

Baya baya tai wasu zafafan hawaye na sauko mata, saurin rikota yai ganin zata fada a cikin zafin ruwan, sai ta durkushe a masa jikinta na rawa ta rike warkin dake jikinsa da karfi kamar zata yagashi ta fashe da kuka mai karfi.

“Kenan na rasa kowa... Na rasa kowa.... Na rasa kowa...�

Ta maimaita har sau uku muryarta na rawa, hawaye na sauko mata kamar ba gobe, lokaci daya idon Wasim ya cika da hawaye.

“Ba ki rasa kowa ba Zainab ina tare da ke har abada�

Ya fada tare da dukawa ya rumgumeta sosai ta yadda zata yarda har a yanzu akwai wanda ya damu da ita kuma yake tare da ita.

_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Khadeeja Candy*

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

3 MONTHS LATER...

Fadime na tsaye bakin bukkarta dafe da waya a kunnenta sai faman dariya take. Yadda dariyar take isa a kunnen Shattima sai ta saukar masa da natsuwa har ya samu damar murmushi.

“To yanzu fada me nake yi?�

Yayi shiru yana kamar mai tunani.

“Kina tsaye bakin kofar bukkarku�

Ta wara ido tana dariya.

“Wallahi ka canka daidai, dan Allah waya koya maka?�

“Wasim�

Ta sake yin dariya.

“Wallahi Wasim be ko ya maka ba, ai baka san shi ba baka taba ganinsa ba�

“Na hadu da shi ban fada miki ba ne kawai, kuma yace kar na fadawa kowa wannan lakanin�

“Hahaha ban yarda ba, sai na ganka a gabana�

“Rufe idonki�

Ta rufe kamar yadda ya bukata, sai ya mike tsaye daga kan kujerar da yakr zaune ya dauki apple daya ya nufi windows din dake dakin.

“Ki fara siffanta ni da irin sifar da kike son ganina zan bayyana yanzu�

“Na san kai fari ne, ina son na ganka a cikin green din yadi, da bakar hula kana kamshin turarenka, kana murmushi kana kallona�

Murmushi yai.

“Gani nan zan taba ki...�

Saurin buden idon tai a zatonta da gaske ne, sai ta ga babu kowa a gurin.

“Ba ka iya ba, kawai kana canka ne�

Murmushi yai sauti.

“I can't wait to see you Fateema...�

Ta yi shiru tana murmushi.

“Idan na fada cewar kana kira wai ba a yarda da ni�

“Ba na ce ki daina fadawa kowa ba?�

“Kuri na ke yi ai�

“Kurin me?�

Ta yi dariya da yar siriyar muryarta, ba ta ce komai ba har na tsawon lokaci.

“Zan aje waya, amman kamin na aje fada min abun da kike so�

“Karatu dan Allah ranka ya dade, ina son karatu ka ga Bappa na yana jin maganar ka dan Allah ka masa magana ya bar ni na yi likita kamar kai�

“Hmmm miyasa sai likita? Why not lawyer ko wani dabam?�

“Aa irin na ka dai�

“To ai kin kusa zuwa nan sai a saka ki makaranta kawai�

“Waye zai kawo ni?�

Yayi shiru yana jin kamar yayi subul da baka.

“Yan'uwanki mana, very soon za a kawo ki�

“Tare da wa?�

“Yan'uwanki�

“Da gaske?�

“Na taba karya?�

Ta yi dariya har da kyalkyalawa ta rufe ido kamar yana gabanta. Shi ma murmushi yai he can't say bata son shi amman zai iya tabbatarwa duniya izuwa yanzu Fadimr bata da wanda yake saka ta nishadi da sauraren labaranta any how kamar shi, all her silly questions zai bata amsa be taba jin ya gundura ba duk da kasancewar ba mutum ne mai son yawan magana ko tambaya, but he can't tell why idan Fadime ce zai tsaya ya saurarenta kuma ya amsa mata, kuma be tana gajiya da kin kiran a waya ba, ita kuma da ta iya kullum za a jera masa filashin ya fi a kirga haka ma Bappanta da duk wanda take da number shi.
Bayan ya katse kiran ta koma cikin bukkatarta ta aje wayar da screen dinta ya gama cin ubansa a hannunta saboda faduwan da wayar take any how, fitowa tai ta nufo inda Inna take zaune tana gyaran shinkafa ta zauna kusa da ita.

“Inna wai zamu ta fi yola?�

Inna ta kalleta.

“In ji wa?�

“Ranka ya dade ya fada yace wai za mu tafi Yola�

“Eh�

“Gurin me?�

“Gurin Aurensa mana�

“Aurensa kuma?�

“Eh�

“Aure zai yi?�

“Eh ba kin ce ba ki son sa ba?�

Take idonta ya cika da kwalla gabanta yai mugun faduwa.

“Amman be fada min ba, Inna da gaske?�

“Eh mana ba kin ce baki son shi ba�

“Ni ban ce ban son shi ba, na dai ce ina son Wasim, kuma na ce garin ya min nisa, amman ai yana da kyau kuma yana da sarauta�

Inna ta kalleta da kyau.

“Ashe kina da hankali, har kin iya kwadayi Fulani?�
Chapter 155 · 0% Book details