← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 172

Sashe 47

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ance ki aje yaran ki fita waje ki karya�

Falmata ta sauke Luma dake bayanta ta mikawa matar sannan ta duka ta dauki tray ta fita waje, kamin ta isa har wani hadiyar yawu take, biredi ne yaka biyar sai kwai ga dankali da plantain da tea mai kauri ga kuma ferfesun kayan ciki a gefe har wani tiriri suke, Falmata fitowa tai daga bangaren gaba daya dan kar ma ta zauna a inda za a ga lomarta ta zagoyo ta gaban ita cen lemu dake kusa da babban garden ta zauna, kayan cikin ta fara kaiwa aiki tana yi tana ashe hannu kamar sabuwar mayya.

AA POV.

Daga bakin kofar dakinsa Anti Rabi ta aje masa dumamem tuwon shimkafa da miyar taushe da tai jiya, sai ya wani yatsine fuska.

“Kai ni ba zan ci dumame ba daga yanzu na daina cin dumamae�

Anti Rabi ta kalleshi da mamaki.

“To yau kuma?�

“Eh daga yau gurin aiki zan rika karyawa, na san abincin kala kala zaka yi asuwaki kaji ka kuskure baki da lemu, Malam harka irin da mutunci�

“Eh nan kuma ta rashin mutuncin ce ba, ka ma samu sa'a mun tashi da dumemen da koko zaka gani, gurin aikin da basa iya baka komai sai ka siye�

Anti Rabi ta fada tana harar shi.

“Amman dai tsakani da Allah kina ganin zubina kin san ni ba jini talaka ba ne, kawao dai Allah ya kawo ni cikinku ne, ni yanzu na fara jin kamshi arziki kusa kusa, kin san ance arziki kashi ko? To na fara takawa�

“Wato dai baka rabo da yarinyar nan ba AA? Sai ka jawa kanka wata matsalar?�

“Aa fa ni ko sunanta ma na manta, ina nan dai ina addu'a kin san mai neman a gurin Allah baya fidda rai�

“Allah dai ya kyauta kuma tsare dan ni wannan neman kudi naka har tsoro yake ba ni�

Yar dariya yai ya shafa kansa.

“Wato ba zaki gane ba ne Anti saboda kina cikin geto area, da ace kina zaune a birni ko? Ga babbar mota ga kato gida ba irin wannan ba, ga kajin safe sa da rana namam rago da dare soyayyar hanta, Wallahi wannan baki baki nan jikinki ma duk bacewa zai yi, ai kudi sun yi a rayuwa, Ni wallahi har jin nake kamar masu kudin garin nan duk yan'uwana ne yanzu�

Ganin yadda take kallonsa da kamar tsoro da kamar mamaki yasa shi daukar talkaminsa yasa yana fadin.

“To wai waye baya son kudin nan ne dan Allah? Kudi fa Anti bama neman haram amman halal kam sai inda karfi ya kare�

Ya nufi kofa yana laleben aljihunsa dan tabbatarwa idan makullin motar da aka bashi yana nan ciki.

“Na tafi ni�

Sai ya waigo ya kalleta jin bata masa addu'a sai yai ma kansa.

“Allah ya tsare ya kai ni lafiya ya dawo da ni lafiya, Anti ayi ta addu'a kudi fa suna tafe mun fara taka matakin nasara�

Ita dai bata ce komai ba har ya fice, tsoro take kar ya saka kansa a wata mummunar hanyar, wannan son kudin nasa yayi yawa. Mai achaba ya tara ya hau ya fada masa inda zai kai shi, kamin su isa gidan ya sauka ya biyashi sannan ya doshi gurin masu gadin gate din ya gaisa da su, tana kallon cctv camera dake leke a gurin, a nan ma sai da suka tare shi suna tambayar inda zai je.

“Ni ne sabon direban Hajiya Nana kun gane ko?�

Ya fada yana jin wata isa sai kace wani sarki ko wani mai babban mukami. Ba su yarda ba har sai da aka ce ya kirata yai magana da ita, sai ya kira number Hajiya bata dade tana ringing ba aka daga.

“Hello Hajiya Nana�

“Wake magana?�

Jin babbar murya yasa shi duba wayar ya gani idan number ce ya kira, sai ya sake maida wayar a kunne sa.

“AA ne sabon direban Nana, da wannan wayar muke magana da ita shiyasa na kira na fada mata gani na zo zan kaita makaranta masu gadin sun tare ni sun hanani shiga�

“Ba su wayar�

Hajiya ta fada daga dayan bangaren, sai AA ya mika musu suka karba su kai magana da ita sannan suka bar shi ya wuce, kai tsaye ya nufi gurin da motar take, tun kan ya karasa ya matsa key din, sannan ya bude ya shiga yai warming dinta yai reverse ya fito daga daga parking space din ya zo bakin kofar fadar Ammy ya faka. A iya tunaninsa kamin Nana ta fito za a fara bashi abun karyawa ne, hakan yasa ya fito ya tare wani bawa dake aikin mopping din gurin yace.

“Dan Allah Malam dan shiga ka ce musu sabon direban Hajiya Nana ya iso yana waje�

“Ba ni da hurumin shiga ciki Malam, sai dai kai ma wadancan hadiman magana�

Kai tsaye AA ya nufi matan ya fadawa daya ya dawo cikin motar ya zauna. Ba a dade ba sai ga ya hango Nana ta fito sanye da uniform yai saurin fitowa daga motar ya bude mata kofar, ita kuma sai kallonsa take tana murmushi wani irin dadi take ji zai fara tukata, sai da ta shiga ya maida motar ya rufe, ya shiga mazaunin direba ya ja motar suka fita.

“Hajiya ina zamu je?�

“Wani guri mu huta sai lokacin dawowa daga makarantar yayi sannan mu dawo�

Kallonta yai ta madubin gaba sai ya ga ta kara kyau kamar ba ita ba.

“Ina kenan? Hajiya�

Ta kara kwantawa tana kallon titi.

“Wani guri dai�

“To amman biya zaki yi ko?�

Ta kalli madubin ta watsa masa harara.

“Eh lallai mai wannan yaron, ban ce na saka an dauke ka aikin�

“Aikin da aka daukani daban, kin kaiki makaranta daban, har inda zan boye ki sai kin biya shine deal din�

“Aiko zaka ja na koreka daga aiki�

“Ai ba kika dauke ni ba, ita wannan Hajiyar ai ta sani shiyasa ta amince ni ina jin ma kamar yar'uwarmu ce, kuma duk kika fada sai na fadi cewar ba ki zuwa makaranta guduwa kike�

“Ni kuma na ce ke kai kake kai ni wani guri ka boye, shiyasa ka ce na dauke ka aiki�

“Na ce karya kike�

“Ai ba a karyata dan Sarauta kana cewa karya nake za a maka bulala ko a saka ka aikin wahala ko a rufe a gidan yari�

Ya dan yi shiru yana tunani sai kuma ya marairaice murya

“Nana yanzu haka zamu yi dake, ni da na dauke ki kamar Mamana ina tunanin komai ke zaki min ko tufafi zaki iya siyamin amman sai fara saka min da wannan, yanzu fa ma yunwa nake ji�

“Karka sake ce min Nana Hajiya�

“Indai kina son na rika ce miki Hajiya sai dai ki biya�

Da sauri Nana ta kalleshi ta cikin madubi.

“Eh lallai kai baka ma da wayo, ai wanda ya dauke ka aiki ka zama yaronsa�

“Eh amman ai idan mutum yana aiki a gidan masu kudi gata ake masa, balle ke Nana da kike yar gata ina jin kamar ke dai aka haifa ko?�

“Ban sani ba, kai ka cika gulma da tambaya�

Murmushi yai be sake ce mata komai ba.

“Ni bani da kudi yanzu kuma karka kai ni school ma fada maka�

Ta fada ganin ya dauki hanyar makaranta har suna kusan isa.

“Miyasa baki son makaranta Hajiyata?�

“Haka nan dai bana so?�

“Wani abu ake miki a makarantar ne?�

“Ba abunda ake min bana son zuwa dai sai na rika jin kamar zan yi kuka bana son school ni�

Juyowa yai ya kalleta ta wani hade rai ta turo baki kamar zatai kuka.

FADIME POV

Tun cikin dare ta labartawa Inna wanda ya zo yai mata juyen gida.

“Inna na fara farinjini ko?�

Inna dai bata ce mata komai ba sai kallonta take da fitilar kwan dake haskata.

“Kina jin wani ciwo?�

“Aa�

“To ki yi addu'a kije ki kwanta�

“To Inna ki min addu'a ni wuya take bani har na manta da wasu addu'oin ma�

“To yayi kyau�

Ta mike tsaye ta dauki kyandir daya ta kunna ta nufi bukkarsu, tana shiga ta dauko littafinta ta fara rubuta abubuwan da suka faru sannan ta aje ta kwanta ba tare da tayi addu'ar ba. Can cikin dare ta fara jin ana wasa da bukkar ta fara ihunta kamar yadda ta saba tana kiran Bapppa sai da ya taso ya shigar da ita bukkarsu sannan aka samu zaman lafiya.
Washe gari sai ta farka cikin jindadi abubuwa biyu, Amo zata je da ita birni a yau kuma jiya an mata juye ta fara farin jini kenan, ko karyawa ba tai ba taje gidansu kawarta Ma'u ta labarta mata abunda ya faru jiya da dare sai wani shauki take yana jindadi. Sai da hantsi ya fito sosai ta dawo gida ta sha kokon da Inna da dama, ta dauki tulu zata je deban ruwa.

“Fulani ki kula kin san kullum kika je sai wani abu ya faru ko?�

“Aa zan yi addu'a babu abun da zai faru�

“To Allah ya tsare�

“Amin�

Ta kallame tulun ta bi hanyar, kana ganinta kasan tana cikin nishadi domin farincikinta ya kasa boyuwa sai far'a take. A maimakon ta isa gurin ruwa kai tsaye inda wasu yan mata biyu suke deba sai ta nufi gurin duwatsun kamar ta san Wasim na tsaye a gurin yana jiranta, tana hangoshi ta karaso kusa da shi da sauri tana murmushi.

“Kai dai jiya... An tashi lafiya dai�

Har ta fara bashi labari sai kuma ta tuna cewar bata gaisheshi ba, wani zancen bata kaunarsa na abun da yai mata duk ya kau saboda farincikin an mata juye.

“Lafiya kalau�

Ya amsa yana kallon cikin idonta kamar zai cinyeta.

“Jiya wani yai min juye�

Yayi murmushi har lokacin kallonta yake wani irin mayen kallo da yake saka shi nishadi da annashuwa, tana matukar burgeshi gashi yadda take abubuwanta tana saka shi nishadi.

“Kin jindadi?�

“Eh sosai mana, sosai ma ai na fara farin jini a haka kenan ko?�

Ya gyada mata kai yana murmushi.

“Kila son ki yake�

Ta yi dariya.

“Amman ai ina da miji dan birni�

“Idan shi ma dan birni ne fa�

“Aa dan kauye ne�
Chapter 47 · 0% Book details