← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 172

Sashe 134

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Direban ya fada sannan ya juya da sauri ya fice daga office din. After ya fita Muhseen ya dauki wayarsa ya kira likitan ya fada masa ga yarinyar an kawo, yana dagowa sai ya ga tana kallonsa baki bude ta gwalo ido waje kamar zata yagasu, a hankali ya sauke wayar ya baro tebur din ya karaso kusa da ita yana yawo da hannunsa a fuskarta sai ya ga tana bin hannun da kallon sai kara fito da ido take. Wani irin ihu ta saka tai cikinsa ta rumgume shi da mugun karfi, kamin yai wani yunkiri ita da shi sun kai kasa...!

Ina mata wadan da suke son sayen kaya kamar su laces, atamfa, materials,shadda lace, normal shadda, atamfa lace, veil's, shoes and bags, da sauransu kuzo ga MAMAN AHMAD tazo dan tashare hawayenku kudai kunemeta ta wannan number 08032350261 banan kadai tatsayaba tanada kayan order kama dana kitchen,tufafi,kuma order ta Bata dadewa ,tana saida kayan gyara kamar su Al'ajabu,shu'umar humra wannan inbakida aure Bama saida maki,hadin kaza me yasin,akwai na mallaka wanda wannan ana rubuta shi atafin hannu ke zakiyi wannan,turaren wuta,kulacca,da sauransu
Mazauninsu nanan a samaru Gusau Zamfara state
Muna aika kaya kowace jaha da wajen kasar nan cikin aminci da yardar Allah kunememu kusha mamaki

https://wa.me/qr/MYY56BH3RMFDG1
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: Ina mata wadan da suke son sayen kaya kamar su laces, atamfa, materials,shadda lace, normal shadda, atamfa lace, veil's, shoes and bags, da sauransu kuzo ga MAMAN AHMAD tazo dan tashare hawayenku kudai kunemeta ta wannan number 08032350261 banan kadai tatsayaba tanada kayan order kama dana kitchen,tufafi,kuma order ta Bata dadewa, akwai turaren wuta,kulacca,da sauransu

https://wa.me/qr/MYY56BH3RMFDG1

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

“Abun kamar na Iska�

Ataa ta fada.

“Damuwa ma na saka haka�

Cewar Muhseen yana kai hannayensa biyu ya rika kanta, sai tai tsit kamar ba ita ba.

“Kina na saurarena?�

Ta yi shiru.

“Idan kina ji ki daga min kai ba sai kin yi magana ba�

Sai ta daga masa kai idonta a rufe.

“Ki daina kokarin tuna komai kin ji?�

Nana ma kam ta daga.

“Ki dauka wacan matar da mijinta da suka tsince ki yan'uwanki ne, ni Sunana Muhseen likita ne ni, zan rika kula da ke ina baki magani, so kina son ki dauke ni a matsayin yayanki and daga yau sunanki ....Yasmin�

Ya fada bayan dogon nazari.

“Da zarar kin ji ance Yasmin to da ke ake sai ki amsa, kin ji? Kuma idonki ma zai bude kin ji?�

Ta daga masa kai a hankali tana kokarin kwantar da hankalinta.

“Yasmin�

Ya kirata murya kasa kasa, da farko sai ta ji kamar ba da ita yake ba, can kuma sai ta amsa.

“Na'am...�

“Good girl�

Ya juya ya kalli Aliyu da Ataa dake tsaye bakin kofar dakin.

“Zan tafi da ita asibitin idan ta kama a kwantar da ita zan kwantar da ita a can, idan kuma dawowa zan zan dawo da ita nan�

“No ka kaita gidan Mama Fulani kawai�

Aliyu ya fada, sai Muhseen ya hanye hannunsa daga rikon kanta da yake, ya kama hannunta. Ya fito da ita dakin zuwa motarsa, har gurin motar Aliyu ya bi shi ya fada masa.

“Duk abun da ake bukata ka fada�

Muhseen dai be ce komai ba ya bude mata gidan gaba ta shiga sannan ya zagaya ya shiga mazauninsa yaja motar. Daga gidan be tsaya da ita ko'ina ba sai asibiti, farkon abun da ya fara bincika shi ne kwakwalwarta, a tunanin idam hankalinta y dawo zata iya bayanin yadda akai ta rasa idon ko kuma irin maganin da take kai. Hotuna ya rubuta mata har guda hudu kuma masu tsada ya saka wani ya kaita aka dauki hoton abun da ke cikin kanta, akai mata gwaje gwaje, at first what he thought is ko ta yi hadari ne ta rasa tunaninta da idanuwanta domin hatsari babu abun da be saka wa, daga ya fara tunanin ko an dura mata kokin ne, kamin ya fara tunanin wata kila damuwa ce tai mata yawa.
Sai dai abun da ya bashi mamaki a duk hotunan da aka dauka da kuma bincike da yai be ga wani abu da zai iya sakata haka ba, komai na kanta kalau yake.
Amman saboda ya tabbatar yasa yai magana da wani kwararen likitan kwakwalwa, sai dai be samu dubata a ranar kasancewar yamma ta yi sosai, ya dai yi alkawarin dubata gobe idan ya shigo asibitin. Sai da Muhseen ya gama komai da yake a cikin asibitin sannan ya sakata mota ya nufi gidan Mama Fulani da ita. Gidan yana nan a yadda yake kamar da a tsari da fasali, sai dai an canja fenti da furnitures. A harabar gidan yai fakin sannan ya bude motar ya fito ya zagayo ta bangaren da Fadime ta ke ya bude mata ya fito da ita.

“Yauwa ya ma sunanki?�

“Yasmin�

Ta fada a hankali.

“Yauwa na kawo ki gurin Mamana kuma mamankin daga yau ita ce mamanki, kuma a nan gidan za ki zauna kamin ki samu lafiya kin ji ko?�

“Too�

Ya riko hannunta suka nufi kofar shiga falon Mama Fulani. Door bell din falon ya danna, babu bata lokaci mai aikin ta bude masa kofa.

“Baaba�

“Na'am Alhaji an shigo�

Tsohuwar ta fada tana yar dariya.

“Eh me kika girka mana?�

“Aa ban girka da kai ba, ban san zaka zo ba ai�

“Mama na ciki?�

“Tana sama ina ga ko bachi take ne�

Ya shigo cikin falon yana rike da hannun Fadime, karasawa yai da ita gurin da set din Kujerun falon ya zaunar da ita.

“Baaba a kawo mata abinci da abun sha, idan ta gama a fada mata yadda za ta yi sallah please, sai dai bata gani�

“To Likita yanzu kuwa�

Baaba ta fada tana kallon Fadime. Muhseen ya nufi dakin Mama Fulani yana cire rigarsa suit dinta. Sai da ya kwankwasa sannan ya tura ya shiga, zaune ya same ta gaban laptop idonta sanye da farin gilashi tana duba wasu laces na manyan mutane. Shigowar Muhseen yasa ta cire gilashin ta kalleshi tana murmushi.

“Yau kuma?�

Ta tambaya domin ta manta when last su shigo gidanta da sunan sun dawo aiki shi da Aliyu, ba kamar da ba da kullum suna nan.

“Bakuwa na kawo miki�

“Bakuwa kuma?�

“Yes danki ne ya tsintota kin san shi da tsince tsince, kuma ya laka min ita�

Ya fada yana kokarin zama.

“Aliyu kuma? Ban gane ba�

A natse Muhseen ya fada mata komai, sai ta cika da tausayinta kamar ba Mama Fulani ba.

“Allah sarki ai ba a wulakanta mutum, baka san ko shi waye ba, wani lokacin ma har shi zai taimake ka, ina yarinyar take?�

“Tana kasa, gobe za a kaita asibiti ko ban biyo ta nan ba zan kira sai ki saka a mota direba ya kaita�

“To ba matsala, Allah sarki...�

Ta fada tana sauka daga kan gadon ta nufi kofar fita, Muhseen ya mike tsaye ya shiga bathroom, ita kuma ta sauko kasa tana kallon Fadime dake zaune a kasa Baaba na bata abinci a baki.

“Hajiya an sauko�

“Eh abinci ake bata ne?�

Mama Fulani ta amsa ma Baaba tana zaunawa.

“Eh na ga zata bata jikin ne shiyasa na soma bata da kaina�

“Allah sarki baiwar Allah ya sunanki?�

“Yasmin, wannan yace na Yasmin ne sunana kuma yace ke ce Mamana�

Mama Fulani ta rausayar da kai tanawa da Ataa.

“Eh haka ne ai da na kowa ne, sannu Yasmin sannu kin ji Allah ya baki lafiya�

Fadime ta daga kai tana tauna abinci. Sai da ta ci ta koshi sannan Baaba ta dauke plates din ta bata ruwa ta sha, ta kama hannunta suka shiga dakinta ta zuba ruwa a buta tai mata alwala ta yadda zata fi fahimta sannan ta saka ta tace tai da kanta, da ido rufe ta kokarta ta yi yadda Baaba tai mata tana ta son ta tuna minene alwala sai ta soma jin abun irin na dazun, take ta kawar da tunanin kamar yadda Muhseen ya fada mata. A gurin sallah kam Baaba daga mata hannu take tana nuna mata yadda za ta kabbatarta sallah, a gurin ruku'i kuma sai ta rikata ta lakwasa yadda zata gane.

BAPPA POV.

Tun da Bappa ya doro gidan ba tare da Fadime ba, Inna ta gane akwai abun da ya faru, sai dai bata masa magana ba duk kuwa da son ganin Fadime da take, sai da ta ba shi abinci ya ci ya koshi ta ba shi ruwa ya sha ta zuba masa wani yai wanka ya gabatar da sallah la'asar sannan ta zauna a inda ya gama sallah tana ta kallonsa kamar ta tambaya ina yarta kuma tana fargabar irin abun da zata ji. Bappa na ganin irin zaman da tai ya san cike take da son ta ji labarin komai. Tunanin ta inda zai fara bata kabarin ya fara, daman ya tafi ya barta ba dan lafiya ta ishe ta yanzu kuma idan ya labarta mata abun da ya faru ya za ta ji?

“Ko dai wani abun ya same ta n Malam?�

Sai da Bappa ya tattaro dukan kuzarinsa sannan ya iya labartawa Inna abun da ya faru, take ta fashe da kuka tana masa magana da yalshen fulatanci.

“Ka ce min kawai na rasa Fulani, damn ita kadai ta tsaya a cikin yayan yanzu kuma na rasata...�

Kuka ta saka sosai wanda ya saka jikin Bappa sanyi wanda har ya ji ina ma ya tsaya a can a bincika ko za a ganta, shi kansa ba wai baya son Fadime ba ne, bacin rai ne ya saka shi haka bacin rai da har yanzu be bar zuciyarsa ba.

“Sai da na ce maka karka je, wata kila zuwan ku ne ya saka ya dauke ta ya kaita wani gurin, babu yadda ban yi da kai ba akan karka je garin nan amman baka ji ba, yanzu ga shi nan ka saka ya sake dauketa wa san inda zai sake jefata? Gashi ba gani take ba�

Bappa ya ja tsaki.

“Ai duk laifinta ne, yarinya bata jin magana kom...�
Chapter 134 · 0% Book details