Sashe 24
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta mike tsaye ta fito daga dakin zuwa inda mahaifiyarta take zaune tana kiranta.
“Gashi nan an gama dauki ki je�
Sai ta gama kirga gidar ko ta nawa ce sannan ta dauka ta dora saman kai, ta koma can kusa da dakinta ta dauki wani karen zana ta fice daga gidan. Dandali ta nufa tana tafe tana rera wakar da ake a dandalin ta Fulatanci, tun kan ta isa ta hango yadda dandali ya cika da mutane masu sana'a sun baza, masu samari kowa ya ja tashi gefe suna fira, masu rawa da wasar dandali na yi. An kunna wutar kara ta kama sosai ta haske ko'ina na gurin. A gurin da ta saba zama ta zauna ta aje gidar dake kanta a gabanta tana bawa idonta abinci.
Sai kusan sha daya sannan kowa ya watse wadanda sukai ciniki sun yi, masu samari kuma akai sallama kowa ya nufi gidansu. Ita ma kanta a gajiye ta dawo gida tana hamma, ko da ta iso Inna ta gyara mata gurin kwanciyarta sai kawai ta shige dakinta ta kwanta. Misalin karfe biyu suka fara jin tafiyar jakuna a rufin dakin na zana, can kuma ta fara kukan mage, kamin ta koma kiran sunanyen mutanen gidan. A take Fadime ta tashi zaune ta kwala wani uban ihu tana kiran sunan Babanta.
“Bappa Bappa Bapppa.......�
Kamar jira ake sai ta fara jin kokan magen a bakin bukkatar tana koyonta da sautin kukan magen.
“Bapkwau Bapkwau�
Sai kuma ta ji tafiyar dakuna a tsakar gidan, har da wani tuma suke suna direwa, sai kuma ta ji kamar kukan kare, a lokacin ne tai ihun na gaske wanda ya farkar da Bappa daga bachin da yake domin shi idan sabo ya saba da irin wannan abun, dan haka baya hana shi bachi ita din dai ce da ta kasa sabawa kuma a duk lokacin da ta ji sai ta yi ihu ta kirashi. Da sauri ya budewa zagen da suka sako wanda shi ne murfin bukkar ya fito, sai yai arba da bakar mage tsaye a kofar bukkar Fadime, cikin kuzari ya nufi inda tabaryar gidanta take ya dauk ya jefeta da ita da sauri tai tsalle ta haye saman bukkar tana masa kuka sannan ta sauka da can baya.
“Bappa....�
“Kone Fulani addu'a akai idan kajji haka haba, kai kullum in zaka kwanta baka addu'a Fulani�
“Ni addu'ar wuya take ba ni�
Ta fada bayan ta ga mahaifinta a cikin bukkatar yana lalaben inda take ya riko hannunta suka fito, komawa yai da ita dakinsu ya saka ta a ta su bukkar, ya kunna ashana ya lika a kyandir yai mata shimfida a kasa, shi kuma ya hau saman gadon karan ya kwanta, mahaifiyarta na daga gefe kwance sai kwasar bachinta take.
03/12/2021, 08:22 - ðŸ¤ðŸ¤ðŸ¤ðŸ¤: *ðŸ„🄠FULANI ðŸ„ðŸ„*
By Khadeeja Candy
*12*
SIRLEEM POV.
“Tun kwanan baya nai maka maganar, ya kamata mu fara hada lefe ba ka ce min komai ba�
Ya daga kansa ya kalli Mahaifiyarsa, kamin ya sake kallon Jarma wanda tun da suka gaisa be sake ce masa komai ba, sai kuma ya sake kallon mahaifiyarsa.
“Yarinyar da aka ce sai ta gama makaranta, idan mu ka ce za mu hada lefe yanzu ai mun yi sauri�
“Ba dole sai ta gama makaranta za ayi auren ba, ba zan iya jira har lokacin ba, idan muka hada komai mu kai musu su ce ba za su karba ba�
“Amman already an yi wannan alkawarin ai, be kamata mu tayar ba�
“To ni na tayar sai ya? Malam ka fara bada kudin da za a hada maka lefe kaji�
“To In-Sha-Allah�
Ya mike tsaye yana gyara rigarsa ya fice daga dakin. Da wani kallo mai kamar harara ta bishi har ya fice, sannan ta kalli Jarma.
“Yaron nan idan ba mu yi da gaske ba, zai iya ba mu kunya�
Jarma yayi murmushi.
“Karki ji komai Hajiya, ai yana da biyayya ba zai tsaba miki ba, yanzu matsalarmu guda biyu ce, Mai Martaba da kuma Shattima, kuma na sama mana mafita�
Hajiya ta mike tsaye duk da isar da take ji da kasaitarta ta isa bakin kofar ta saka mata key sannan ta dawo ta zauna.
“Wace mafita ce?�
Jarma yayi murmushi a karo na biyu sannan ya ce.
“Akwai wani gari can yamma da Katsina, garin wasu matsafa manyan arna, ance aikinsu kamar yanka wuka yake�
Hajiya ta dauke kai cike da kasaita.
“Na saba jin irin wannan daga bakinka, sai mun gwada kuma mu ga ribar yar adan ce, ni yanzu masu yi da gaske na ke nema�
“Wannan karon masu yin da gaske ne Hajiya, domin su ba a musu aike sai dai mai sako ya isa da kansa, bari ki ji na fada miki a yadda aka ba ni tarihin garin basa bako, sai da sanin manyan gari gudun kar rayuwar bakon ta shiga hadari, wanda ba jinin garin ba baya zama garin. Sannan aikinsu kamar yankam wuka ne, sha yanzu magani yanzu, tun kan ki fadi bukatarki za su sanardar ke dalilin zuwanki da inda mafita take, ke bari na baki wani labari gaba daya jama'ar garin ba su yarda da wani abu wai cigaba ba, na zamani ko mai moriyarsa, in yanzu kika ce a kashe miki Shattima take za su masa harbin kasko su aika shi lahira, mayan yan siyasa da masu kudin garin nan ance can suke yada zango dan biyan bukatunsu�
Cike da gamsuwa Hajiya take kallon Jarma, yadda ya koda mata mutane da ace ba a gaske haka suke ba, zata iya yarda domin ta ji abunda ta dade tana nema.
“A ina ka san su Jarma�
“Wani abokina Malam sa'idu ne ya fada min su, shi mutumen Bandalo ne wani kauye da ke Katsina, sai dai cirani yake a garin nan sai dai shi din amintaccen na ne�
“Mutumen da zai iya rike mana sirrinmu ne?�
“Idan ma zai tona mana asiri, sai dai ya fadi cewar ina nemawa yata maganin aure ne, domin na fada masa yata Nafisa ce take fama da bakaken aljannu da suka hana ta lafiya kuma suka hana ta, sai ya bani shawarar cewar da zan iya da naje can zan samu gani a take�
Murmushi mai kyau Hajiya tai tana kallon tv dakinta kamar da gaske hankalinta yana can.
“Jarma sarki wayau�
“Hajiya kenan, wani ai be isa ya san sirrin mu ba, sai dai zuwan ne da kamar wuya a yanzu�
“Zuwa ba shi da wahala duk inda samu yake zan iya kai kaina, ba ni da kowa a katsina amman zan iya karyar zuwa wani gurin sai mu je can, matukar zan samu biyan bukatata Jarma, bana tsoron ratsa ko'ina zuciyata a bushe take�
“Zan neman takamaimen inda garin yake, da inda ya kamata mu sauka da kuma wanda zai magana jagora a cikin garin�
“Ka nemo Jarma amman ka tabbatar idan muka tafi ba zuwan banza za mu yi ba, za mu samo maganin ciwon mu�
“In-Sha-Allah�
Daga haka yai mata sallama ya fice daga dakin, ita kuma ta mike tsaye ta isa gaban windows dakinta tana kallon bayan gidan, ji take kamar ta runtse ido ta ganta a garin.
FADIME POV.
A yau ma sai da ta rubuta domin ta yi mafarkinsu, sai dai a yau mutum biyu tai mafarki da nai busar sarewar nan da kuma dayan da yake tsaye a gefensa dukansu sun bata baya ne.
Daga bukkatarta ta fito ta nufo inda Inna da Amo suke zaune suna maganar sarautar garin.
“Ni ina ganin kamar abun nan zai zama rigima ne, tun da duka yayan suna son sarautar fa�
Amo ta lashi baki da wata uwar tsaga da ta bata mata fuska tace.
“Mu dai na mu ido, ban da rashin hadin kai, yayan uku ba za su hakura su bar wa daya ba? Wannan ai ba burgewa ba ce�
“Ni ma dai haka na ce�
Fadime na zuwa ta zauna kusa da mahaifiyarta ta kwanta jikinta.
“To mage sarkin son jiki daga ni�
Da sauri Fadime ta dago ta kalli Inna wacce tai mata maganar.
“Inna jiya ma sai da mage ta zo�
Hanzarin tashi tsaye Amo tai ta dauki kwayar danyen manshanunta ta dora saman kai.
“To muka zamu bunni sai wada hali yai�
Bata ko tsaya jiran abunda Inna zata ce mata ba ta saka kai ta fice daga gidan da saurinta, har kusan karo su kai da wata makociyarsu wacce ta kunno kai cikin gidan rike da takarda hannunta.
“Maraba da Nene�
“Na yalle dam Inna Fadime�
“Janfelen�
“Na sukkaɓe?�
“Janfelen, na wurinde?�
“Janfelen�
Ta zauna inda Amo ta tashi tana mikawa Fadime takardar hannunta.
“Fadime karanta mini injiya minana Mai samari yak aiko min�
Fadime ta karbi takardar ta bude tana karanatawa, gaisuwa ce farko sai tambayar lafiyar mahaifiyarsa sannan ya sanar da ita sakon kudin da ya aiko mata dubu bakwai ta hanyar abokinsa, dan rani.
“Munafwuki amman be ba ni komai ba, sai wasika, yalla ya aza babu me karanta min ita, bari naje yanzu na iske shi, mugun ba'adare�
Inna ta saka dariya ita da Fadime dan sun san halin Nene da kudi bata jin has. Nene ta fita daga gidan sai fada take ko sallama bata tsaya yi ma Inna ba.
“Fadime tashi ki tahi rahe ki samo mana diyam�
A take ta bata fuska ta fara shura kafafuwanta.
“Inna ko hutawa ban yi ba, yanzu na farka daga bachi ai�
“Wallahi ina sa miki sanda yanzu, wa zai dauko ruwan ni?�