Sashe 14
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya fada ne kawai amman wani bangare na zuciyarsa na kara raya masa yadda zai sake samun wasu kudin haduwarsu ta gaba, tun da ta karbi lambarsa yake jiran kiranta.
“Wallahi Allah ne ya ji tausayi na ya kawo min yarinyar nan, Allah kadai ya san me babanta ke yi�
Ya fada a ranshi yana aikin saka talkaminsa, sai da yai ma Anti sallama sannan ya fice daga gidan, kamin ya isa gurin aikin nasa har addu'a yake Allah yasa yau ma ta zo, ya kuwa taki sa'a domin ya tarrarda ita zaune a gurin tana ta boye fuskarta kamar yadda ta saba, wannan karon be tsaya komai ba ya nufi inda take, Nana na ganinshi ta fara dariya.
“Tun dazun na zo�
“Muje waje mu yi magana�
Ya fada yana kallon daidaikun mutanen da ke wajen, domin safiya ce ba kamar da rana ba ko dare da ake taruwa sosai a restaurant din. Mikewa tai tsaye ta riga shi fita sannan ya fito ya same ta tsaye a inda ta tsaya jiya.
“Kin samo min aikin driver?�
Ta bata fuska kamar za ta yi kuka.
“A a ta hana�
“Daman karya kike yi�
“Da gaske ne mana�
Shiru ne ya biyo baya na tsawon lokaci, sannan ya sake kallonta ya ce.
“Yau ma kina son na kai ki wani guri ki boya?�
Da sauri ta daga kai.
“Eh Eh�
“To kawo kudi na karbo babur din, amman yau ya ce sai an bashi 4k�
Bata tsaya komai ba ta bude jakar ta dauko kudin ta mika masa.
“Na je can waje na jira ka kamar jiya?�
“Eh�
Ta nufi hanyar fita shi kuma ya koma ciki gurin abokinsa Bashi, ba laifi yau ya manna masa 500 sannan ya karbi key babur din ya fito ya kunna ya hau ya fito da shi waje, yana isowa bata tsaya komai ba ta hau ya boye fuskarta, sai da ya su kai nisa sannan ya fara tunanin inda zai kai ta, ya san zai ba zai sake kaita gidan Anti Rabi ba, bayan dazun da safen nan ma sai da tai masa gargadi, to ina zan kaita? Ko ya kaita gidan Gwaggonshi? Ko gidan Kawu Bala? Kuma idan na kaita suka gano abunda cewar boyeta na yi za su min fada? Sai tambayar kansa yake yana neman mafita, be an karo ba yaji kamar an bugu babur din da suke kai yana kokarin saita babur din suka fadi kasa daga shi har ita, babur din ya haye shi ita kuma ta mulmula ta fada kwalbati.
Kamar ita ta fi kowa ihu a duniya haka ta kwala ihu ta fashe kuka na gaske tana duba hannunta da yaji rauni da kafarta, daman can ko allura aka ce za a mata sai anyi da gaske take tsayawa balle kuma wannan da ta gurje a hannu da kafa da gefen fuska.
“Wayyo Allah Wallahi sai na fadawa kowa, sai an kashe ka yau Wallahi kai ne ka ji min rauni kai ne ka fadar da ni da babur, sai na fadawa kowa yau sai an kashe ka�
Cikin wani irin kuka da tsoro take fadar hakan tana kallon jikinta, AA na jin haka ya manta da nasa ciwon ya taso ya nufo ta ya daga ta, mutane sai sannu suke musu, ganin yana jan kafar wani yace
“Zaka iya jan babur din kuwa�
“Eh zan iya ku taimaka ku dora min ita dan Allah�
Sai da ya hau sannan suka dora masa Nana dake ta ihu tana fadin sai ta fada a gidansu. A hankali ya fara tafiya gabansa na mugun bugawa kamar zai fito, sai da ya samu wani mai chemist sannan ya faka babur dinsa a gurin ya sauko ya rikota ta sauko ya shiga da ita cikin chemist din, zaunar da ita yai sannan ya ce.
“Bari na gyara fakin din babur di na�
Bata ko kula shi ba tana ta kuka da duba kafarta domin har a cinya ta ji ciwo. AA na isa ya haye babur din ya auna a guje be be nufi ko'ina ba sai unguwarsu, kamin ya isa har wani zazzabi ya rufe shi babu muryar da yake ji sai ta Nana tana fadin sai ta fadawa yan gidansu yau ko sai an kashe shi, laifi goma da ashiri, ga boyon da yake mata ga na fadar da ita akan babur dinsa dan ya san yarinyar yar masu abu ce wata kila ma ita kadai iyayenta suka haifa ya san kuma ba za su kyale ba.
Kamar wani mahaukaci haka ya shigo gida hannunsa na ta jini sai dingishi yake. Anti na ganinshi gabanta ya fadi.
“Lafiya AA�
Kasa ce mata komai yai ya zauna bakin kofar dakinta ya dafe kanshi.
“Lafiya hadari kai?�
“Eh yarinyar ce ta roki na kawo ta nan shine na sake aro babur, muna tahowa sai wani mai Napep ya kade ni muka fadi ta ji ciwo ni ma na ji�
Anti Rabi ta daki kirji.
“Me? La'ilaha illallahu Muhammadu Rasulullah Sallalahu Alaihi Wassalam�
AA ya kalleta a tsora ce ya soma magana gumi na karyo masa.
“Kuma Wallahi na ji tana cewa sai ta fadawa duk yan gidansu, wai yau sai an kashe ni tun da na fadar da ita akan babur�
A take cikin Anti Rabi ya murda, ta dora hannu aka ta fashe da kuka.
“Ka gani ko? Sai da na gargade ka amman baka ji ba, Allah kadai ya san waye ubanta mun shiga uku, ina yarinyar take?�
“Na barta a can wani chemist na gudo�
“Kai Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, mun shiga shida�
Ta fada tana nufar butar da ke tsakar gida ta dauka ta nufi bandaki. Mikewa tsaye AA yai ya fice daga gidan, chemist din unguwarsu ya nufa yana isa be ko tsaya gaisawa da abokin nasa ba ya ce.
“Dan Allah Ilya kai min treatment din ciwon nan kuma ka min allurar malaria, ina jin zazzabin malaria na ta so min�
_________________
Waye zai zo ya cece AA 🤣😂
Me iya take kullawa? 🤔
Anya dai Hajiya Karama mace ta tana neman miji da kanta kamar yadda kike?😥
Wai me Falmata ta tarewa Tumba ne?ðŸ˜ðŸ¤§
03/12/2021, 08:07 - ðŸ¤ðŸ¤ðŸ¤ðŸ¤: *ðŸ„🄠FULANI ðŸ„ðŸ„*
By Khadeeja Candy
*6*
HAJIYA BABBA POV.
“Jarma har yanzu ban ga komai ba�
Ta fada tana karewa Jarma dake zaune a gabanta sanye da babbar riga, kansa kuma da rawani.
“Kina gaggawa ne kawai Hajiya, ba gashi mun fara ganin haske ba? Komai a sannu ake binsa�
Ya dauke kai tana kallon wani bangare na dakin.
“Ba Mai Martaba nake magana ba, Shattima shine matsalata a yanzu�
“Da Shattiman za mu fara kamin Mai Martaba ya biyo shi, idan mu ka yi gaggawa to kamar muna fallasa sirrinmu ne, ya kamata mu bi komai a sannu�
“A sannu na ke bin komai Jarma, domin burina dole ne ya tabbata, Talba kadai na ke son ya yi mulkin garin nan, so na ke na ga Ammy na zubar da hawayen bakinciki, shekarun da ta saka na yi a damuwa so na ke ta ninka a cikin bakinciki, na san a yanzu tana farinciki da ciwon Mai Martaba saboda tana ganin Shattima ne zai gaje shi ko? Hmmmm�
Ta karasa tana murmushin gefen baki. Jarma ma murmushin yake yana kallonta zuciyarsa na saka masa burinsa.
‘Za mu kawar da Shattima da Mai Martaba, amman dan ki ba zai yi milkim garin nan ba, indai ina raye�
A zahiri kuma sai ya gyara babbar rigarsa ya ce.
“Da sannu komai zai wuce Hajiya, kuma kar Salim ya fasa neman Nana�
Sai a lokacin Hajiya ta dawo da kallonta a gurinsa.
“Ai dole ya neme ta, tun da har Mai Martaba ya sallama masa babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu, dole ne Ammy da zuri'ar ta su dawo karkashin kulawata, duk abun da tai min a shekarun baya sai na maimaita mata shi�
Ta karasa zancen fuskarta na sauyawa alamar bata son tuna bayan.
“Komai zai wuce Hajiya komai zai zama tarihi da yardar Allah�
Ya daga masa kai tana sauke wani dogon numfashi.
“Haka ne, tashi ka je kar a fara yi mana zargi�
“Zargi kuma na nawa? Sai dai kar a koma�
Ya fada yana mikewa tsaye da murmushi a fuskarsa, sannan ya dan risina mata.
“Na bar ki lafiya�
Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta mike tsaye ta nufi gaban drawer ta dauki wayarta ta aikawa Hajiya Talatu kira bugu daya ta daga tana jerowa Hajiya Balki wani irin kirari da ke kasa kan Hajiya fashewa.
“An gaishe da Talatu Uwargidan Waziri�
Talatu ta risina kamar Hajiyar ce a gabanta.
“Allah ya kara miki lafiya da imani, Surukar Ammy kuma Uwar Sarkin gobe, a ganki a bar ki kuma a bi ki a dole�
Hajiya Bilki ta yi wani irin kasaitaccen murmushi.
“Yanzu Jarma ya fita daga nan�
“Tsohon makiri, Allah yasa dai ba ki masa zan ce na ba, domin tsab zai labartawa Waziri komai ya kashe mim aure a asirance�
“Taya za ayi na bar shi ya san shirin mu Talatu? Bayan na san shi akwai kwadayin masarautar nan a ransa? Ubansa daya fa da Mai Martaba kuma babu yadda be yi ba Mai Taba ya bashi Babbar masauta ya ki, yanzu kuma kike tunanin baya sha'awar wannan?�
Hajiya ta dan yi jimm tana murmushi mai sauti
“Mu dai gama da bangaren sauran ne sannan mu dawo kansa, na kira ki na ji yadda ake ciki�
“Zan shigo da kaina ranki ya dade, domin maganar ba ta waya ba ce�
“Ina jiranki�
“To ranki ya dade�
Daga haka ta aje wayar ta juya ta fice daga dakin, kofar dakin bata kara idam an bude ko an rufe gashi akwai yar tazara sosai tsakanin dakunan da inda aka jera kujerun falon, hakan ne yasa Sirleem be ji motsin mahaifiyar tasa take tsaye a bayansa tana kallon Mansura wace ke a fuskar Laptop dinsa yana video chat da ita ba. Har sai da ya ga Mansurar ta kasa karasa maganar da take tana kallon gafensa, sannan ya juya sai yai arba da mahaifiyarsa. Da sauri na rufe laptop din.
“Hajiya Barka da fitowa�
“Ban maka iyaka da yarinyar nan ba?�