← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 172

Sashe 82

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yasan ba zata ce mishi komai ba, ya bude motar ya fita ba tare da jiran abun da zata fada ba, hannu ya mikawa Ameer suka gaisa sannan ya danna door bell din falon, after like 10 minutes Momy ta bude masa ya shiga ciki ya maido kofar ya rufe. Da hannu Ameer yai ma Falmata alama da ta zo, sai ta bude motar ta fito tana share hawayenta, gaba daya ta manta da wani mayafi bata mayafi take ba, ta tashin hankalin dake gabanta take yi, bata cikin kwanciyar hankali amman hakan be hanata tafiya a natse ba, be kawar da komai daga tarbiyarta da tsantsan da kai ba. Gaban entrance din ta tsaya kanta a kasa hawayen kuma sun ki daina mata zuba, ganin bata karaso ba yasa shi takowa ya sauko inda take ya tsaya.

“Me kike yi ma kuka?�

Ta kasa magana sai kokarin hade kukan take, duk da bata iya jin abun da ya fada ba.

“Me ke tsakaninki da Sirleem?�

Wannan kam ta ji domin ya kara matse tazarar dake tsakaninsa da ita kamin ya furta mata tambayar, ta girgiza masa kai alamar babu komai, sai dai bata furta masa komai ba.

“Zauna�

Ya fada yana nuna mata, sai dai kamin ta komai ya rigata kai wa kasa yai ma kansa mazauni a gurin. A hankali ta daga idonta ta kalleshi sannan ta zauna tana jin kamar an yanke mata kukanta.

“Miyasa kike kuka?�

Ya tambaya da rada, he just need to know because shi kanshi yana kallon Sirleem as bad guy saboda wasu celebrities sun batawa wasu suna.

“An kore a gurin aikina�

“Shi zai saka ki kuka?�

Ya tambaya da mamaki domin shi be ga abun kuka ba dan an koreta a gurin aikinta, ko bata fada b ya san na aikin office ba ne, domin ba tai kama da masu aikin office ba, ta ma yi kankanta da irin wannan aikin.

“Idan na koma gida Umma zata iya min duka Baba ma haka?�

“Mamanki?�

Ta girgiza kai.

“Mamana ta rasu, abokiyar zamanta dai�

“Oh. Sorry�

Ya furta yana jin wani iri, haka yake samun kansa a duk lokacin daya hadu da marar uwa mace ko namiji yana tausaya masu.

“Rashin uwa ba dadi, idan mutum ya rasa uwa ya rasa babban jigo�

Ya fada yana kallon harabar gidan alamar yana kokarin nisawa a duniyar tunani.

“Kai ma ta ka ta rasu?�

Unexpected Falmata tai masa tambayar, juyowa yai ya kalleta sai ya sakar mata murmushi.

“No i don't think so, i can't say a ina mahaifiyata take a yanzu, and i can't say me ya raba ni da ita, i just got lucky na samu Momy tana kula da ni sosai not like other step mothers, and i hope wata rana Mama na zata nemi ni, ban san abun da ya hana ta zuwa gareni ba, ni ma kuma ban san abun da ya hanani nemanta ba, a duk lokacin da nai unkurin haka sai na kasa amman ina fatar sake ganin fuskarta ko da sau daya ne a rayuwa, i need to meet my biological mother�

Ya sake kallon Falmata yana ta kokarin kirkirar wani murmushi ya yaba a fuskarsa, domin yana samun kansa cikin damuwa a duk lokacin da ya tuna da mahaifiyarsa.

“Ya sunanki ma?�

A maimakon tace masa Falmata ko Fulani sai ta zabi fada masa ainahin sunanta.

“Fateema�

“Nice name, ni kuma sunana Ameer ko ki ce black wato baki kamar ke, mun yi anko, ni baki ke baka hakan na nuna ba mu yi gadon farin ba kenan�

Ta yi murmushi kamar ba ita ce ta gama kuka a yanzu ba.

“Ni Babana fari ne, Mamana ce baka�

“Ni kam Mamana da Babana duka bakake ne, sai dai Mamana ta fi baki but tana da kyau sosai, sai dai a kamani Babana na dauko ban biyo Mama ba�

“Ni ma fuskar Baba na dauko, amman bakin na Mamana ne, har Umma tana cewa wai ba dan ina da kamanin Baba ba da sai ace ni ba yarsa bace, wai na cika baki kamar zunubi�

Ta fada da dan karamin murmushi fuskarta, ido ya kura mata hakan nan yake jin ta kwanta masa a rai sai ya ke jin kamar daman can ya santa ba, kamar yadda ita ma take jin sakewa da shi.

“Hakan ya nuna babanki yana da kyau�

Ta yi murmushi, shi ma murmushin yai ya mike tsaye yana duba agogonsa.

“Momy kar nai latti fa�

“Ina zaka je?�

Ta tambaya tana mikewa tsaye.

“Airport zata kai ni na bi jirgin Abuja, zan koma makaranta ne America�

“Wata kasa?�

“Yeah hutu ya kawo ni nan, amman na kusa gamawa na dawo gaba daya, ke ina kike karatu?�

“Ni bana makaranta ban taba zama aji ba�

“Da gaske?�

“Eeh�

Sai ya ji taba shi tausayi.

“Ina mayafinki?�

Sai a lokacin kunya ta lullube ta, domin ta manta da wani zancen mayafi har sai da yai magana.

“A can gidan na bar shi...�

Tana rufe baki Momy ta bude kofar falon ta fito Sirleem na bayanta sai dai shi yana rike da kofar falon ne. A nan wata sabuwar kunya ta sake lullube Falmata haka cikin dauriya ta risina ta gaishe da Momy.

“Momy ina kwana�

Momy ta amsa mata tana mata kallon tausayi.

“Lafiya Kalau ai wuni yayi 12 bata kusa ba?�

Falmata ta sunkuyar da kanta.

“Ki shiga ciki, zan aje Ameer airport na dawo, Sirleem ka sama mata Hijab ta saka�

Daga bakin kofar da Sirleem yake tsaye ya amsa da Okay, sai da Falmata ta kalli Ameer din sannan ta taka zuwa gaban kofar Sirleem ya bude mata ta shiga. A kasa ta zauna tana shi kuma ya wuce sama ya shiga dakin Ammy, be dade ba ya sauko rike da karamin veil kusa da ita ya zaune, sai dai shi a saman kujera yayinda da ita kuma take zaune a kasa.

“Saka wannan ban ga hijaban ba�

Ta mika hannunta biyu ta karba ta yafa, ya ciro wayarsa yana dannawa ba tare daya ya kalleta ba.

“Na fada ma Momy komai, and i hope zata dauke ki a aiki a nan, idan ma bata son aiki as i know bata son yar aiki zaki rika wuni a nan sai dare ki koma, idan lokacin biyan kudin aikin ki yayi zan baki sai ki bata, ina fatar hakan ya miki? Ba sai sun san an koreki ba balle su yi miki horo...�

Tun da ya fara maganar ta daga kai tana kallonsa sai idonta ya cika da hawayen farinciki, kura masa ido tai tana ta kallonsa wani irin kaunarsa ce take jin tana kirkirar muhallin a zuciyarta. Jin ta yi shiru bata ce komai ba yasa ya kalleta sai ya ga hawaye a sauko mata.

“Hakan be miki ba ne?�

Ta girgiza masa kai a hankali.

“Da ace zan iya, da na bude maka zuciyata kaga yadda kimarka ta cika ta, da ace kowa kamar kai yake da duniya ta zauna lafiya, kana da kirki fiye da tunanina, kana da kyautata ga masu bukata, baka kyamar kowa baka da girman kai, har yanzu na zuciyata ta kasa aminta cewar kai ne Sirleem M2, ina rokon Allah yai maka fiye da yadda kai min, ya zama gatanka, yai maka jagora ya shiga maka gaba akan dukan al'amurranka�

Yayi murmushi yana mata wani kallo mai wuyar fassara, kalamanta na ratsa jini da jiniyar jikinsa.

“Wata mace mai kalar shekarunki ko kasa dake, ko sama da ke bata taba fada min kalamai masu dadi kamar yadda kika fada min ba, ina jindadi idan na yayewa wani bakinciki, ina jin dadi idan nai taimako, amman ke... Ina ji kamar ace zan iya yaye miki damuwarki fiye da kowa, kina bani tausayi sosai, and yadda kaddara take ta hada mu maybe you need me the most, zuciyata ta cika da tausayinki, yadda kika da natsuwa, hankali, juriya, hakuri, sai kika burge ni, duk da kasancin shekarunki kin iya magana mai kyau Falmata, kin cika yadda ake so ko wace mace mijinki yayi dace...�

Ta yi kasa da kanta, bayan yabon da yai mata a mota na cewar tana da kyau yau ma ya kara yabonta da wasu hawaye da dabi'u da bata taba sanin tana da su ba.

“You know sometimes idan Allah zai taimake ka, na wai zai maka taimakon ba ne kai tsaye, sai ya kawo wani wanda ta dalilinsa zaka samu taimako ko kuma wani abu da kake nema, so ina daukar kamar haka ne a tsakanina da ke�

Bata sake dago kan ba, kuma bata sake ce masa komai ba har ya mike tsaye.

“Akwai inda zan je, ki zauna a nan har Momy ta dawo, ni zan wuce�

Ta daga masa kai b tare da ta dago ba, sai yai murmushi ya dauki keys dinsa ya nufi kofa, sai da ya kusa fita sannan ta juyo ta kalleshi, kamar yasa magana take son mishi sai ya juyo shi ma ya kalleta.

“Na gode�

Yayi mata murmushi kadan sannan ya bude kofar ya fita. Sai da ya fice sannan ta daga kanta tana karewa falon kallo, ciki har da katon hoton mijin Momy dake manne a falon.
Falmata na zaune falon har kusan awa daya sannan ta ji an sakawa kofar falon key ana kokarin budewa daga waje. Hankalinta ta tattara gaba daya ta maida gurim kofar har sai da aka bude kofar Momy ta shigo tana sauke gajiya.

“Oh na barki kina da jira ko? Wallahi jirgin ne be tashi da wuri ba�

“Sannu da zuwa�

Falmata ta fada, sai Momy ta zauna tana amsawa.

“Yauwa sannu dai, na barki ke kadai ko?�

“Ya tafi yace yana da aikin da zai yi�
Chapter 82 · 0% Book details