Sashe 10
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ciki suke Allah ya baki yawan rai, tuba nake�
Cewar Kulu tana kara noce kai kasa.
“Kina da matsala Kulu, duk abunda ya kamata ki saka ido akai ba kya yi�
“Zan bincika ko waye shi Allah ya huci zuciyar ki ya kara miki lafiya�
“Kira min Jarma�
“An gama ranki ya dade�
Kulu ta mike da sauri ta fice daga dakin ganin yadda Hajiya ta hade rai kamar bata taba dariya ba. Ba a dauki dogon lokaci ba Jarma ya shigo dakin yana sanye da babban riga ga wani uban rawani a kansa, inda Kulu ta zauna ya zauna tana kallonta hankalinsa kwance sai dai har ya zauna ta kira shi ya amsa ta kora masa bayani bata kalleshi ba.
“Jarma�
“Hajiya�
“Akwai wanda ke son shiga tsakanin Sirleem da Nana�
“A cikin masarautar nan yake?�
Jarma ya tambaya cike da mamaki, sai a lokacin ta kalleshi.
“Bare ne, yaron da yake zuwa duba yaran Shattima�
Jarma yayi murmushi.
“Doc Deen? Kar hakan ya damu Salim, wayayyace kawai irin ta yan zamani ke kinsan ai ba zan bari wani ya dauki hankalin Nana ba�
“Idan ma ka ga zai kawo mana matsala ko wasa, aka yi masa sanadi da gidan nan�
“Baki da matsala da wannan Hajiya Salim ya cigaba da neman yarinya babu abunda za a fasa�
Ta dan yi murmushi tana kallon wata doguwar Fulawa dake gabanta.
UNCLE A A POV.
Ya yamutsa shinkafa da waken dake gabansa a kwano yana bata fuska.
“Anti Rabi sai ayi ta mana wake da shimkafa ba wani canji�
Anti Rabi dake aikin damawa dabbobinta kasari ta yi dariya.
“Hmm Unclen dinsu wani lokacin iskancin ka yawa yake, wani na can be samu kamar wannan ba amman kai ka raina, da alama dai kana da kudin cin wani abinci shiyasa�
Ya shafa kansa yana yar dariya.
“Wallahi kuwa wata yar marasa sanin darajar naira na samu nai mata na yan talakawa na ci kudinta�
“Ban gane yar marasa sanin darajar naira ba�
Yayi dariya a karo na biyu sannan ya labartawa Antinsa yadda ya yaudareta.
“Amman dai Uncle din yara baka da tausayi�
“Wane irin tausayi kina ganin yarinyar nan kin san yar masu abunce ce karamar yarinyar yar secondary school ta ciro kudi sun kusan 50k ta bani 5k ya maida saura, uwayensu ne barayin Jihar mu ai�
Ya mike tsaye yana ciro kudi, 2k ya cire a ciki ya mikawa Yayar tasa sannan ya maida sauran aljihu.
“Ni bari naje waje na ci abu mai kyau�
“Ni wannan aikin na ku yana bani mamaki kuma aiki a restaurant amman ba zaku iya cin abinci a ciki ba?�
“Ai wannan mutumen be da kirki ko ruwansa ka sha sai ka biya shi, zaka ci idan kana so amman zai cire a cikin albashinka�
“Allah dai kyauta ni kam ban taba gani ba�
“Ai ina samun wani aikin zan bar na shi Wallahi�
“Allah dai ya kawo rabo mai amfani�
Da amin ya amsa sannan ya fice daga gidan. Abun ka da unguwar mai mutane yana fita abokasa suka fara dago masa hannu.
“Sai Sardaunan samarin Yola�
Ya nufe su yana dariya.
“Amman na talakawa�
Ya karasa ya basu hannu suka gaisa sannan ya kara gaba ya siye alalen gwangwani gurin wata ya cika cikinsa a titi.
Washe gari ma fa yaje restaurant din sai da ya sake tararda Nana a inda ta saba zama, wannan karon ba bachi take ba idonta biyu suna hada ido ta watsa masa harara ta kawardar da kai, a iya ganinta da yake yi a yanzu kam ya tabbatar karya take da tace yayanta ne yake cewa ta jira a nan, ya lura idan ta ga mutane sai ta boye fuskarta kar a ganta haka yai ta aikin raba ma jama'ar da suke shigowa abinci yana kallonta zuciyarsa na karantarta tana tsara masa yadda zai sake samun wasu kudin a gurinta.
 Sai da ya koma gurin zamansa ya zauna sannan ya dauki biro da takaradar yai rubutu a kai ya dauki bottle water ya nufi inda take ya aje mata takardar a saman tebur din tare da ruwan ya koma ya zauna yana kallonta.
Tun da ya nufota take turo baki tana harararsa har ya karaso ya aje mata ruwan da takardar ya koma, a zatonta zai ce yau ma sai ta biya kudin zaman dana bachi amman bata ji yace mata komai ba, sai dai ta lura duk abunda yake idonsa na kanta.
“Ni nace ka kawo min ruwa ne�
Ya fada tana turo baki cikin sautin da ita kadai zata iya jin kanta, na kusa da ita ko kuma mai kallonta sai dai yaga bakinta na motsi sai hararar da take watsa masa ta isa ta sanar masa cewar da shi take. Hannu ta kai ta dauki takardar ta jefar a kasa tana cigaba da turo baki ita ala dole ga shagwa6a66iya.
“Ba za a karanta ba�
Daga can inda yake zaune ya gwalo mata ido ya hade rai yana mata alamu da ta dauki takardar ta karanta ko ya daketa, sai ta make masa kafada tana murguda masa baki, sai da ya unkura kamar zai taso ta karaso inda take sannan tai saurin kai hannu ta dauki takardar ta bude.
“Idan kina so zan iya kai ki wani guri inda zaki rika boyewa ba tare da kowa ya sani ba, amman nan ai public place ne kowa zai iya ganinki, idan kin aminta fita waje mu yi magana�
Da sauri ta dago ta kalleshi tana gyada masa kai alamar eh ta amince din, da ido yai mata alama da waje sai ta dauki school bag dinta ta nufi hanyar fita tana waigensa. Sai da tai kusan minti biyar da ita sannan Sardauna ya fakaici idon mutane ya tashi ya fita. Can gefe ya hangota ta juya baya dan kar a ganta sai boye boyen fuska take.
“Ke�
“Ni ba ke ba ni Nana Aisha�
“To ina ruwana da wani sunanki�
“To nima ina ruwana da kai�
Ita ta amsa masa ta shigar da yai mata maganar wato da fada fada, sai yai kwafa ya juya alamar zai tafi ya barta, da sauri ta riko hannun rigarsa.
“To akwai ruwana�
Ya sake yin kwafa sannan ya kalli security camera dake gurin ya kalleta.
“Idan kina so zan iya kai ki gidan ku sai ki boya a can idan lokacin da direban ki zai dauke ki yayi sai na dawo da ke�
“Ina zuwa�
Ta fada kai tsaye cike da jindadi, kallonta ya tsaya yi a ransa yana ayyana cewar idan shi barawo ne sai ya sace ta salon alon.
“To ai zamu aro babur da zamu je can unguwar�
“To aro�
“Zaki hau?�
Ya tambaya da mamaki dan be dauka zata yarda ba.
“Eh�
“To ai kudi ake biya kamin a bamu aron babur din�
“Nawa?�
Tunani ya tsaya yi kamin ya ce.
�2k kuma a can gidan da zaki zauna sai kin biya kudin zama�
Ta dan bata fuska.
“Nawa?�
�3k�
“Toh, ai dai ba zaka sace ni ba ko?�
“Eh shekararki nawa?�
�16�
“Amman dai ke wawuya ce�
Ya fada yana dariya a ransa sannan ya juya ta nufi cikin restaurant din, abokinsa Mu'az yai ma magana ya karbi makulin mashin dinsa sannan ya fito ya same ta a inda ya barta.
“Ki fita can titi sai na zo na dauke ki�
Ba musu ta kama hanya a ranta tana jin zafin wawuyar daya kira ta dazun, karasa yai gurin da suke aje abun hawan a gurin ya bude mashin din sannan yasa masa key yai tashi mashin din sannan ya fara tukawa ya fito da shi bakin titi can ya hangota ta boya a kusa da wani shago, karasa yai gurim ya faka mata ta hau yana fara tafiya ta rirrike shi gam ta boye fuskarta a bayansa, kusan sai ta rantse a rayuwarta bata taba hawan achaba ba, iyakarta keke shi ma tana yin wayo Ammy ta hana ta hawa saboda tana mace.
“Ke dallah sake ni kin wani rike ni kamar yar iska haka zan shiga da ke a unguwar mu kina tabani, ni ba dan iska ba ne ba a saba ganina da mace ba balle kuma ta rike ni�
“To ni ba tsoro nake ji ba ko kuma ni aka ce masa yar iska ce, ni yar iska ce kai ne dai dan iska mai sato yarinyar mutane kaje ka kaita wani guri ta boya�
Ta fada tana turo baki har lokacin bata yarda ta dago kanta ba. Tafiyar ba tai nisa ba ya faka mashin din gefen titi ya sauko ya fuskance.
“Ni ne ma dan iska mai sace yaran mutane? Ai ke ce stupid girl mai guduwa daga makaranta kina boya a wani guri, kuma ba zan kai ki din ba na fasa�
Ya karasa yana dangwararta da yatsansa.
“Ai Wallahi ba zan sauka ba, zan maka ihun ka yi satar mace�
Yadda ta daddage kan mashin din kamar na gidansu tana watsa masa wani kallo ya sani sarai zata iya iya masa ihun abunda ba halinsa ba, kwadayi yaja masa bala'i, ya san ma it's risk tsayinsu a gefen hanyar dan wani wanda ya santa zai iya ganinta da shi, ba shi da wani option da ya wuce kaita gidansu din ko kuma maidata inda ya daukota. Da farko yayi kudirin maidata inda ya daukota sai dai zuciyarsa na son kudin nata da yake gani kamar na banza a dole ya daure ya cije ya cigaba da tafiyar idan ta riko shi ya buge hannunta har suka kusa isa unguwar sannan yai mata dabara da ta rike karfen mashin din ta sake shi.
Bata yarda ta dago fuskarta ba sai da ya faka mashin din kofar gidansu ya sauka sannan ita ma ta sauka tana wani kyankyamin unguwar balle kuma da aka shiga cikin gida har wani dage kafa take sama sama kar ta taka kasa.
Shi yai sallama Anti Rabi dake aikin hada kwado ta amsa masa, ita kam banda aikin bata fuska da karema gidan kallo babu abunda take. Anti Rabi ta bishi da kallo har ya shiga dakinsa Nana na biye da shi ya dauko tabarma ya shimfida mata bakin kofar Anti Rabi.
“Zauna a nan�