Sashe 92
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka ta cigaba da yabon Allah tana fada masa damuwarta, daga karshe ta cika da fatiha ta rufe da salatin Annabi, sannan ta tashi ta koma ciki, tana kwantawa sai ta ji ta samu sa'ida da sakewar zuciya sabanin farkon daren da tunani da kuka ya ki barinta tai bachi. Bata farka ba sai da asuba, ta farka da nauyin zuciya na damuwa da kukan da ta sha kamin ta kwanta domin idonta har ya soma kumbura, sai dai ta nemi bacin ran ta rasa, tana jin bata son mutumem amman bata jin kunci da damuwa kamar na jiya abun ya mata sauki sosai.
Bayan ta gama sallah tai azkar dinta na safe data saba sannan ta dauko qur'ane ta karanta sai da rana ta fara dan bullowa sannan ta rufe qu'anen ta dauko maganinta ta saka a kunne ta saka kada, sannan ta maida ta aje ta fito harabar gidan tana gaishe da Tumba.
“Lafiya kalau�
Ba da wani karfi ta amsa mata ba, amman hakan be hana ta ji ba duk kuwa da kasancewar ta saka kada a kunne. Lumshe ido tai ta bude tana jin wani irin sanyi a ranta, sannan ta mike tsaye ta nufi inda Babanta yake zaune rike da redio asuwaki a bakinsa ta durkusa har kasa ta gaishe shi.
“Baba ina kwana?�
“Lafiya kalau, Tumba ta fada miki sako jiya ko?�
“Eh ta fada min�
“To yayi kyau bana son na sake ganinki da wani a waje, kuma bana son ki samu matsala da mutumen nan�
“To Baba�
Ta amsa sannan ya daga mata hannu ta mike tsaye ta juyo gurin iya tana kallon dumamen tuwon da take yankawa.
“Zan tafi gurin aiki�
“To Allah ya kiyaye, kin san dai Babanki ya hana a baki abinci da sai na zuba miki ko da sanyi ki ci�
“Aa a can nake karyawa ai�
Tumba ta juyo ta kalleta da kyau.
“To ki ce kayan dadi suke baki, shiyasa na ga kin yi kyau jiki sai fitowa yake, kwai kike ci ko?�
Falmata dai ta yi shiru sai kallon yatsun hannunta take.
“Wata dai ya kusa yau sauran kwana biyar kar a baki kudin nan ki taba su, dan na san halinki da keta�
“Ba zan taba ba Umma�
“To Allah ya tsare hanya�
“Ameen�
Ta amsa sannan ta sa kai ta fice daga cikin, fitar ke da wuya Naja ta dawo kusa da Tumba ta risina tana mata magana murya kasa kasa dan kar Baba ta ji.
“Umma da ni aka maida aikin nan, ji fa har zuwa daukarta, kuma Allah kadai ya san dadin da take sha a can�
“Wuyar da take sha dai, wani dadi zata sha? Ke baki masu kudin nan ba? Ai ko kallo bata ishesu ba, kuma rainon yara an fada miki sauki ne da shi? Ita ce kashinsu fitsarinsu da komai na su, kuma idan suka yi kuka ita zata dauke su tana basu hakuri ta ciyarda su, way sani ba ko har wanki take musu, kuma ke da kika karatu? So kike ki lalata karantun na ki ne?�
Cewar Tumba tana tubo baki gabana irin yadda magulmata suke yi idan za su yi magana.
“Gashi ma idan ta fita bata dawowa sai dare, ni ina zan iya wannan�
“To kin gani ki daina wahalar da kanki ma�
Sai da Naja ta saci kallon Baba sannan ta mike tsaye ta bar gurin.
     ***
A inda mai napep din jiya ya sauke ta ta tsaya, tana ta kwankwanto ko dai ya zo be same ta ba ne ya tafi? Ko kuma yana kan hanyar zuwa ne, domin tun jiya ya fada mata cewar ta rika jiransa a nan, saboda Napep da Mota basa shiga longunsu sai dai achaba. Sai dai tai jiran minti shirin sannan ya iso, daidai ita ya faka ta shiga tana masa ina kwana.
“Lafiya kalau, kin ta jirana ko? Wallahi na tsaya daukar wasu ne, na dauka baki shirya ba�
A nan ta ji abun da ya fada, duk d be daga murya sosai ba, sai ta ji wani irin dadi marar misaltuwa, sai dai tana jin maganar ne kamar daga wata duniya, kamar ana fisgo maganar da karfi aa jefowa kunnenta haka take ji. Sai dai ko kadan hakam be dameta ta san idan ta cigaba da amfani da maganin zata warke ta koma kamar da, daman lafiya raguwa ce da rarrafe take farawa.
“Ni ai tun bakwai nake tafiya�
“Kai kina kokari gaskiya, aikin me kike yi a gidan?�
Rasa tai abun da zata ce masa, Momy dai bata da yara balle tace raino take.
“Aikin gida haka, kuma ina tsare mata gidan saboda tana zuwa aiki�
“Okay. Allah ya taimaka ya sunanki ma?�
“Falmata�
“Falmata ai ba suna ba ne�
“Fateema�
“Ashe ke Mamana ce�
Ta yi dariya kamar yadda yai daga haka bata sake cewa komai ba, har ya isa bakin gate din gidan.
“To Mamana sai kuma na dawo daukarki ko?�
“To Allah ya tsare�
“Ameen�
Yaja Napep dinsa yayi gaba ita kuma ta kwankwasa kofar gate din mai gadin ya bude mata.
“Ina kwana?�
“Lafiya Kalau an iso�
“Eh�
“To madallah�
Ya bude mata gate din ta wuce ciki. Harabar gidan take ta kallo ciki har da wata bakuwar mota da bata taba ganinta a gidan ba. Kamar yadda ta ga Sirleem haka tai bayan ta danna door bell din kuma ta kwankwasa kofar, Momy ce da kanta ta bude mata kofar.
“Ahhh na dauka ma Sirleem ne shiya ko ya miki wannan knocking din ko?�
Ta yi murmushi sai Momy ta matsa mata ta shigo cikin falon.
“Bakowa kika yi�
Cewar Hajiya Umaima tana kallon Falmata.
“Eh to ba bakuwa bace, yata ce tana dan rage min aiki ne�
“Oh Allah sarki�
Cewar Hajiya Umaima tana murzawa yarta Nafiza allurar da akai mata.
“Ki shiga kitchen akwai dankali sai ki firaye, zan zo na dora girkin a gas saboda ki ga yadda ake�
“Tau�
Falmata ta amsa sannan ta mikawa Hajiya Umaima gaisuwa ta nufi kitchen din. Da kallo Hajiya Umaima ta bita har sai da ta shiga sannan ta kalli Momy ta ce.
“Ke kuma haka kawai zuciyarki ta raya miki ki samo mai aiki? Kina zaune kalau ta aure miki miji�
Momy ta yi dariya tana kokarin zama.
“Ah haba dai wannan yarinyar da kika gani bata da matsala Wallahi ko kadan, magana ma be dame ta ba, tana cikin halin rayuwa ne, ni ma ba son me aikin nake ba ai kin sani kawai dai dan na taimaka mata ne�
“Allah sarki, to ko dai dashen za a mata ne?�
Ta karasa tana mere baki, Momy ta kalleta da mamaki domin ta manta da ta taba mata maganar.
“Dashe kuma? Uhm Hajiya Umaima kenan, ni ai na watsar da wannan alamarin tuni�
“Aa fa Zaliha, ni ba abokiyar da za a boyewa sirri ba ce, kin san mun saba kashewa mu binne babu wanda yata taba ji, kuma na san kin taba min wannan maganar�
“Eh kuma daga baya na zafafa bincike sai nake ganin kamar be dace ba, malamai ma suna fadar yin hakan yana da illa gaskiya�
“Ke ba wata ila, idan kika biye malamai ai ko azumi sai wani yace be dece ki yi ba, ke a yadda kika cikin halin nan kuma kina bukatar haihuwa har dama ta same ki haka ki yi wasa? Haba dai Zaliha, kowa fa yana son haihuwa musamman ke da shekaru suka fara ja, sannan ga gorin yan'uwan miji, sai ki mutu shikenan ba ki da copy nunawa? Mijinki dai na san ba zan hana ba tun da shi ma yana son ki samu haihuwar, kuma ke fa likita ce kin san yadda zaki yi abun nan�
Momy ta nisa duniyar tunani tana sauraren kalaman da Hajiya Umaima take mata.
“Amman irin wannan abun yana da matsala Umaima, saboda yana bukatar sirri kuma yawan idan akai wasu za su yi amfani da damar ne su rika tasar kudi a hannunka ko su maka barazanar tona asiri�
Hajiya Umaima ta tabe baki.
“Ita wannan karamar yarinyar kike tunanin zata iya miki wannan? Kuma ai be zama lallai ki yi da saninta ba, dan ba kowa yake yarda ba, idan har kika da sanin mace shine zata yi amfani da damar tana cin duduniyarki, amman wacce akai wa cikin hikima zata nemi rabuwa da abun ne kawai, haba dai Zaliha, sai kace ba ke ba, duniya fa ta cigaba yanzu, ke fa kika fada a kullum baki cire rai da samun haihuwa ba, kuma duk wannan be saka kin yi tunanin mafita ce Allah ya kawo miki ba?�
Momy ta kalli agogon falon a kokarinta na kawar da zancen Umaima.
“Bari naje na hada abun karyawa yau da wuri zan shiga office�
Hajiya Umaima ta mike tsaye tana yar dariyar mamaki.
“To yayi Allah ya bada sa'a mu dai mun gode da ejection, sai kuma idan asman ta sake tashi, mu na gaida Yaya idan ya dawo�
“Zai ji inshallah�
Momy ta amsa tana kallonta har ta juya sai kuma ta juyo tana fadin.
“Wai Ameer ya koma ne?�
“Eh ya wuce jiya�
“Ah lallai kuwa, shi ne ko sallama? Ko da yake ba laifinshi ba ne laifinki ne ai�
“To ma zauna kullum ana ta dora muku dawainiya, abun kuma ai sai yayi yawa�
Cewar Momy tana murmushin da be kai zuci ba.
“Hmmm To Allah ya dawo da shi lafiya�
“Ameen�
Momy ta amsa tana binta da kallo har ta fice sannan Momy ta soma cire safar hannunta tana ta tunanin maganarta. Upstairs ta nufa tana sauke ajiyar zuciya, sai da ta shiga dakin ta jingina da kofar dakin ta rufe ido can kuma ta bude tana karewa dakin kallo kamar wani bakonta. Bed dinta ta nufa ta zauna still thinking, kamin ta shiga bandakin ta wanke hannunta ta fito daga bandaki kamar wanda bata son tafiya.