Sashe 79
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shigowar Shattima dakin yasa ta fita daga falon Ammy gaba daya, sai da ta sauko kasa da zimmar zuwa garden sai ta tuna cewar Jurry tace ta zo ta yi ma Hajiya gyara. Da sauri ta juya sai kuma ta aikawa kanta wata tambayar, anya idan ta fita bata fadawa Ammy ba ba zata yi laifi ba? Hakan yasa ta koma cikin falon sai dai bata tararda da kowa ba, har ta zauna sai kuma ta ji tsoron kar ita kuma wacan ta ce bata zo ba, hakan yasa ta mike tsaye ta fice daga bangaren gaba daya. Da dan tsoro ta shiga bangaren Hajiya domin bata taba zuwa gurin ba sai yau, shi ma tsarinsa kamar na Ammy ne, banbancin na Ammy daga dama ne na Hajiya kuma daga hagu. Tana daga kai sama ta kalli stairs din ta hango Jurry tsaye rike da waya tana kallonta, Falmata ta kara cira kafa cira kafa ta hau saman ta risina gaban Jurry.
“Ranki ya dade ga ni�
“Okay biyo ni�
Ta fada tana mata alama da ta biyo ta din domin ta san ba lallai ne ta ji ba a yanayin da tai maganar. Falmata ta mike tsaye ta bi bayanta har suka shiga ciki, wannan bangaren ma ya hadu ya ji kayan alatu da abubuwan more rayuwa na zamani, tsarinsa da fentin da kofar irin na Ammy ne furnitures ne kawai banbanci. Tun da Falmata ta shigo falon kanta a kasa yake, hakan nan ta samu kanta da rashin sakewa kamar yadda ta saba a bangaren Ammy duk da a can din ma ba wani sakewa take sosai ba, bata kalli ko'in ba bayan gabanta hakan yasa bata kula da su waye a cikin falon ba, ciki kuwa har da Sirleem dake zaune can karshen falon gurin wasu set din cushion, ya baje documents da system a gabansa da alama wasu abubuwan yake dubawa, sai dai shi ya lura da ita idonsa na kanta har ta shige corridor da zai sadata da dakin Hajiya. Ita dai tana biye da Jurry har suka shiga dakin Hajiya. Tana shiga sau ta ji wani iri domin bata taba shiga bedroom din Ammy ba balle kuma Hajiya da take kamar bakuwa a gurinta. Daga jikin kofar ta tsaya ta risina kasa tana gaishe da Hajiya.
“Zo ga tufafi can ki jera min su a wardrobe can�
Hajiya ta fada ba tare da ta amsa gaisuwar da Falmata tai mata ba sannan ta mike tsaye ta fice daga dakin. Tana fitowa ta hadu da Nana ta doso dakin da alama shigowa za tai, da sauri Hajiya ta tare ta.
“Daughter zo muje wannan room din gyara ake min acan�
Nana bata ce komai ba ta bi bayanta suka second bedroom dinta, ta zauna saman kujera tana kallon Nana fuskarta da murmushi, Nana ta zauna kusa da ita tare da cire mask din fuskarta.
“Hajiya ba ki yi komai ba?�
“No na yi mana, i try my best, police din ne suka ce sai sun gama bincike�
Nana ta kalleta, a yau duk wata kima da kunya da nauyin Hajiya da take ji saita neme su ta rasa, abun da AA ya fada mata sai yawo yake mata a kwakwalwa, and yes he's right indai har Hajiya tana son ta zata yi murna da abun da yai ba wai ta juyar da case din ba, wanda har yanzu Nana bata san dalilinta na yin haka.
“Hajiya na ji kina waya jiya, ban san da wa kike waya ba, amman na ji abun da kika fada, kina son a juyar da case din Sardauna zuwa kisan kai, kuma kin ce zan yi abun da ya fi sata, kuma kin ce sai Ammy ta yi kuka�
Hajiya ta dafa Nana da sauri.
“Ke Nana ke ce kike fadin haka? Yaushe na fadi haka? Ni din? Ni Balkisu? Ko dai Ammy ce ta kitsa miki wannan abun?�
“Babu wnda ya kitsa min, kuma Wallahi idan aki fito da Sardauna ba, sai na fadawa Mai Martaba wannan maganar, kuma Wallahi ba zan auri Sirleem ba�
Nana ta fada kai tsaye tana hawaye, gaba daya Hajiya jin tai kamar babu duwawu a jikinta sai ta ji kamar tana kan ƙaya har sai da ta gyara zama sannan ta samu damar hade yawun daya cika mata baki.
“Nana ni Hajiya Bilki kike fadawa wannan maganar? Ni zaki shiryawa karya? Kin bata wayonki�
“Mai Martaba da kowa na gidan nan ya san ba zan miki karya ba, Wallahi Hajiya idan Sardauna be fito ba sai na fadawa Mai Martaba�
Ta karasa da kuka ta tashi da sauri ta fice daga dakin.
“Ni....�
Hajiya ta nuna kanta.
“Yaushe Nana ta lalace haka? Har ta iya labe? Ko dai wani ya ji?�
Ya mike tsaye wani irin gumi na keto mata ta ko'ina.
***
Falmata bata ji ba har sai da Jurry ta sake fada mata sannan ta tashi ta nufi gurin tulun tufafin da bata san ranar gama jerasu ba, saboda yawansu. Cikin natsuwa ta fara jera kayan da yawancinsu sabbi ne da ba a saka ba, sai kuma wandanda aka saka amman an goge su an shiryasu. Laces ta fara jerawa guri daya sannan ta shiga jera yadi, after like thirty minutes Jurry ta dawo dakin ta mika mata wasu yan kunne yara kanana masu kyau da kyalli.
“Karbi wannan na baki�
Falmata ta girgiza mata kai.
“Aa ki bar shi na gode�
A take Jurry ta hade mata fuska.
“Karbi mana, sai ki kulle a dankwalinki dan kar ya fadi�
Abun ka da mai tsoro sai ta karba gudun kar ta mata fada ta yi yadda ta umarce ta wato ta saka a dankwalin da kulle sannan ta maida dankwalin a kanta ta daura ta cigaba da abun da take, sai kusan 10am ta gama jera kayan, hannunta har yayi sanyi ga gajiyar tsayi da tai, komawa tai gefe ta tsaya tana jiran shigowar Jurry ko Hajiyar ko wane sannan ta fada musu ta gama. Cikin sa'a kuwa Jurry ta shigo dakin.
“Ranki ya dade na gama�
“Okay�
Jurry ta karasa cikin dakin ta bude drawer madubin Hajiya ta dauko wata sarka ta gold cikin gidanta ta mikawa Falmata.
“Gashi Hajiya tace a baki�
Ta fada da karya yadda Falmata zata ji, sai ta girgiza mata kai da sauri tai baya da hannayenta.
“Aa ba zan karba ba, fada za a min a gida�
“Oh Ammy ko? Zata ce waya ce ki karba? Ai ba sai kin bari ta gani ba, a boye zaki shiga da shi idan kin je gida sai ki aje abun ki, ba a maidawa Hajiya Kyauta�
Ta girgiza kai tana jin bata son karba duk kuwa da bata san muhimmancin sarkar ba balle ta san ta zinari ce ko azurfa ko kuma sarkar ce kawai ta fashion.
“Dan Allah karki saka ni na karba dole, Wallahi a zan iya saka ta ba�
“Ki karba na ce, you're very stupid ina cewa ki yi abu kina cewa aa yar talaka da ke useless girl�
Jurry ta fada a tsawace da sauri Falmata ta kai hannu ta karba ta saka a cikin Hijab.
“Na gode�
Ta juya da sauri ta fice daga dakin, tana tafe gabanta na faduwa, kamar wacce ta sato sarkar haka ta rika boyonta a cikin hijabin har ta fita daga bangaren Hajiya. Cikin fargaba da tsoro na rashin dalili ta shigo bangaren Ammy ta danna door bell din ba bata lokaci aka bude mata, ganin Ammy da Jekadiya a falon yasa gabanta faduwa saboda ta fita ba tare da ta fada musu ba.
“Ke daga ina kike?�
Jekadiya ta jefa mata tambaya tun kan ta karaso cikin falon, sai ta tsaya nesa da su ta risina kasa kamar yadda ta saba.
“Daga bangaren Hajiya, ta saka ni gyaran kayanta ne�
“Amman babu neman izini zaki tashi ki fita dan kin raina mutane? Wa kika tambaya da zaki tafi? Ko gyaran kaya kika zo yi nan? Tun da kike nan an taba saka ki wani aikin da ba na raino ba�
“Aa dan Allah ku yi hakuri ba zan sake ba�
“Wallahi kin kuru da Shattima be wuce ba, da sai kin karbi hukuncinki, ki bar masa yara kije gurin wani aikin dan rainin hankali�
Jekadiya ce take ta fadan Ammy dai tun da ta kalli Falmata sau daya ta dauke idonta bata sake kallonta ba, domin hankalinta da tunanin yana can gurin abun da Nana ta fada mata ta yi jiya, tun jiya da abun ya soketa be barta ba har yau sai dai bata iya labartawa kowa ba, saboda ba labari ne mai dadi ba. Tunanin abun da zai zame mata mafita take, wanda zuciyarta take raya mata aure ne kadai mafitar Nana, idan akai mata aure wata kila zata natsu kuma zata yi hankali, and controlling dinta zai koma karkashin kulawar mijinta ne, beside bata son karatu then zaman me zatai a gidan? Shigowar Jurry tare da wata hadimar ne yasa Ammy dawowa daga duniyar tunanin da ta tafi, bata ji karar door bell da aka danna ba har tashin da Jekadiya tai ta isa gurin kofar ta bude mata bata sani ba sai da ta iso cikin falon ta mika mata gaisuwa.
“Ammy barka da hutawa�
Ta fada daga tsayen da take fuska a hade.
“Sannu Juwairriya�
Jurry ta mikawa Falmata hannu.
“Ba ni sarkar da kika sata�
Falmata ta mike tsaye da sauri tana kallon Jurry, da mugun mamaki, ta ji abun da Jurry ta fada sarai domin a tsawace tai maganar.
“Ba ni sarkar da kika sata... Ke chajeta�
Jurry ta fada tana kallon hadimar da suke tare, Falmata kan mutuwar tsaye tai har hadimar da isa kusa da ita ta daga hijabinta ta karbi sarkar.
“Gata kuwa a jikinta.�
Hadimar ta fada tana mikawa Jurry sarkar.
“Ka ji yarinya daga shiga tai ma Hajiya gyara sarka na kan gado ta sace, ni na dauka daga daga cikin hadiman gidan nan ne shiyasa ma na kirata, ashe barauniya ce, ke ni ban ma yarda da ita ba chajeta a ko'ina�