← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 172

Sashe 67

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Haka ne, haka mijina yake fada shi ma be cire rai da cewar zan haihu ba, ni ma ban cire rai ba ko dan rikon da nake ma Ameer ina fatar Allah ya dube ni ya ba ni haihuwa�

Ta karasa idonta na cika da hawaye. Sannan ta dauko takarda ta rike biro tana tambayar yadda Falmata take ji da kuma lokacin da abun ya fara, after ta yi nata bincike ta kira likitan kunne ya dubata ya rubuta mata magani, da kanta ta karbi takarda maganin taje ta siyo mata a pharmacy dake asibitin sannan ta dawo office din waya a kunnenta.

“To ka biyo ka sauke min bakuwa a Masarautar su Sirleem�

Tana fadar hakan ta sauke wayar ta mikawa Falmata maganin, kamin ta shiga mata bayanin yadda za ta yi amfani da shi. After like thirty minutes Ameer ya shigo Office din, hannunsa rike da makullin mota.

“Tashi kuje shi zai sauke ki gida�

“Tau na gode Allah ya saka da alheri�

“Ameen, drive carefully�

“Okay Mom�

Ya amsata sannan ya juya suka fita tare da Falmata, a tare suka jera har gurin da ya aje motarsa, sai ya shiga sannan yai unlock din motar ta bude ta shiga.

“Ina wuni�

Ta gaishe shi ba dan ta san zai amsa mata yadda zata ji, bata a damu da sai ya amsa mata din ba, ta maida hankalinta gurin titi tana kallon motocin dake shigowa cikin asibitin a yayinda su suke kokarin fita. Lokaci zuwa lokaci yake kallonta haka nan yake jin takwanta masa a rai natsuwarta ya masa. Sau daya ta juyo ta kalleshi sai ya sskar mata murmushi ba ta sake kallonsa ba har suka isa bakin gate din Masarautar, sai da ta masa godiya sannan ta bude motar ta fita, be bar gurin ba sai da ta shige cikin Masarautar sannan yaja motarsa ya gaba. Cikin masarautar ta shigo rike da ledar maganinta dake cikin hijab, kai tsaye ta nufi bangaren Ammy, tana isa ta danna door bell din wata hadimar ta bude mata, babu kowa a katon falon sai ac da katuwar plasma, dakinsu yaran ta nufa, a hankali ta tura kofar ta shiga, sai ta samu Luma ta yi tana ta bachi, Labib kuma baya dakin, fita tai daga dakin ta sauka saka gaba daya ta nufi Garden daman da yamma haka a gurin take zama ko da yaran, balle yanzu da babu ko daya a hannunta.

SHATTIMA POV.

Ya farka da tunanin maganar da sukai jiya da Baba Waziri, babu abun da yafi tsaya masa a rai kamar maganar aure da kuma transfer, ba wai baya son zama kusa da iyayensa ba ne, irin halin da Mai Martaba yake ciki yana daga masa hankali gashi kuma idan yana gari dole ne sai an saka shi cikin harkokin sarautar. Sakon DSP Nura ne ya shigo wayarsa cewar police din daya bukata suna waje suna jiran Zainab, call list dinsa ya shiga ya kira Zainab ya sanar mata, sannan ya mike tsaye ya fito harabar gidansa, a zahiri motocin dake jera a harabar gidan yake kallo, abadini kuma zuciyarsa na can ta lula wani gurin da tunani. Juyawa yai koma ciki yana shiga ya tube tufafin jikinsa ya shiga bathroom yai wanka ya fito ya shirya cikin kananan kaya sai kamshin turare yake kamar wani sabon ango. Keys dinsa ya dauka da wallet dinsa ya nufi motarsa Baba Adamu na ganin haka ya taso da sauri.

“Ran ya dade masarauta zamu je?�

“No zauna abun ka ni kadai zanje�

Ya furta yana bude motar ya shiga, kamin yai warming din motar har mai gadi ya bude masa gate. Kai tsaye ya dauki hanyar da zata sada shi da masarautar daman can a ka'ida ba a masarauta yake kwana ba sai idan ta dauro, duk wani abun daya shafi masarautar yana nisanta kansa da shi domin ko kadan sarautar bata burgeshi. Tun daga babban gate din har cikin gida ake ta mika masa gaisuwa amman be amsa ko ka daya ba, daman can kasaita bata barinsa amsa gaisuwa balle kuma yanzu da tunani ya saka shi gaba. Yadda ya fito cikin motar yana takawa sai ka rantse da Allah ba zai mutu a saka a cikin kasa ba, kallo daya zaka masa kasan cewa jinin sarauta ne, domin sarautar ta nuna a tafiyarsa da maganarsa da isarsa da fuskarsa da kamalarsa ga wani irin kasaita a tafiyarsa kamar shi ne sarkin ma. Kai tsaye ya nufi bangaren Mai Martaba sai ya kararda shi yana bachi, hakan yasa ya dawo bangaren Ammy, sai da ya fara duban yaransa dake hannun Jekadiya sannan ya nufi dakin Ammy ba tare da ya tambayi mai rainonsu ba. Ammy bata dakin Sai Nana dake aikin mata abincike a wardrobe ganin Shattima yasa jikinta ya fara rawa.

“Ya Shattima sannu da zuwa�

“Yauwa Sis Morning baki je school ba�

“Eh sai gobe?�

“Why�

“Bana jin dadi ne, kuma na fadawa Driver yaje makarantar ya fada�

“Me ke damunki?�

“Fever amman an sha magani�

Tana amsa masa ta nufi kofa da sauri, shi kuma ya bita da kallo cike da kulawa. Tana fita Ammy ta shigo rike da plate din wainar kwai a hannunta.

“Morning Ammy�

“How are you?�

Ya dan tabe baki alamar ba Kalau ba.

“Tunani ko rashin lafiya?�

Ammy ta tambaya yana mika masa farantin.

“Tunani dai�

Sai tai murmushi.

“Waziri ba zai yi abun da zai cutar da kai ba, ni kaina na dade ina son ka dawo garin nan da aiki ka ki, yanzu kuma baka isa ka sabawa Umarninsa ba�

Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana kallon Ammy.

“Maganar Auren ma bana fatar ka saba masa, tun da har ya zabi rufe ido ya aura maka yarsa be kamata kace aa ba�

“I accept it�

Daga haka be sake cewa komai ba. Be koma bangaren Mai Martaba ba sai da suka fito daga sallah la'asar. Ko da ya shiga falonsa sai ya same shi a ciki zaune, ko'ina na falon duhu ne kamar dare, bayan kuma yamma ne akwai haske a ko'ina. Ganinsa a falo ma abun ma farinciki gurinsa domin a da kullum yana kan gado kwance, amman yau gashi akan kujera zaune. Kamin ya karasa kusa da shi yai masa sallama, Mai Martaba ya dago kansa a hankali ya kalli Shattima, wanda siffarsa da ke shimkide a siffar Shattima kallo daya zaka masa ka san jini daya ne. Gaban Mai Martaba Shattima ya zauna yana murmushi.

“Barka da Yamma Mai Martaba ya kufan jiki?�

“Alhamdulillah�

Mai Martaba ya amsa yana ta kallon Shattima.

“N ga jiki ya fara kyau Alhamdulillah�

Shattima ya fada cikin jindadi, sai Mai Martaba yai murmushi ya ce.

“An samu shigowa?�

“Eh Baba Waziri ne ya kira ni jiya, akan maganar fitar da kai waje da kuma aurena da neman transfer�

A hankali Mai Martaba ya sauke ajiyar zuciya.

“Hakan yana da kyau, ni kaina aurenka yana cikin rai na, neman transfer ma yana kyau, domin kai ne babba a yanzu, sai dai magana fita da ni waje a bar wannan maganar�

Shattima ya dago ya kalleshi.

“Saboda me? Ba san inda za a dace ba Mai Martaba duk fata muke yi�

“Hakan yasa nake son maka wata wasiya, na san matsalar auren nan yana damunka, ina son nai maka wasiya cewar kai ta aure ko da kuwa yau zaka aura gobe ta mutu, to jibi ma ka sake auren wata, a koda yaushe ina maka kallon babba a cikin iyalina, ina jin dadi da alfaharin da Allah ya bani kai a matsayin da, Omar ina maka wasiya da ka ji tsoron Allah, kuma ka rike yan'uwanka tsakani da Allah babu banbanci ko nunawa wani ya fi wani...�

A take jikin Shattima yai sanyi, sai ya ji kamar Mai Martaba na masa wasiyar bankwana ne. Shiru mai Mai Martaba yai na dan lokaci sannan ya cigaba.

“Rayuwa a gida da Family irin wannan akwai wahala, amman idan ka jure Allah zai taimakeka, bana son ko bayan raina a samu rabuwar kai a tsakaninku, bana son tsabani ko kiyayya ta shiga tsakaninku, ka yi kowa biyayya ka bawa kowa hakkinsa...�

Mai Martaba bai karasa ba Shattima ya katse shi jin kamar kunnuwansa da zuciyarsa ba za su iya daukar abubuwan da Mai Martaba yake fada masa ba.

“Inshallahu zaka samu sauki Mai Martaba�

Mai Martaba ya gyada kai.

“Sauki yana tafe da yarda Allah, amman sauki na har abada, sauki wanda daga shi babu wani ciwon Inshallahu, ni kadai na san me nake ji akan ciwon nan Omar, bayan ciwon jiki a nake kwana da shi kullum na tashi da shi, ga ciwon tsoron rabar mutane da tunani, na yarda wannan jarabawa ce, babban Sarki kamar ni ace bana iya shiga cikin mutane, bana iya sauraren al'ummata, ina jin tsoron abun da zan fadawa Ubangijina, ina jin kamar sauka ta cancance ni wata zuciyar kuma na raya min idan nai hakuri nan ba da jimawa ba zan tafi na bar Sarautar, ba barin sarautar ce tashin hankalina ba, yadda zan tafi n bar ku, rashin hadin kanku da irin matsalolin da kuke samu tun a yanzu da nake raye, babu uban da zai so ya tafi ya bar iyalansa a watse kansu a rarrabe, kai ne babba Omar dan Allah ka kula da yan'uwanka, na san na dora maka abu mai nauyi, amman Allah zai taya ka, ka bi Hajiya Bilki kamar Ammy, kuma kai ta hakuri da yan'uwanka, musamman Mama Aisha (Nana) ita ce karama a cikinku ita ce kadai ta tashi bata san gata da dadin uba, bata san ta rabe ni ba saboda lalurata, ka kyautata mata ka zame mata uba, kuma kai hakuri da halayenta akwai kurciya a tare da ita, sannan ka saka ido akan tarbiyar Karima, ka bi kanen mahaifinka kamar ni.... Kuma kai ta hakuri da rayuwa�

Shattima ya rufe idonsa da suka gama cika da hawaye.

“Inshallah zaka same ni mai cika umarninka Mai Martaba�

“Allah ya maka albarka�

“Amin�

Ya amsa yana jin kamar ya fashe da kuka.
Chapter 67 · 0% Book details