← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 172

Sashe 83

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Ya fada min, abu na biyu kuma Sirleem ya fada min abubuwan da suka faru, maganar gaskiya ni bana bukatar yar aiki saboda aikin gidana ba wani aiki ne mai yawa na, kuma mijina yana Abuja gurin uwargidansa, saboda a can yake zama, ni kuma na zabi zama a nan saboda aikina da kuma yan'uwana, sai an dan kwana biyu ne yake zagayo ni ko kuma ni na tafi, sai dai hakan ba zai hana na daukeki aiki ba saboda halin rayuwar da kike ciki, and Sirleem ya roki idan ma bana son aikinki na barki ki rika wuni a nan idan lokacin zuwanki yai zai samo wanda zai rika kai ki gida, idan wata yai zai biya kudin aikinki, so from now on zamanki ya dawo a nan, zaki wuni a nan ko da baki yi aiki ba, abun da nake son ki da shi shine rikon amana da kuma tsabta�

“Inshallah zan kiyaye Hajiya�

“Ki kirani Momy, baki da wani suna bayan Falmata ne?�

“Mamana tana kirana da Fulani, amman dai sunana na kwarai Fatima�

“To zan rika kiranki da Fulani daga yau Inshallah�

“Na gode�

Falmata ta fada tana jin wani irin dadi a ranta.

_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:53 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

UNCLE AA POV.

“Hankalina ya tashi babu inda ban je nemanka ba tun jiya, saboda baka saba wuce 10 baka dawo gida ba, yau ma sai a wayarka yarinyar take fada min an kama ka, ni da su abokanka babu police station din da ba muje ba, ashe kana nan, Ahmad miye amfanin rashin jin magana?�

Anti Rabi da kira shi da sunansa kai tsaye tana kuka.

“Kaddara ce Wallahi, ban isa na wuce abun da Allah ya rubuta min ba, kuma abun da suke zargina da shi ban aikata na Wallahi Anti, dan Allah ki yarda da ni�

“Na goye ka a bayana, na san abun da zaka iya da wanda ba zaka iya ba, na san ka na san halinka, n yarda da kai Sardauna, amman da ace ka ji magana da haka be faru ba�

Shiru yai ya kasa cewa komai, daman can tashin hankalinta yake gudu, satar da aka laka masa ma ta kasance a haka ina ga ya labarta mata cewar za a juyar da case din zuwa kisan kai, ba zai iya labarta mata haka ba.

“Dan Allah kamin ka aikata abu ka rika tunawa da halin da zan shiga, zuciyata ba komai take dauka ba, kuma ba ni da walwala matukar baka cikinta, zan siyar da gidana na fara biya kudin sarkar, in ya so daga baya sai mu cika�

“Haba Anti wane irin gida kuma? Dan Allah karki yi haka, gidan nan fa gadon su Khaleel ne su su yi yaya?�

“Yayana ba su fi kanena muhimmanci ba, gidan ne kawai abun da nake da shi, kuma zan siyar na biya wani abu daga kudin sarkar, nawa ne kudin?�

“Ba fa cewa sukai a biya kudin Sarka ba, sarkar tana hannun mai ita, kawai dai sun aje ni nan ne saboda wata manufa da ban san ta micece ba, kar ki yi gagawar yin haka ki jira har sai mun ga abun da suke nufi tukuma�

“To, bari naje na samo maka wani abu ka ci, ji yadda duk suka buge maka fuska da jiki Uncle AA baka jin magana�

Ta fashe da kuka. Shi kanshi ya san ya ji jiki, domin ba a taba masa irin dukan da akai masa jiya ba. Fita tai daga gurin wanda hakan ya bawa abokansa damar shigowa suna gaisawa da shi, su kansu sun yi mamakin abun da aka zargeshi da shi domin sun san waye Sardauna, ba zai taba daukar abun wani ba. Har daya daga cikin abokinsa yake cewa ya ja hakkinsa.

“Kai wa zai iya ja da masu kudi? Wuya kawai zai sha Wallahi, Allah dai ya sar masa kawai�

Cewar abokinsa Abdul, AA dai be ce komai ba sai kunyarsu yake ji, duk da yana da tabbacin ba su yarda ya dauka ba, sai dan nauyin abun da aka zargeshi da shi. Anti bata dade ba ta dawo rike da takeaway irin wanda masu shinkafa a hanya suke zubawa masu tafiya da shi, sai kunun aya da ruwan sanyi.

“Gashi ka ci�

“Ba zai ci ba sai kin fara ci Hajiya�

Wani dan sanda ya fada, haka ta bude abincin ta ci kadan ta bude kunun ayar shi ma ta sha sannan ta mika masa.

“Na gode Anti da ba ni da ke da na shiga uku�

Ta furta yana jin wani irin son yar'uwarsa fiye da kima.

“Zan je na fadawa su Kawu, anjima zan dawo na kawo maka wani abincin, kai ta addu'a ka ji, Allah yai maka mafita�

“Amin Anti�

Sai da yai sallama da abokansa sannan ya sake yi mata sallama, abun ka da mace sai ta fashe da kuka, domin jin take kamar ta ja hannunsa su tafi gida amman babu hali ga kuma dukan da suka masa gwanin ban tausayi. Sai da ya gama cin abincin sannan aka bada umarnin maiyarda shi cikin cell din. After like one hour da maida shi aka sake kiran sunansa ya taso.

Police din daya fito da shi yana gaba, AA na baya har suka fito reception din.

“Ka yi free yarinyar ta yafe ma�

Police din dai handling case din ya fada yana rubuta a wani  littafi, kamin ya duba abubuwan da aka kama shi da su ya fara mika masa abun sa, zube agogon hannu tufafinsa biro sai kuma yan canjinsa da suke aljihu. Kamar almara haka AA ya rika ganin abun, da dai daya ya rika karbar komai nasa har ya saka tufafinsa ya saka komai nasa.

“To sai a kama hanya, gobe ma ka kara sata a bikin manya, Allah ne yai maka gidar dogo Wallahi ya takaita ma Wahala da sai ka gane shege ma da ne�

Shi dai be ce komai ba, ya nufi kofar fita yana jin wani iri, domin kalmar da police din ya jefeta da ita wato sata ta muzanta shi fiye da kima, sai da ya fito waje ya ji yana shakar iskar yanci, kamar wanda ya shekara a cell din haka yake jin kansa, sai a lokacin ne ya ji yana kyamar kansa, irin warin da cell din ke yi ga mutanen ciki kowa kalarsa daban, ya dan ja rigarsa ya shinshina kai kace da ita ya kwana a cell din.

“Wallahi Allah ya isa, Allah ya isa, daga police din har ita bakar Hajiyar da duk mai hannu a ciki har ma wanda ya jidadin an kama ni, Allah ka wulakantasu, Allah ya tsinewa arzikin Hajiyar albarka, kuma Wallahi sai ta gani tun da ta tana marayan Allah, bakar muguwar mata kawai, kuma na rantse Nana ba zata auri danta ba, kut�

Yayi kwafa yana huci kamar mai yi da wani, da hannu ya tare dan achaba ya fada masa unguwar da zai kai shi.

ZAINAB POV.

Tun da suka kamo hanyar zuwa cikin garin Katsina Zainab take hawaye har suka isa, yar rayuwar da su kai da Auwal cikin kankanen lokaci ne ta tsaya mata a rai. Zuciyarta ta kasa daukar rashin masoyinta, ta kasa aminta cewar Auwal ya tafi ya barta. Harabar gidan Hajiya Amutu suka faka motar ta bude purse dinta ta dauko 20k ta mika musu, da murna suka karba suna godiya, ita kam bata kula su ba domin hankalinta ba a nan yakr ba, su Hajiya ma da suke falo, tana amsa sannu da zuwan da suke mata ta wuce dakin da kayanta suke, gaba daya jin tai tana bukatar komawa Yola, kamar wanda aka cewa idan ta koma Auwal zai dawo, cikin gajiya da rashin kuzari ta rama sallah magariba sannan ta gabatar da isha'i, babu komai a addu'arta sai nemarwa masoyinta yafiya da rahamar Allah, tun tana yi tana jirewa har ta fashe da kuka.

“Ashe Allah be kaddaro mu yi rayuwa ba Auwal, ashe ganin da nai maka na karshe ne�
Chapter 83 · 0% Book details