← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 172

Sashe 19

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ya fada a fili sannan ya mike tsaye, da gaske he miss her, Allah ka dai ya san irin karyar da tai, da kuma irin sakin da za tayi, no wait ta ma isa gida? What if inda ya barta wani abun ya same ta? Ko ta bi wani kamar yadda ta bishi, ai ba kowa ne na gari ba right? Idan ta nunawa wani kudi zai ma iya kidnapped dinta. A take hankalinsa yai mugun tashi wayarsa dake aljihunsa ya ciro ya chiga contacts sai a lokacin ya tuna ai shi ya bata number sa kuma bata kira shi ba.
Gaba daya sai ya ji ba shi da natsuwa tunaninsa be kawo masa haka ba sai yanzu, and if wani abu ya same ta shi ne sanadi, domin shi ya barta a gurin kuma ya san abunda yai be kyauta ba. Gaba daya sai ya ji hankalinsa yai mugun tashi, be bari Anti Rabi ta fahimci komai ba ya shiga dakinsa ya cire vest din jikinsa ya dauki wata bakar t shirt ya saka ya fito.

“Anti bari na leka nan waje�

“To Allah dai ya tsare idan ka ji baka natsu ba ka dawo gida dan Allah�

“Okay In-Sha-Allah�

Sai da yai addu'ar fita daga gida sannan ya fita gidan. Kai tsaye gurin aikinsa ya nufa duk da ya san ba lallai ne ya ganta ba, sai dai sanin cewa tana yawan zuwa gurin wata kila ma an zo nemansa.

SHATTIMA POV.

Ya saba every end of the week yana ziyartar dakin motsa jiki, but wannan karon sati biyu be je ba saboda be samu zama ba. Hakan yasa yake jin jikin kamar ba nasa ba, tafiya yake a hankali kamar wanda baya son taka kasa da daidaiya yake bin ko'ina da kallo har ya shigo bangaren mahaifiyarsa.
A falo ya tararda yaransa, Iya na zaune kusa da su tana musu wasa sai dai gaba dayansu wani laye suke kamar basu jin bachi.

“Babban Mutum an shigo?�

Iya ta fada baki har kunne.

“Eh Iya ya gidan?�

Ya amsa mata yana leka yaransa.

“Gashi nan fa sun sha ado, yanzu na gama gyara dakinsu�

Da mamaki ya kalleta.

“Mai gyaran bata zo ba ne?�

Iya ta tabe baki tana mikewa tsaye.

“Wannan yarinyar, bata zo ba, wata kila sai gobe ko jibi�

Shattima be ce komai ba, but maybe dan ta kamata tana yi ma yaransa addu'a ne yasa ta ji tsoro ta ki dawowa.

“Karka damu ba dole sai an kawo wata ba, ni kaina zan iya kula da su da dakinsu�

Dan murmushi yai.

“Haba Iya ai ba girmanki ba ne, idan bata dawo ba dai za mu samu wata�

Iya ta yi murmushi tana kallonsa.

“Haka ne Allah ya taimaka, bari na maida su dakinsu�

“Amman a samo wacce zata tsaya da su bana son a na barinsu su kadai�

“An gama Babban Mutum�

Ta amsa masa har da dan risinawa, shi kuma ya wuce dakin mahaifiyarsa. Kwance ya same ta waya a hannunta tana latsawa, sai da ya zauna sannan ya mika mata gaisuwa. Sai ta dago ta kalleshi.

“Lafiya Kalau Shattima�

“Ammy ina tunanin gobe zan koma�

Bata ce masa komai a har na tsawon minti uku. Hakan yasa ya sake cewa.

“Amman ba zan yi dadewar wacan lokacin ba zan dawo�

“Ya dai kamata ka nemi transfer gaskiya, ka fi kowa sanin halin da mahaifinka yake ciki�

Kwankwaso kofar dakin da akai ne ya hana shi cewa komai, be kuma dago ta kalli kofar ba, sanin wanda ya shigo dakin ba bayan Ammy ta ba shi umarni, kamshin turaren kadai ya isa ya sanar nasa cewer Sirleem ne domin ya san kalar turarensa kamar yadda Sirleem din ma ya san na Shattima. A kasa ya zauna yana mikawa Ammy gaisuwa sai ta amsa masa da murmushi tana kokarin tashi daga kwancen da take.

“Ya gida ya aiki?�

“Alhamdulillah, dazu Hajiya ke Fada min Nana ta samu accident�

“Eh amman da sauki sosai�

“Allah ya tsare gaba�

“Amin�

After some minutes ya mike tsaye yana mata sallama.

“Shattima ba ku gaisa ba�

Daga shi har Shattiman ba su dadin maganar Hajiya ba. Domin kowa jin kansa yake ba ma kamar Shattima, ko da wasa Shattima be dago ya kalli Hajiya ba gudun kar ta masa umarni da ido cewar ya gaisa da Sirleem domin shi ya cancanci Sirleem ya gaushe shi ko dan neman auren kanwarsa da yake. Sirleem ya kasara inda Shattima yake zaune ya mika masa hannu sanin cewar idan za a shekara dari a haka Shattima ba zai ce masa uffan ba.

“Shattiman ai ban kura da kai ba sai yanzu�

Sirleem ya fada yana mika masa hannu. Hannun kawai Shattima ya mika masa suka gaisa ba tare da ya kalli Sirleem ba balle har wata kalma ta fito daga bakin Shattima. Sai da Sirleem ya nufi kofa sannan Shattima ya daga kai ya kalleshi, sai kuma ya dauke kai ya kalli mahaifiyarsa wace ke kallonsa tun lokacin da Sirleem ya mika masa hannun.

Sam Sirleem be jidadin abunda Shattima yai masa ba, ya sani ba tun yau Shattima ya saba nuna masa cewar shi ne dan masu gida shi kuma agola, ba shi kadai ba har Zainab wacce kusan matsayinsu daya da shi haka take nuna masa isa tana takama.
Kamin ya karasa fita falon Nana ta kira shi.

“Ya Sirleem�

Juyowa yai ya kalleta be ce komai ba, sai da ta kalli kofar corridor dakin Ammy sannan ta karaso inda yake.

“Ya jikin na ki?�

“Na ji sauki, Ya Sirleem ban karya ba�

“Why?�

Ya tambaya cike da mamaki ganin har 5pm ta kusa ace bata karya ba. Sai da ta sake kallon corridor sannan ta ce.

“Dan Allah zaka kai ni restaurant na ci abinci? Amman karka tambayi Ammy?�

Ya kalli inda take kallo sai kuma ya kalleta kamar ya musa mata sai kuma wata zuciyar ta hana shi.

“Alright muje�

“Kaje can bangarenku ka jira ni, bari na dauko mayafina�

Har ta juya sai ya kira ta ta juyo.

“Nana... An hana ki fita da ni ne ko me?�

“Zan fada maka a mota kaje can ka jira ni�

Bata tsaya jiran abunda zai ce ba ta koma dakin ta dauko kudin da Hajiya ta bata 20k ta saka a cikin skirt dinta sannan ta saka wani karamin veil ta fito da gudu kamar ba ita ce ke ciwon kafa ba. Kamar wacce tai wani kaifi take tsoron a ji haka ta sauka stairs din ta nufi bangarensu Hajiya gabanta sai faduwa yake kar tai arba da Shattima ko Zainab ko wani wanda zai fadawa Ammy ta fita tare da Sirleem.

Can bangaren Hajiya ta nufa sai dai bata shiga ciki ba ta nufi gurin da motocin gidan suke, tun kan ta karasa ya bude mata front seat tana shiga ta rufe motar da sauri.

“X&Y restaurant za mu je, kuma ba fita za ka yi ba, ni zanje nai mana takeaway Please�

Jinginar da kansa yai jikin motar yana kallonta. Can kuma ya tashi motar suka fara tafiya.

“Waya hana ki fita da ni hala?�

“Babu�

Da bashi amsa tana taba kudin da ta boye jikinta dan ta tabbatar idan suna nan.
03/12/2021, 08:22 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄*

By Khadeeja Candy

*10*

FALMATA POV.

Haka ta kwana da ragowar yunwa a cikinta, washe gari tun da asubar fari Tumba ta fito ta fara kunna wuta a lokacin Falmata na waje tana alwala sallah asuba, baya ta gama ta shiga daki ta dauki hijabinta zata saka tai sallah sai ta ji an rikota sakamakon kiran da ta yi ta mata bata ji ba.

“Karki sallah bari ki yi wanka�

Ta rada mata a kunne, ba ta isa tace mata bari na gama sallah ba, dan haka ta aje Hijabin ta fito bakin kofar dakin ta zauna tana ta kallon wutar da Tumba ke ta aikin fetawa tana tura ledodi, nan da nan ruwan sukai zafi sai ta dauko wani garin magani ta zuba a cikin ruwa ta juya shi sannan ta sauke ta tsirka mata da ruwan sanyi.

“Zo dauki ga shi nan ki yi wanka maganin tsari ne�

Tana maganar tana mata alama da abunda take nufi irin yadda ake ma kurame. Falmata ta tashi daga inda take zaune ta dauki ruwan maganin ta shiga bandaki ta cire kayan jikinta ta watsa ruwan ta fito. Da hannu tai mata a alama da ta zo, sai Falmata ta aje bokitin hannunta ta karasa inda take tsaye, duba ta tai dan ta tabbatar idan ta yi wanka, ga kuma shaida ta gani maganin ko'ina a jikinta.

“To je ki yi sallah ma�
Chapter 19 · 0% Book details