← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 172

Sashe 123

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A take hankalin Baba ya tashi, tsoro ya kama shi kar dai ace siyar da yarsa yai, duk da kasancewar ba wani barin kudi Malam Mu'azu yai musu ba.

“Dole ne a sake bincike, ba mu san halinsa ba�

“Ni ma shi ma gani, kamata yai ace ta dawo gida ya zauna har sai komai ya daidaita tukuna�

Baba yayi mata wani wawan kallo da bata taba tsammani daga gare shi ba.

“Tumba? Ta dawo gida kuma? Yarinyar da aka akai jiya jiya sai ace ta dawo gida a yau saboda kawai muna zargi akan mijinta? Ina ce ke kika shige masa gaba wajen neman auren nan?�

“Malam ni Tumba kake fadawa haka?�

Ta nuna kanta da mugun mamaki.

“Am fada miki! Uwata ce ke? Kullum cikin tsagwamar yarinyar nan kike, bata tana jindadinki, yanzu kuma ta daga ta samu inda zata raba ta ji sanyi sai ki fara jefanta da mugayen kalamai da mummunan zato? Babu abun da ba ayi ma Fulani a cikin gidan nan ke ki mata kuma ki saka na mata, a haka take ta hakuri har abinci sai da na hana mata, haba haba haba abun nan ya isa haka ya isa haka...�

Ya fada idonta na cika tab da hawaye yana jin kamar ya fashe da kuka tunawa da abubuwan da yake yi ma yarsa ta cikinsa. Tumba kam mamaki ya hanata kara cewa komai, a yau Baba ya bata abun be taba ba, musa mata akan abun da ta fada har yana gada nata da watsa bayan a da ko kallonta yai sai ya ji tsoronta ya kama shi kamar uwarsa.

“Toooo haka yau abun ya zo min?�

Ta fada a ranta, kana ta dora.

“Ban ga ta zama ba�

Ta juya da sauri ta bar turken awakin ta nufi dakinta, sai da ta wuce sannan Baba ya saka hannun rigarsa ya share hawayensa. Tana shiga ta bude kwanon samirarta ta dauko kudinta ta saka a karamar jaka ta dauki hijabinta ta saka ta dauko talkaminta na fita ta saka ta fito tana kiran Naja.

“Na'am Umma ga ni�

“Naja karki kuskura bar min daki a bude, ki zauna a ciki ga bakin nan har na dawo, kuma kowa ya tambaya ki ce na tafi kai kudin na karbo gara�

Tumba ta fada tana jadadda mata, Naja ta amsa da to, sannan Tumba ta shiga cikin dangin mahaifiyar Falmata da dangin Baba ta fada musu cewar zata je ta kai kudin gara.

“Ba ance yace baya son komai ba?�

Inna Laure ta tambaya tana kallonta sai Umma tai dariyar yake.

“Allah yasa ga Laure, dan yace baya so sai a ki yi masa? Ai ba a haka, duk wannan Hidima da yai ai sai mu kuma mu bashi yar gara saboda rabawa baki, ba wai gara ta abincin ba, yar dibilar nan da cincin ai zai samu na ba abokai da yan'uwa, ita sai ta samu na ba kawayenta�

“Eh gaskiya haka ya kamata, kina da gaskiya kowa yana son kyautata wa�

Tumba ta ji dadin da Indo ta taya ta.

“Shine ai ko mutunci da girma ai sai mu fi yi a gurinsa�

Kowa ya goya mata baya, ban da Inna laure, ita ganin take idan ma ta yi ba dan Allah tai ba dan kunya ne da neman gindin zama. Da haka ta sa mu damar barin gidan cikin aminci ba tare da kowa yayi tunanin gurin wani mugun abun za ta je ba. Tana fitowa ta fara uban sauri kamar zata tashi sama, mamakin abun da Baba yai mata ta ci uban abun da ta gani a gidan Falmata, ance mai kidan kare ya ji kidan kura. Kamin ta iso titi duk ta matsu, ganin neman Napep zai bata mata lokaci yasa ta nemi achana ta hau, bayan ta fada masa inda zai sauke ta. Tsakanin unguwar da zata je da kuma unguwar da take tafiya ce mai nisan gaske, domin unguwa ce da take bayan gari, su kuma suna cikin gari ne.
Mai achaba na aikinsa hankalij Tumba yana can gurin abun da Baba yai mata, ko a mafarki ba tai tunanin Baba zai musa mata ba balle har ya furta mata haka ba, sai a yau ta yarda magani dan kwana arba'in ne domin a yau kam ta ga zahiri, kamar a mafarki ta ji an yi sama da ita an buga jikin wata motar, sai kuma ta ji wani abu ya fado mata kamar karfe.

“Wayyoooooooooooooooo�

Ta furta iyakar karfinta tana jinta a wata duniyar mai zugi da radadi tare da gusar da hankali.

SARDAUNA POV.

Washe garin ranar da Ammy ta masa magana ya fara hada takardunsa cikin murna da jindadi, ba shi kadai ba Anti Rabi ma ji tai kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, tsabar jindadi domin ta san abun da kanenta ya dade yana nema kenan cigaba da karatu, gashi a yanzu ya samu ba ma a Nigeria ba a waje.

“Anti ban fada miki ba, haduwata da yarinyar nan alheri ne gashi kin fara gani�

“Amman da farko ai wuya ka sha�

Yayi dariya yana kade takardunsa.

“To ai dadi baya zuwa cikin sauki, kuma wani lokacin sai anjarrabeka kamin a baka abun da kake bukata�

“Haka ne, kuma in da hakuri sai ka ga komai ya zo ya wuce kamar ba yi ba, na jidadi sosai da ta saka maka da wannan, amman tafiyarka ba zata min dadi ba domin zaka yi nisa da ni�

Ya karasa da muryar da ke nuna har a ranta abun ya taba ta, dan murmushi yai irin murmushin nan na rashin jidadi.

“Ni kaina ba zan jidadin tafiya na barki ba, amman Anti wannan ce kadai damar da ke da ita, idan nai karatu na samu result mai kyau, sai na samu aiki da zan iya daukar nauyin kaina da kuma na ki �

“Allah ya baka iko kuma a taimake ka, ita kuma Allah ya saka mata da alheri ya nisanta da dukan shari�

“Amin ya rabb, bari na tafi na kai mata takardun, wata kila ma idan ta gan ni ta tuna da zancen gidan da tace zata baki�

“Allah ya sa mu samu, aiko da mun gode, wannan sai a saka shi haya ana ajewa yara kudin saboda gaba�

“Zamu ma samu Anti tun da Nana ce tai maganar kuma ita da kanta Ammy sai da tace zata fadawa Mai Martaba, kin ga ko ta manta Nana zata iya tuna mata, ni Wallahi jin nake kamar yar'uwar mu ce, matar nan akwai kirki sosai, ni Wallahi har kunyar ta nake ji�

Anti Rabi ta yi dariya tana cigaba da tankaden garin dan wakenta, sai ya rufe jakar takardun ya maida daki ya dauki na sannunsa ya saka a wata jakar sannan ya kara fesa turare ya fito.

“Ban ce ka labartawa kowa ba, ka bar abun sai ya tabbata sai kawai mutane su ji zaka je�

“Anti ban da abun ki wa zan fadawa, ni kaina ai sai komai ya tabbata sannan jindadi zai kara tabbatuwa a gareni, Allah yai ya bude mana kofafin alheri�

Anti ta amsa da Ameen. Yana ma ta sallama ya fice cikin jindadi da zumudi.

_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Juyowa tai ta fito daga dakin tana share hawayenta, da sauri ta nufi kofar fita daga falon ta bude sai ta gashi tsaye jinkin kofar yana kallonta. Wani irin faduwa gabanta yai a lokacin da idonta ya sauka cikin na shi.

“Ina Fadime?�

Ya tambaya yana cire hular kansa wanda hakan ya bawa gashin kansa fitowa ya sarara.

“Bana son jin sunan yarinyar, ita ce silar wagaza farincikina, zuwanta ta zo min da bakaken abubuwa i hate her�

Ta fashe da kuka tana sakin kofar da zimmar faduwa kasa sai ta ji saukar hannayen Wasim a kafadarta. Mikar da ita yai tsaye ya ya girgiza mata kai, sannan ya matsa da shoulder sa ta dora kanta.

“Ba laifinta ba ne, laifinki ne ke da kika nemi kulla alaka da ita tun farko, da baki je garin ba da duk haka be faru ba, har halin da take kokarin shiga a yanzu da bata shiga ba�

Ta dago kanta hawaye na mata zuba.

“Kasan iya abubuwan da ta sanadiyarta na ji?�

“Na sani...�

Ya amsa mata calmy.

“Ba ni da komai a yanzu, ta bata min komai na rasa farincikina, ba ni da kowa sai uwar da bata da tausayi�

“Kina da ni...mu yan uwa ne kin tuna?�

Ta fada yana kallon cikin idonta holding her hand tight, fashewa tai da wani irin kuka wanda hakan ya bashi damar yi mata masauki a kirjinsa. Ya dora kansa saman nata nasa idon na cika da kwalla.

“Na san yadda kike ji, ina jin makamancin abun da kike ji, Baba ya fada min ba zai bar Fadime ta samu idonta ba har sai na yanke alakar da ke tsakamina da ita alaka ta har abada�

Dagowa tai ta kalleshi sai ta ga hawaye a idonsa.

“Hakan na nufin sai ka rabu da ita sannan zata samu lafiya�

Ya daga mata kai.
Chapter 123 · 0% Book details