Sashe 60
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani dogon numfashi Kawu Manu ya sauke sannan ya juyo yana kallon Bappa.
“To yanzu ya ake ciki? Kai kana ganin wannan abun da take yin kanta ne?�
“Kawu ga zahiri kana gani, shiyasa na kiraka ka zo ka tafi da ita�
Cewar Bappa, sai Kawu Manu yai wani murmushin takaici.
“Ka kyauta Sama'ila, duk yadda ake ka yi, Allah ya saka maka da alheri, ke kuma ki jira sakamakonki�
Ya karasa yana haska Inna d Fadime, sannan ya kama hannun Amo.
“Ba ni da sakamako sai alheri, sherinka ya bika, ka ga mugun abu kai da yarka can mukan alheri zamu gani da yardar Allah�
Uffan be sake ce mata ba, yana dai rike da hannun Amon har suka fita, sai da dansa ya fara hawan babur din sannan ya dora Amo a baya, hajjo ta hau sannan shi ma ya hau a baya suka kama hanyar garin Dan-Isa.
FALMATA POV.
Sai da suka yi bachi sannan ta fito daga dakinsu, a falo ta samu Ammy da Jekadiya da kuma wata bakuwar suna gaisawa, har inda Ammy Falmata ta karasa ta risina kasa ta kwashi gaisuwa sannan ta mike tsaye ba tare da ta ji amsawarta ba, daman ba amsarwa take jira ba ita dai muradinta ta gaishesu ta tafi gida ganin dare ya soma yi sosai gashi a kafa zata je, sai ta fito waje ta kara tsinkewa ganin hadari ya hada ko'ina a garin iska sai kadawa yake. Cira kafa tai tana kallon sama gabanta ya fadi yadda hadarin ya hadu yana da wahala ta iya isa gida ba a sako ruwa ba. Ta baro gate din gidan sai ta tsinci kanta ita kadai a unguwar sai wata mota dake can gefen titi a fake, arzikinta daya unguwar manyan mutane ce ko'ina a haskake yake kamar wani gurin taro. Daga nesa aka dallo mata fitilar motar dake fake har sai da ta tsaya cak sai kuma aka kashe, aka sake dallo mata aka kashe sosai hakan ya firgitata wanda ya saka har ta juyawa ta waiga bayanta tunanin komawa take a masarautar, ganin hakan yasa Sirleem ya bude motar ya fito ya nufo inda take tsaye, tun kan ya karaso ta gane shi, hakan yasa ta dan ji sanyi har tai kokarin daidaita natsuwarta. Kallon mamaki yake mata tun da ya hango ta ta fito daga masarautar ya gane ta, sai dai mamakinsa me ta zo yi a nan? Ko wani take nema?
“Uhmmm�
Ta furta yana nunata kokarin tuna sunanta yake amman ya kasa.
“Me kika zo yi nan?�
Ganinta tana ta Kallonsa ba amsa yasa ya tuna cewar bata ji sosai, sai ya matsa kusa da kunenta.
“Me kike a nan?�
“Aiki nake yi�
“A ina?�
“A gidan Mai Martaba�
“Aikin me?�
“Raino nake ina kula da wasu yara�
“Oh ke kike kula da yaran Shattima kenan�
Ya fada da sigar da ba zata ji yana dan mamaki. Kamin ya sake kai bakinsa a kunnunta.
“Kike kaiwa dare haka ba ki jin tsoro�
“Ina ji su suka ce ba zan tafi ba sai yaran sun yi bachi�
“Kasa kike tafiya?�
Ta daga mishi kai, sai ya ji tausayinta ya kara kama shi, as her age ace tana bin hanya zuwa gidansu a kafa kuma a irin wannan lokacin.
“Babanki ya san kina aikin nan�
Wannan karon ta sigar da zata ji yai mata tambayar, sai ta daga masa kai ta maida idonta kasa tana ta wasa da hannayenta cikin hijab dinta.
“Kuma ya aminta ki kai irin wannan lokacin a waje?�
Nan ma kan ta daga masa tana kallon hadarin dake haduwa a garin.
“Ina ne unguwarku?�
“Unguwar madinka�
“Muje na sauke ki�
Yana fadar hakan be jira cewarta ba ya juya ya nufi inda motarsa take fake, ita kuma ta bishi a baya tana masa kallon mamaki, a iya yadda ta fahimta ko kadan Sirleem be da rayuwar wulakancin ko kyamar mutane ba kamar sauran celebrities ba.
Tsayawar da yai yana magana da Falmata yasa ran Mansura daya baro a mota ya bace, gashi tana hangensa sai kai bakinsa yake kunnen Falmata zuciyarta sai tafarfasa take kamar zata fasa kirjinta ta fito, tana ganin sun doso motar ta bude ta fito tai tsaye hannunta rike da ganbun motar. Sirleem na iso gurin motar ya budewa Falmata back seat.
“Zo ki shiga nan�
Kamin Falmata ta karasa Mansura ta daka mata wata muguwar tsawa.
“Keeeeeee!�
A zarane Falmata taja ta tsaya tana yi ma Mansura kallon tsoro, ba kasafai take jin komai ba amman ta ji wannan tsawar da Mansura tai mata cikin daga murya.
“Ban gane ta zo ta shiga ba, ashe Sirleem kana tare da yarinyar nan biyoka take har gida... Amman ni yanzu ka gama fada cewar kar na sake biyoka gida, amman ita har cikin gidanku take shiga�
“Ba abun da kike tunani ba ne, I'm just helping her�
Ita ce amsar daya bata cikin natsatsiyar murya yana kallonta da manyan idonsa masu kyau da haske. fashewa Mansura tai da kuka akan Sirleem bata ji zata iya saurara ko wace mace balle kuma Falmata da a sanadinsa ya santa.
“Zo ki shiga�
Sirleem ya fada yana kallon Falmata wacce ta tsaya kallonsu duk kuwa da bata jin abun da suke fada amman ta san fada suke. Kai ta girgiza masa da mugun tsoro.
“Aa zan tafi a kafa...�
Tana rufe baki aka fara saukar da yayafin ruwan sama, barin jikin motar Mansura tai tana kallonta.
“Shiga�
Ta fada a tsawace, ganin hakan yasa Falmata ta nufo motar da zimmar shiga, kamin ta karasa Mansura ta rika kanta ta buga da murfin motar na front seat iya karfinta, wani irin mahaukacin ihun Falmata ta saka tai baya da sauri ta fashe da wani irin mahaukacin kuka.
“Baki da hankali Mansura me yake damunki? Taya za ki cutar da innocent girl, miyasa kike abubuwan hauka wai?�
Cikin wani irin tsawa da fusata yake fadawa Mansura haka jinin zuciyarsa na wani irin zillo, domin ba karamin baci ransa yai ba. Yadda yake jin tausayin Falmata da ace ba Mansura ce ta taba ta da sai ya dake ta ko waye kuwa. Falmata kan firgicewa tai ta fara tafiya tana kuka ga ruwa ya fara sauka da karfinsa, cira kafa yai yai hanzarin cin mata ya riko hannunta.
“Zo nan a duba miki�
Da sauri ta girgiza masa kai tana kuka duk da bata ji abun da ya fada ba.
“Aa aa a kafa zan tafi�
Be bi ta kanta ba ya rike hannunta ya nufo motar da ita, da kansa ya saka ta a motar ya rufe ya zagaya dayan bangaren yana yi ma Mansura wani kallo na bacin rai.
“Wallahi kika sake cutar da wani akaina sai na baki mamaki�
“Ba ni da hankali akanka Sirleem kai min duk abun da zaka min, amman ba zan lamunci ganinka da wata mace ba, kuma Wallahi idan baka rabu da yarinyar nan ba sai na kasheta�
Uffan be sake ce mata ba, ya bude motarsa ya shiga tana ganin haka ita ma ta shiga front seat din ta rufe motar tana ta kuka, kamar Yadd Falmata ma take ta kuka tana jin goshinta na mata wani irin zugi na bala'i ga jini sai zuba yake, gaba daya a firgice take har wani zazzabi take jin yana kokarin rufe. Key yai ma motar ya hau titi har ya isa wata silent unguwa be kalli inda Mansura take ba, gaban wani madaidacin gate ya faka sannan ya juyo ya kalleta.
“For the very last time kar na sake ganinki kofar gidanmu ba tare da izinina ba, and ki shiga hankalinki i won't tolerate nonsense�
“Ka kira abun da nai da nonsense? Fine, idan baka rabu da yarinyar nan ba sai na kasheta Wallahi, Wallahi zaka jama mata bala'i�
Ya karasa cikin kuka sannan ta bude motar ta fita tana haki. Sosai Falmata dake bayan motar ta sha jinin jikinta tsoro ya gama kamata, duk abun da Mansura ta fada ta ji saboda ta fada a fusace ne da kuma muryar da Falmata zata iya ji. Sai ta fashe da sabon kuka jikinta sai kyarma yake daman ac motar ya gama ratsa kassan jikinta har ya soma saukar mata ta zazzabi.
“Ka sauke ni a nan... �
Ta fada muryarta na rawa hakoranta na kasa na haduwa da na sama. Juyawa yai ya kalleta for no reason ya ji ta kara bashi tausayi domin har numfashinta wani sama yake kamar zai bar jikinta, silently ya sauke ajiyar zuciya ya juya ya cigaba da tukin, zuciyarsa bata raya masa ko'ina ba sai gidan Momy. Kai tsaye ya nufi can duk kuwa da kasancewar ba shi da tabbacin tana gidan a irin wannan lokacin kasancewarta likita. A kofar gidan ya faka ya bude motar ya fito ya zagaya side dinta ya bude mata.
“Fito�
Ba musu ta sauko da kafafuwanta sannan ta fito gaba daya tana hawaye kamar ba gobe, ga zafin da goshinta yake mata ga kuma tsoron maganar Mansura sai ta ji abun ya hade mata ya zame mata biyu a lokaci daya.
“Zamu je ciki Momy ta duba ki sai na kai ki gida�
Ya fada mata saitin kunnenta, ita dai bata ce masa komai ba, har ya rika hannunta ya doshi gate din da ita yai knocking mai gadin ya bude ganin Sirleem yasa shi washe baki.
“Ranka ya dade kai ne ka tsaya waje?�
“Bana son bata lokaci na shigo da motar ne, fatar dai Momy tana nan�
“Eh Hajiya tana ciki�
“Okay�
Ya fada yana nasa kafarsa cikin dakin bayan mai gadin ya bashi hanya, a lokacin ruwan sai sauka yake da dan karfinsa sai dai be damu da ruwan ba tafiyarsa yake a natse har ya isa gurin kofar ya kwankwasa kofar falon. Sai da ya ji motsin taba kofar da ake ana kokarin budewa sannan ya saki hannun Falmata. Wani kyakkyawan saurayi ne da ba zai wuce 23-24 ba bude musu kofar, Sirleem ya mika masa hannu suka gaisa.
“Ameer kana nan ashe?�
“Eh Wallahi hutun be kare ba�
Ya fada yana janyewa jikin kofar wanda hakan ya bawa Sirleem da Falmata damar shigowa falon.
“Zauna a can�