← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 172

Sashe 143

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Saboda yana sonki kuma so ba na wasa ba, duk namijin da zai yarda ya auri mace ba tare da sanin kowa na shi ba kuma auren fari ba dan komai ba sai dan ya taimake ta, to hakika wannan namijin ba karamin sonta yake ba, ko da makoci kike da shi ya damu da ke, za ki jidadi balle wanda ya zabi dauke ke kacokan daga wacan duniyar marar dadi a saka ki a wata rayuwar mai cike da daula da farinciki, kamin ke Sileem yana soyayyah da wata Mansura, amman be duba halin da zata shiga ba, shi ma be damu da duk irin abun da Hajiya da mu yan'uwan mahaifinsa za mu masa ba, ya runtse ido baya ganin kowa sai ke da damuwarki, duk da kasancewar ba ki yi boko ba, kuma ke ba yar wani mai arziki ba ce, Sirleem yana sonki sosai Falmata�

Falmata ta dago ta kalli Momy sai Momy ta kama hannunta ta rike.

“Na jidadin da ba ki auri Ameer ba, da yanzu dan'uwanki kika aura kenan? Kuma na jidadin da zuciya bata saka ni na aikata kuskure ba, da yanzu ban san da wane idon zan kalleki ba ke da dan'uwanki, Na miki alkawari Falmata Sirleem ba zai taba sakinki ba, ba zan bar shi ya sake jefaki a matsala ba, domin ba Hajiya kadai take da iko da shi ba, ni ma muna da iko da shi, kuma Allah be ce a bi uwaye a tsaba masa ba, ki kwantar da hankalinki kin ji?�

Falmata ta daga kai wasu hawayen masu kama da na farinciki da alhini na sauko mata. Momy ta tashi ta shiga kicin ta sake hada mata wani tea tana da godiya ga Allah da be saka ta aikata dashen da kawarta Umaima ta zugata tai ba, kenan da ta yi mata dashe da kwan mijin mahaifiyarta kuma mahaifin yayanta. Falmata ta saka hannu biyu ta karbi kofin tea, tana sha a hankali kalaman da Momy tai mata suna ta mata yawo a kwakwalwa, upstairs Momy ta nufa after like 30 min ta sauko rike da jakarta da makullin motarta.

“Zan tafi gurin aiki�

“Allah ya tsare Momy ya dawo da ke Lafiya�

“Ameen�

Momy ta amsa tana kallonsa sannan ta nufi kofar fita ta fice. Sai da ta ji tashin motar Momy sannan ta aje kofin tea da ta gagara shanyewa ta kwanta kan 3 seater din tana sauke numfashi a hankali, idonta sai ciwo suke. Tana kwance a gurin har aka sallah azahar, sannan ta tashi ta shiga dakin Ameer tai sallah, ta hau gadon ta kwanta tana ta kallon hoton mahaifiyarta, sai kusan uku da yan kintuna Momy ta dawo, sanin ta bar Falmata a gida yasa ta biya tai musu takeaway, da key dinta ta bude kofar falon ta shigo, sai da ta da ta shiga dakinta ta aje jakarta da kayan hannunta sannan ta dauko leda daya ta nufo dakin Ameer inda Falmata take, ta tura kofar dakin a hankali domin a tunanin ko Falmata tana bachi ne sai ta ganta farke tana kwance saman gadon idonta na kan hoton mahaifiyarta hawaye sai sauko mata. Momy ta karasa kusa da ita ta aje mata ledar.

“Tashi ki ci abinci na san ba ki ci komai ba ni ma kuma na dawo a gajiye shiyasa na yi mana takeaway be zama lallai na iya dafawa ba�

Falmata ta yi saurin boye fuskarta tana amsawa Momy.

“To na gode�

Momy ba ta ce mata komai ta nufi gurin da hoton yake ta juya shi, sannan ta fice dakin. Sai da ta fita sannan Falmata ta tashi ta share hawayenta ta sauko kasa ta bude abincin ta fara ci, turashi kawai take ba dan tana jin dadinsa ba, kamar yadda bata jin yunwa haka ma bata jin koshi, damuwar dake ranta ta saka ta ji bata bukatar komai, domin har a yanzu tana sauraren aiken Sirleem na takardar saki kamar yadda ya fada, a iya ganinta mawuyacin abu ne Hajiya ta barshi da aurenta.

Tana cikin dakin akai la'asar, ta shiga bandakin ta sake yin alwala ta fito ta gabatar da sallah, sannan ta daga hannayenta ta roki Allah ya zaba mata abun da ya fi zama alheri a rayuwarta, kuma ya saka komai ya zo mata da sauki kana ya sassauta mata abun da take ji a zuciyarta da kuma wanda take hangowa. Kamar wanda aka kulle haka ta sake zama cikin dakin har aka kira sallah magariba, sannan ta sake shiga bandakin tai alwala, kamin ta fito ta ji lokacin da aka turo kofar dakin aka shigo, sai dai a zatonta Momy ce ta shigo yin wani abu ko fada mata wani abu, hakan yasa tai hanzarin fitowa sai tai arba da Sirleem zaune gafen gadon yana kallon kofar bandakin, tsaye tai cak tana kallon fuskarsa da rama ta samu muhalli a gurin, zuciyarta na bugawa da mugun karfi. Sai ya mike tsaye ya miko mata hannunsa, kallon hannun tai sannan tai je gareshi da sauri ta saka masa nata hannun, sai ya rike gam ya jata zuwa jikinsa yai mata masauki da kirjinsa, kamkamshi tai hawaye na sauko mata, shi kuma ya daga kansa sama yana jin yadda hawaye suke bankwana da idonsa, ashe wani abun ya fi gaban kuka, duk wani abun da za ayi ma hawaye ko kuka mai sauki ne, domin a yanzu shi kasan be san inda hawayensa suke ba.

‘Na gode Allah da na aureki, na gode Allah da ban auri Nana ba, na gode Allah da ban sake ki ba, na gode Allah da gaskiya ta bayyana�

Ya fada a ransa yana tunanin abubuwan da mahaifiyarsa ta fada, taya zai iya labartawa wani cewar mahaifiyarsa ta so kashe mijin da take aure saboda abun duniya? Ta ya zai bar wani ya san kanwarsa ta jini da ita aka hada baki a kashe mahaifinta? Lallai Allah yayi gaskiya domin ya fada a cikin yayanku da matanyenku akwai makiyanku! I can't believe da sa hannun Hajiya a lalacewar Nana, me Shattima ya tare mata har take son a kashe shi? Why all this? Ashe daman akwai manufa a aurensa da Nana? A yanzu auren Falmata ya bayyanar da komai, duk kuwa da kasancewar ba dan auren ne kawai ya saka ta shiga hali ba, ya tabbatar har da alhaki na cutar da innocent people.

IYA POV.

Duk wanda ke gurin tsoron taba ta yayi, saboda tartsatsin wutar da jikin ke fitarwa, ga shi ta saka hannu sai tisgar naman jikinta take saboda zafin yankan da take jin mutanen da ta cinye ma kurwa suna mata ta ko'ina, tun tana yi abun na hankali har ta fara ihu tana fadin ayi mata rai.

“Dan Allah kui min rai! Jama'a wai ba ku ganin abun da nake gani? Ba ku ganin yadda suke yankana?�

Babu wanda yace mata uffan sai kallonta ake, ganin wasu sun fara fito da wayarsu suna daukarta yasa Baba Waziri ya rufe kofafin, ba dan komai ba sai dan mutuncin Mai Martaba.

“Wannan bala'in yayi min yawa, wadannan kaya ina za ninda su?�

Ta fada tana faduwa kasa sai tisgar naman jikinta take tana ihu, sai ta fara mulmula tana jin nauyin dazun yana dawo mata.

“Ku fita waje ku sama manyan sanduna�

Baba Waziri ya fadawa mazan da suke dakin sai uku daga cikinsu suka fita da sauri abun nema ya samu, ba su dade ba suka dawo, Baba Waziri ya ba su izini suka fara labtawa Iya iya karfinsu, wani irin uhu tai sai zabar ta zame mata hudu ga na mutanen da take gani ga yankan da suke mata ga kankarar maitar dake ta mata yawo a ciki tana sakar mata nauyi, ga kuma dukan da take ji ta ko'ina da bata san ta ina yake zo mata ba, dukanta suke duka bana wasa ba.

“Kar a asheta Waziri kar a kasheta�

Ammy ta fada tana hawaye.

“Ba kasheta za ayi ba, ubanta za a ci ta yadda idan akai mata magana za ta ji�

Shine amsar da Baba Waziri ya bawa Ammy, su kam matasan suka saka Iya gaba da duka har sai da suka fitar mata da jini a jiki. Wani abun mamaki ana dukanta tartsatsin wuta na tashi a jikinta, sai da suka kusan kasheta har ta kai bata iya motsi sannan Baba Waziri yace su dakata. Ya motsa kusa da ita ya kira sunanta sai ta kasa amsawa.

“Me zaki yi da kurwar Mai Martaba da kika kama?�

Muryar kawai take ji amman iyakar ganinta bata ganin komai da kowa sai mutanen da ta ci ciki har da mahaifiyarta. Baba Waziri ya sake maimaitawa amman ta gagara amsawa, har sai da ya maimaita sauko kusan hudu.

“Saboda... Na aurawa Shattima Zainab, sai na kashe sarkin sai Shattima ya gaji sarautar su haifa min jika�

Ammy ta dora hannu saman kai tana kalmar shahada, kowa na gurin sai da ya cika da tsananin mamaki, Baba Waziri ya girgiza kai.

“Azzaluma, ke da baki da gadonmu amman kin san ki yi kwadayin sarautar ku? Bayan duk hallacin da akai miki�

Ta motsa daker tana fadin.

“Suna ta yankana�

“Su waye?�

“Wadanda na cinyewa kurwa, ga su sun tsare ni suna ta yankana�

Ta shiga zana sunayensu a wahalce.

“Allah yasa su kashe ki, Azzaluma macuciya, macijiyar soshiya�

Baba Waziri ya fada cikin bakinciki da bacin rai.

“A ina kika rufe kurwar Mai Martaba?�

“Tana gida�

Ta fada kamar wanda ta kusa mutuwa muryar tai mata nisa.

“Tashi muje ki kwance ta�

“Ba kafa, kankarar maita ta min nauyi a ciki�
Chapter 143 · 0% Book details