← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 172

Sashe 113

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sau uku tana mika hannunta da zimmar kaiwa ta bude kofar dakinta sai ta saka saboda kukan da ya ci karfina. A bakin kofar dakinta a zauna tana wani irin kuka mai ban tausayi, da tasa irin abubuwan da Iya zata fada mata kenan da bata bukaci sanin komai ba. A yau sai ta ji ta raine kanta sai a yau ta gane ita din ba kowa bace, daukarar da take da ita ya yawan mabiya a instagram be haifar da mata da komai ba, a yau ta tabbatar da kaskantatun mutane da take rainawa wayo ma sun fita a yau, domin wasu da yawa ta hanyar sunna aka haife su, tsabanin ita da aka haifa ta hanyar zina zinar ma a tasha, sannan tai rashin dacen mahaifiya ta kwarai.
Daker ta yunkura ta tashi tsaye ta kai hannunta ta bude kofar dakin ta shiga ta bata da mu ta rufe ba ta taka har gaban gadonta ta zauna tana jin kanta na juyawa idonta na nauyi kamar zasu fito, zuciyarta na bugawa ta karfi.
A yanzu ta gane bata yi sa'ar rayuwa ba ta ko'ina, ta kwanta saman gadon tana jin tausayinta kanta, domin ta san wannan sirrin dole wata rana zai bayyana dole ne wata rana duniya zata sa wacece ita, wacece ita na asali ba na daukakar da aka riga aka santa da ita ba.

“Komai ba shi da amfani a gurina asali mai kyau shine komai�

Ta furta wasu hawayen masu zafi na sauko mata.

“Na rasa komai�

Ta sake fada tana jin wani irin tausayin kanta marar misaltuwa. A cikin kowa ce rayuwa akwai faduwa da tashi akwai samu da rashi, kuma akwai jarrabawa a yanzu kam ta yarda wannan ita ce jarrabarwata kuma jarrabarwa da tafi ko wace muni. Ta kwanta ba dan bachi ba domin har dare ya raba bachi be kusanci idonta ba, babu komai a kwakwalwarta sai tunani kala kala a cikin har na zalincin da Iya tai ma Ammy. Domin a iya ganinta be su cancanci a masu masauki a fadar ba amman aka ba su har aka jasu a jiki amaimakon ta kyautata sai ta cutar da Ammy har take bibiyar yayanta. A yanzu ta kara jin tausayin Shattima a ranta sanin gaskiyar abunda  yake faruwa, a yanzu ta gane dalilin da yasa Iya take cilasta mata son Shattima, a yanzu ne ta gane dalilin da ya saka Iya bata taba mata fada akan yin ibada ba, bata taba ganin ta yi wata shiga ta kusheta ba ko kuma ta nuna mata kar tai, Ammy ce ko Shattima wani lokacin suke mata fada kan yanayin shigarta, sai a yanzu ta gane dalilin da ya saka Ammy tace kar a sake bari su shigar mata falo saboda Iya ta nemi a hada Shattima da ita, Ammy ta yi gaskiya da ta fada ma Iya cewar kalar zaren ba kalar yadin ba ne. Da tunani kala kala ta washe safiya tana yin sallah asuba ta fito harabar gidan ta zauna sai ta rasa abun da ke mata dadi, ita dai ba tace bata da lafiya ba, ba ta ce lafiyarta kalau ba, haka ba zata iya bayyan yadda take ji a zuciyarta ba for now.
Tana zaune a gurim har rana ta fito tana sanye da kayan bachi tana zaune a gurin sai kallon harabar take, a zuwa yanzu bata san abunda ya kamata tai ba kuka ko dariya? Ko murna? Ko bakinciki ko kishiyarsa? Tama kasa yarda cewar wai ita ce Zainab aka samu ta wannan hanyar, duk irin jin da kanta da take sai ta ji kamar ta fi kowa kaskanci tsakanin jiya da yau.

“Kenan Iya ita ta cinye Auwal?�

Ta fadawa kanta tana jin wani sabin hawaye yana cika mata ido, rabon da hawaye ya kusanci idonta tun jiya da abun ya faru domin ta tabbatar wani abun yafi gaban kuka, a tsakar dare neman kuka tai ta rasa. Ta lumshe idonta kana ta saka hannunta ta dafe zuciyarta tana sauke numfashi a hankali.

“Komai zai wuce zai zama tahiri Zainab, zaki samu farinciki wata rana zaki tuna wannan ki ji ba komai ba, ba ki da laifi ba ki ce a same ki ta wannan hanyar ba, ba ki ce a haife ki a haka ba, ba ke kika saka mahaifiyarki ta zama haka ba...�

Ta fadawa kanta a kokarinta na kwantarwa da kanta hankali. Bata taba sanin hawaye na da zafi ba sai a yau, domin hawaye masu dumi ne suke sauko mata, a take ta ji wani zafi ta taso mata ya baibaye jikinta har saman kanta.

“Zainab har zuwa yaushe za ki daina wannan kukan?�

Iya dake tsaye bakin kofar falon ta tambaya, ganinta a gurin zaune bayan ta duba dakinta bata ciki.

“Har zuwa lokacin da zan mutu...�

Ta amsa mata ba tare da ta bude idonta ba.

“Na san zaki samu kanki a damuwa shiyasa ban taba labarta miki wannan ba, shiyasa na boye miki kuma na shimfida miki wata karyar wanda zaki rayu akanta kuma jiki dadin rayuwa�

“Ko ba ki fada min a yanzu ba, wata rana gaskiya zata bayyana kanta, dole ne za a binciko wannan abun, dole ne za a bukaci sanin asalina, domin shi n martaba ya mace�

Iya ta sauke ajiyar tana jin damuwar da yarta take ciki, ba damuwar abun da ta aikata ba.

“Na sani, amman dai yanzu ki manta da komai ki kwantar da hankalinki, bana son damuwarki....�

Zainab ta mike tsaye sannan ta juyo ta kalli Iya hawaye na bin fuskarta.

“Ba ki son damuwata? Amman kina son damuwar wasu? Me Ammy tai miki kike cutar da ita? Ba mu cancanci mu taka bakin kofar falonta ba, amman ta bar mu mun rabi jikinta, sanadim mijinta da yayanta ake min kallo mace mai kima bayan ni ba kowa ba ce, ba ki auna yadda wata uwar zata ji ba idan ta rasa nata yaya? Baki ayyana yadda Ammy take ji saboda halin da Shattima yake ciki? No Iya fada min akwai hannunki a jikin Mai Martaba ko?�

Iya ta daga mai kai, kai tsaye tana kallonta da idanuwanta na maita. Zainab ta yi kasa da kai tana murmushin da ya fi kuka ciwo, can kuma ta dago ta kalleta.

“Ke kika kashe Auwal?�

Nan kam ta daga mata.

“Ina yin komai ne saboda ni da ke...�

Zainab ta girgiza kai tare da kada mata tsawa.

“Ba saboda ni da ke kike ba, saboda son zuciyarki kike, wace irin macece ke? Wace irin zuciya ce a kirjinki? Baki da tausayi Iya? Baki jin be kamata ki yi wani abun ba? Miyasa zaki cutar da bayin Allah? Me suka miki? Why? Why?�

Ta tambaya tana dukewa a kasa ta fashe da kuka.

“Na yi nadamar haihuwata da kika yi a yau, ina ma na zo a mace, ina ma na mutu tun kamin wannna burin ya shiga rayuwarki? Kin cutar da mutane da dama, kin cutar da ni ta hanyar haihuwata ba ta hanyar sunna ba, kin cutar da Ammy da iyalan gidanta bayan ba su miki komai ba sai kyautata, har Auwal da be miki komai ba kim cutar da shi, kin maida yayansa marayu kin maida matarsa bazawara...�

Iya bata ce komai ba ta juya ta koma ciki, ko kadan bata taba jin nadamar abubuwan da tai ba, bata taba jin tausayin kashe rai ba, bata taba jin tausayin cutar da kowa ba, saboda babu tausayi babu imani a zuciyar maye, shiyasa ake cewa su bada wani shakiki na su, kamar uwa ko uba ko da ko wani dan'uwa ta yadda ba za su taba jin tausayi ko fashin cin kurwar wani ba, babu komai a cikin zuciyar mayu sai keta da hassada ga rashin tausayi da rashin imani, domin sai mutum ya siyar da imaninsa sannan yake iya yin maita.

SARDAUNA POV.

Farin bokitin wanki ne a gabansa ya maida hankali sai wanke kayansa yake, yana amsawa Anti Rabi firar da su ke sama ma, da fira tai dadi ne take dauko masa zancen mutuwar da akai a gidan Sarki.

“Ni ma na aji, indai ta bangaren Ammy ne gaskiya ba zan ji mata dadi ba, amman idan bangaren Hajiya Babba ne Allah ya jikan musulmi, ta fi kowa a duniyar nan bakar cuta da zalinci�

Ya fada yan murza wandon dake hannunsa da dukan karfinsa, Anti Rabi ta yi dariya tana saka kananan itace a wuta.

“Kai ba baka a taba ka baka iya yafiya ba�

“Wallahi na zance yafiya tsakanin da baiwar Allah nan, ta cutar da ni ina maraya na ta cutar da ni, bayan Annabi yace wanda ya taimaki maray kafada da kafada za su shiga aljanna tare da shi, amman ita neman cutar da ni take, hakam ya nuna ba karamin cutar mutanen gidan nan take ba�

“Ai kai yanzu ka wuce maraya, ka girma ka isa tallafawa kanka fa�

“Aa ni ban tashi a maraya ba, sai ranar da na gina kai, irin ginuwar da zan iya taimakon wasu�

“Ni na tsorata sosai a lokacin nan, Allah ne dai ya saka abun ya zo da sauki�

“Ni Wallahi na dauka ko akashe ni za su yi, babu imani a fuskar police din nan, dukana suke kamar sun samu kayan wanki a take suka sauya min fuska, ina da dan haskena yanzu na zama baki, jikina be gama dawowa ba�

Anti ta girgiza kai tana murmushi, ashe sara sukai akan gaba, suna tsaka da zancen wani katon bafade ya sallamo musu kofar gidan. Tun daga yanayin sallamar da tsayarwar mota ya isa ya sanar musu masu sallamar na musamman ne. Sardauna ne ya sama sannan ya wanke hannayensa ya nufi kofar gidan, yana ganin mutane dake sanye da jajayen kaya ya ji gabansa ya fadi domin ya san daga fada suke, tsoronsa daya kar ace wani laifi ya sake aikatawa, dan baya tunanin Nana zata aiko masa wannan tawagar.

“Lafiya dai?�

“Lafiya kalau dan talakawa? Kai ne Sardauna?�

“Aa yayana ne, me ya faru?�

Ya amsa da sauri numfashinsa har gargada yake tsabar tsoro.

“Daga masarauta ake nemansa, ka kira shi a duk inda yake yanzu nan�

“A gaskiya baya garin nan, ya tafi nijar gurin nema�

“Babu ta inda za a iya samunsa?�
Chapter 113 · 0% Book details