← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 172

Sashe 96

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta amsa cike da mamaki, kamin ta maida hankalinta gurin Gate din da ake bugawa, mai gadin ya tashi da sauri ya nufi gate din ya bude karamar kofar ya leka.

“Malam Sannu dai�

Ya fada kamin yace.

“Eh tana nan wa za a ce mata?�

Ya saki gate din ya juyo gurin Zanab.

“Hajiya ana sallama da ke a waje�

“Waye?�

“Be fadi sunanshi ba, yace dai ace miki bako ne?�

“Bako? Ka san shi ne?�

“Aa yana tare da wata dai�

“Da mota yake?�

“Aa a kafa yake�

“Ce ya shigo�

Ta fada a zatonta irin mutanen nan masu neman taimako ko wani abu, Mai gadin ya nufi gate dan cika aikinsa.

“Bismillah Malam�

Mai gadin yaja baya yana bude musu karamar kofar gate din. Sai da Wasim ya fara shigowa sannan ya janyo hannun Fadime ta shigo. Daga kasa Zainab ta fara kallonsa kananan kaya ne a jikinsa wando da riga sai facing cap, tufafin sun karbe shi sidai ga shi fari sol cikin bakin tufafi, ba dan Fadime dake tare da shi ba da ba zata iya gane shi ba. Zaro ido tai cike da tsoro tai baya baya tana wani irin numfashi da karfi, ta da fa kirjinta.

SHATTIMA POV

Wani gurin ya nufa wayar na makkale a kunnensa.

“Ammy...�

“Na'am�

Ta amsa masa tana maida numfashi.

“Shattima na san kai mai yarda da kaddara ne, na san kai mutum ne mai karba duk abun da ya zo masa �

A take yaji gabansa yayi mummunar faduwa.

“Lafiya Ammy?�

“Kasan rayuwa aro ce Allah yake ba mu, ni kaina wata rana zaka wayi gari babu ni, ina son kai imani da wannan kaddarar�

“Wa na rasa Ammy?�

Ya fada yana rika karfen dake gabansa.

“Labib da Luma, aron da Allah ya baka ya karbi abunsa...�

Matsa hannunsa yai jikin karfen sosai kansa na mugun tsarawa, take idonsa y cika da kwalla.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un�

Shi ne abun da yai ta furtawa ta jingina da gurin ya dafe zuviyarsa, sai dai hakan be hana idonta cika da hawaye ba, wayar dake hannunsa ta subuce da fadi kasa sakamakon nauyin da yaji ta masa, gaba daya sai yaji jikinsa kamar ba nasa ba, muryar Ammy nata maimaita kanta a kunnensa.

“Doc Lafiya?�

Wani friend dinsa ya fada ya dauko wayar ya mika masa, sai Allah ya ba shi ikon bude ido ya sauke ajiyar zuciya tare da kai hannu ya karbi wayar ba tare da yace masa komai ba. Ya juya ya koma office dinsa, zaunawa yai saman kujerarsa sam ya manta da wani zancen Fadime, ya jingina da kujerar ya sake rufe ido yana kansa na mugun sarawa. Shigowar Inna da Bappa da kuma Sule ne yasa shi bude idonsa da su kai masa ja.

“Mun dawo an musu komai ranka ya dade�

Kai kawai Shattima ya iya daga masa, ya kalli Inna yana tunanin inda ya bar Fadime, a kujera right.

“Ba ku fita da yarinyar ba?�

“Aa nan na barta, ba kai kace mu barta ba muje mu dawo�

“Ni ma na barta nan na je amsa waya ko maybe ta fita, Dan Allah Sule a dubata waje�

Ya fada yana saka duka hannayensa ya murza each and every side of his head.

“Zata iya shi indai Fulani ce ai, bata jin magana�

Cewar Bappa yana bin bayan Sule, Inna kuma ta bi bayansu hankali tashe. Suna fita Shattima ya dauki wayarsa ya kira Ra'ees.

“A sama min ticket gobe zan je Yola, idan kuma za a samu yau lemme know pls, i lost my kids�

“Oh....... Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un�

Ra'ees ya amsa daga dayan bangaren, Shattima be tsaya saurarensa ba ya aje wayar ya sauke idonsa kan littafin Fadime dake saman teburin.

HAJIYA BABBA POV.

Kamar yadda ta fada kai tsaye ta wuce Kaduna su kuma suka sauka a Yola, yadda ta tararda yayarsa sai abun ya tayar mata da hankali, wata kila da bata yi ma mai martaba karya da ita ba da yanzu tana lafiya, domin bata sanin shigowar kowa balle fita hankalinta gaba daya ya face, kana ganin yayanta ka san hankalinsu a tashe yake. Ita ma kanta Hajiya hankalinta a tashe yake domin Hajiya Hansai ce kadai ta rage mata a cikin yan'uwa na kusa kuma wadanda suke jini daya, sai dai ganin hankalin yayan ya tashi musamman mata sai yasa dole ta danne nata tashin hankali ta rika basu magana tana nuna musu cewar zata tashi, duk kuwa da kasancewar ita ma kanta ta tsinke da rashin lafiyar, domin Alamu na nuna kamar bankwana take da duniya.
Kwananta biyu a asbitin ita take mata komai na jinya duk da kasancewar yayanta na kusa, domin Hajiya uwa ce a gurinta, kuma daman can tana kaunar jininta indai jininta ne wanda bata so bare ne.
Bayan ta gama sallah azahar tana zaune a harabar asibitin rike da carbe tana ja tana dan taba wayarta, kiran yarta Rima ya shigo wayarta.

“Hello�

“Hajiya�

“Na'am Karima ya gidan?�

“Ba lafiya, yanzu na ji ana cewa wai Luma da Labib sun rasu�

Hajiya ta dan tabe baki kamar abun be taba ta, kuma be bata mamaki ba.

“Da gaske kuma�

“Hajiya an karyar mutuwa ne? Wallahi da gaske ne�

“To Allah ya jikansu, sun lashe abun su kenan, mugun abu da bi su, daman ai ba albarka za su yi ba tun da suka saka mugun abu a gaba�

“Hajiya mutuwa ce? Haba ai kowa be wuce lokacin fa, ni Wallahi jikina duk yayi sanyi�

Wannan furucin da Rima tai yasa Hajiya ta tuna da Karima take waya ba Juwairiyya ba.

“Haka ne kuma Allah ya sa mu cika da imani�

“Ameen Hajiya yaushe zaki dawo?�

“To gani dai sai Hajiya ta ji sauki tukuna, Talba din ya dawo?�

“Aa ba ki yi waya da shi ba?�

“Taya ni zan kira shi shi be kira ni ba? Ina matsayin uwarsa daga tafiya n dawo ya taka jirgi ya bar gari zuwa wani birthday abokinsa a Abuja? Ai ko rikonsa nake na cancanta ya fada min, amman sai ya rika min abu kamar ni ce kasa da shi? Ya duba yayansa Shattima mana, shi haka yake? Haka ya ga yana yi ma Ammy, kullum ina fafuta akansa amman hankalinsa yana can wani guri�

“Hajiya yanzu fa duniya ta waye no need ace dan zaka je wanu guri sai ka fada, it's free world�

“Okay tau yayi kyau, ku cigaba�

Hajiya ta tsinke wayarta cike da bacin rai. Ta aje wayar tana kallon wani bangare na asibitin, cike da jindadin labarin mutuwar yayan Shattima, daman can tana bakin ciki da ba ta kanta Mai Martaba ya fara samun jikoki ba.

“Ai kadan kuke gani Wallahi, sannu sannu dai, duk wani mugun abun da kika shuka sai kin girbeshi, gashi nan kina komawa babu komai, ance bar ganin ka tara kiyayya mai nema�

Ta furta da murmushi a fuskarta, kamar wanda akaiwa albishir, sai ka rantse da Allah ba sakon mutuwa aka fada mata ba. Ya mika hannu ta dauko wayarta ta kira layin Hajiya Talatu.

“Hajiya yanzu nake shirin kiranki, sai gashi kin kira�

“Ince ke ma kin ji mutuwar?�

“Mutuwar wa kuma?�

“Yan jikokinmu, yau duk su buyin suka tafi�

“Ikon Allah? Kuma dai? Tau wannan abu wai ya yake ne?�

“Waya sani? Gamu dai gani ai da sannu sai mun cin ma nasara gashi Allah yana taimakonmu, shiyasa na ce miki ni maganar wannan bokan ba zata kayar min da gaba ba, bari dai Hajiya ta samu lafiya babu abun da za a fasa�

“Yo daman ai ba fasa zamu yi ba, ita dai wannan na dafa mata abun a nama na bata ta ci, ban san ni ko zai yi aiki oho, kuma an fada min akwai wata mai aljanu tana nan kusa da garin mola�

“Irinta ai sai dai a dauko mana ita, domin shiga irin wannan garin ai zaka ga wadanda suka sanka sosai�

“Eh nima ai haka na ce sai kin dawo zan saka a daukota, dan ce ita da madubi take aiki kuma zata fada maka komai, ko mutum kake so zata saka a dauko maka shi�

“Yauwa irinta na ke so, Allah dai ya ba Hajiyata lafiya na dawo Yola�

“Ameen, ya jikin nata yau duk ban kira ba�

“To jiki gashi nan sai hamdala, ba a cewa komai, ance ciwo ba mutuwa ba�

“Oh Allah ya bata lafiya�

“Ameen sai kin ji ni�

“To Hajiya Allah kara girma�

“Ameen�

Tana sauke wayar wani kiran na tsinkewa daga line Jurry, nan da nan ta kara kira. Hajiya ta yi picking tana murmushi a zatonta zata labarta mata ancen mutuwar yayan Shattima ne.

“Hajiya jirgin da Talba ya biyo ya fadi�

Kamar an cira Hajiya sama haka ta mike tsaye, dafe da kirji.

“Wane Talban?�

“Yaya Talba dai na mu, jigin ya kone gaba daya...�

“La'ilaha illallah, La'ilaha Illallah, La'ilaha Illallah�

Ta saki wayar ta dora hannayenta duka biyu a kai, gaba daya hankalin mutanen dake gurin sai ya dawo gurinta sai kallonta ake.

“Na shiga uku na lalace jama'a, dana Talba! Ta tabbata tafiyar da ba dawowa La'ilaha illallahu�

Yayan Hajiya Hansai sun nufo inda take da kukansu a zatonsu mutuwar mahaifiyarsu take yi ma kuka.

“Mun shiga uku Hajiya Mama ta tafi Mama ta tafi ta bar mu�

Macen ta fada tana kuka, Hajiya Babba ta juyo tana kallonta hawaye shabe shabe a fuskarta.

“Kuma dai...�

Ta furta kamin ta fadi rigigif a kasa....
Chapter 96 · 0% Book details