← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 172

Sashe 127

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammy bata sake ce masa komai ba bayan kallonsa da take, shi kuma ya juya ya fice daga dakin, kamar yadda ya fada da kansa ya isa bangaren da akai wa su Bappa masauki, tun kan ya isa hadiman gidan kd faduwa kasa suna kwasar gaisuwa sai dai be kula ba har ya isa. Wani hadimin ya saka ya sallamo masa Bappa da kawu suka fito, su ma masa suka fadi suna kwasar gaisuwa kwarjinin Shattima ya cika musu ido sosai. Hannu ya daga musu alamar su tashi tsaye ko wannensu ya ki suka maida kai kasa ko kallon inda Shattima yake basa iya yi.

“Am... Daman tafiyar da na ce za ku yi gobe...�

Sai kuma yai shiru kamar mai nazari ko fargabar abun da zai fada.

“Ina tunanin za a daga ta har zuwa wani lokaci.. Saboda Fateema mun nemeta a cikin gidan ba mu ganta ba sai dai a gama bincike ba...�

Wani irin abu ne ya soki kahon zuciyar Bappa, sai ya ji abun kamar almara, ya san ko a kamanni da sura Shattima ba zai iya shimfida muau irin wannan karyar ba dan kawai ya fadar musu da gaba ko ya tsorata su ba, balle kuma ga sarautar da ta isar ta sanar da ko wane talakawa cewar dan sarauta da sarki basa karya musamman wandanda suke jigo a sarautar, sai dai abun da Bappa be fahimta ba shi ne cewar Fadime ta bata, ta bata ta fita zuwa wani guri ko kuma ta bi wani ko sace ta akai? Ko kuma Shattima ne ya canja shawarar tafiyar? Lokaci daya Bappa ya jero ma kansa wadannan tambayoyin da ba shi da amsar su, gashi kuma yana jin be isa ya daga ido ya kalli Shattima ba balle har ya sake yi masa wata tambayar.

“Ku kwantar da hankalinku za a ganta Inshallah�

“To to ranka ya dade mun gode�

Kawu ya fada, Bappa kam be iya cewa komai ba har Shattima ya bar gurin Bappa be iya tashi daga duken da yake ba, gaba daya sai ya ji kamar ba shi da lakka, dan kuzarin da zai saka ya mike tsaye sai ya neme shi ya rasa.

“Ka gani ba, wannan Fadime ban san wani irin hali take son saka mu ba, yanzu kuma wa ta bi ga gudu? Ko kuma shi din ya sake sace ta? Ni Wallahi da Shi Mai Martaba zai yarda da ya bar mu mun tafi gida gurin harkokinmu�

Cewar Kawu dan Iroro cikin fusata da bacin rai. Bappa ya numfasa ya yunkura daker yana ambaton Allah tare da kokarin mikewa tsaye, sai ya ji kirjinsa ya rike kamar an soka masa mashi. Komawa yai ya duka yana jin wani irin zafi a kirjinsa da be taba ziyartarsa ba, duk abubuwan da Fadime take be taba bata masa rai matuka irin wannan ba, gashi sanin gaskiyarta sai Allah, zuciyarsa na ta raya masa cewar saboda yace ba zata auri Wasim din ba me yasa ta gudu ko kuma ta hada baki da shi Wasim ya sake dauketa.

“Wallahi yarinyar nan tana jefa mu cikin matsala, da na san abun da zai faru kenan da ban zo garin nan ba, yanzu wani garin zata sake jefa mu kenan�

“Daga nan ba za mu sake zuwa ko'ina neman Fulani ba, na san ita kadai ta rage min, amman na yafe ta kawu, idan ta dawo zan karbe ta idan kuma bata dawo ba ba zan sake nemanta ba, wani nawa kuma ba zai neme ta ba, Allah ya ba mu dangana�

Bappa ya fada cikin wani irin bakinciki marar misaltuwa, numfashinsa har wani taushewa yake saboda nauyin da zuciyarsa tai, sake yunkurawa tai ya mike tsaye sai ya kasa, gaba daya abubuwan da Fadime take masa na bacin rai sai suka taru suka masa tsaye lokaci daya. Kawu ya dafa shi.

“Lafiya dai?�

“Kawo ka fita ka samu wanda zai yi magana da shi Mai Martaban a fada masa muna son mu kama hanyar tafiya gobe Inshallahu�

“Idan mu ka yi haka ai sai yace ba mu ji maganarsa ba, mu dai hakuri mu ga abun da Allah zai yi�

“Ba zan fasa tafiya saboda Fulani ba, komai take so taje tai, kuma komai take ganin yinsa daidai a rayuwarta na bata dama�

A karo na uku Bappa ya sake yunkura sai yai nasarar mikewa tsaye, sai dai ko kadan zuciyarsa bata barshi ya samu sukunin yin numfashin kamar yadda ya saba ba. Hanyar da ya ga Shattima ya bi ya fara bi yana jin kamar baya iya cira kafarsa sosai, Kawu yayi saurin rikosa.

“Aa Jauro, karka ce zaka musa masa akan maganarsa, mu hakura kawai har sai yadda hali yai�

Bappa ya saka hannunsa ya cire hannun Kawu dake rike da rigarsa.

“Aa Kawu ka bar ni magana kawai zan yi da shi, idan be yarda ba sai mu hakura�

Kawu ya ja da baya yana jin mugun tsoro kamar shi ne zai tunkari Shattima da maganar. Bappa kuma ya cigaba da tafiya ba dan yana da tabbacin zai gadu da Shattima ba kuma ba dan yana da tabbacin zai hadu da wanda zai sadashi da Shattima ba. Duk wani tsoro da fargabar tunkarar masu sarauta da yake sai ya cire shi ya aje gefe saboda ransa yayi mugun baci, duk karfin halinsa da dakiyar zuciya irin nasa sak da hawaye suka cika masa ido. Kamin ya fito harabar da suke har jin yake kamar baya iya numfashi, babu abunda yake tunanin sai abubuwan da Fadime take tun tana karama har girmanta har kawowa yau da ya kamata ace ta yi hankali ta natsu, domin zuciyarsa ta fi raya masa cewar da saninta komai ya faru, idan ma bata sanin ba ai duk laifinta ne da ace tana jin magana tun farko da yanzu komai be faru ba. Can kusa da Bangaren Ammy Bappa ya hango Shattima tsaye ya maida hannayensa baya, tare da wasu mutane hudu sun zube a gabansa, a kokarin Bappa na cira kafa ta isa gurin da Shattima yake tsaye sai ya ji shi a kasa, daman tafiyar kawai yake yana jin kamar kafafuwansa basa iya daukarsa. Faduwar da yai ne ya saka mutanen da suke gaban Shattima juyawa su kalli inda yake ban da Shattma da kasaita ta hana shi, sai dai kana kallonsa ka san ransa a bace yake. Bappa ya tattara dukan karfinsa da kuzarinsa ya yunkura ta tashi ta isa gaban Shattima sai dai ya tsaya nesa da shi ya zube kasa. Shattima na ganin haka ya dagawa mutanen da suke gabansa hannu sai suka tashi da sauri suka bar gurin suna masa godiya. Takawa Shattima yai ya isa gaban Bappa da ya daga masa hannu alamar girmamawa.

“Tashi mana Baba�

“Aa ba zan tashi ba, alfarma dai na zo nema idan zaka amince mana�

“Ina jinka�

Shattima ya fada yana gyara tsayuwarsa wanda hakan ya ba wa talkamin sarautar da suke kafarsa motsawa.

“Dan Allah ranka ya dade kai mana alfarmar tafiya gobe, saboda akwai abubuwan yi a gaban mu, musamman ma Kawu, ni kaina na baro mahaifitarta da sana'a a can hankali ba kwance ba�

Fahimta daya Shattima yai ma maganar Bappa wanda kuma ita ce gaskiya, yanayin fuskarsa da yanayin yadda ya ke furta kalaman cikin dannewar numfashi kadai ya isa ya saka Shattima fahimtar cewa Bappa fushi yai kuma ransa ya bace a kan hakan.

“Idan kuna ra'ayin zuwa ba zan hana ku ba, kuma ba zan ga laifin ku ba, idan kuma kuka tsaya zan yi maraba ku na san cewa ka damu da yarka�

“Ranka ya dade, ban so musa maka ba kuma ban isa na ki bin umarninka ba, amman tabbas yarinyar ta wuce inda kake tunani�

Shattima ya dauke kai yana jin dacin maganar Bappa akan Fadime, ko kadan baya son ya ji a fadi laifinta musamman a yanzu da be an halin da take ciki ba.

“Shikenan za'a sanar da direba sai ku shirya da wuri�

“Allah yasa dai ban bata maka rai ba, a gafarce ni idan na bata maka rai dan Allah, tuba na ke tuba na ke�

Bappa ya fada, Shattima dai be ce komai ba sai dai shirun da yai ya isa ya karantar da Bappa cewar ransa ya bace. Bappa ya mike tsaye yana cire talkaminsa ya juya ya baro gurin yana jin wani irin ciwon kirji da be taba jin irinsa ba, numfashim ma idan ya fita sai yayi da gaske sannan yake dawo masa. Shattima ya bishi da kallo yana mamaki wane uba ne irin wannan da za a cewa yarsa ta bata har ya zabi tafiya ya barta ba tare da ya tsaya bincikar inda take ba.
Yana tsaye gurin motar su Jekadiya ta iso, tun da suka hangoshi tsaye yasa suka kashe fitilar motar gudun kar su haska shi, nesa da shi suka aje motar suka fito Jekadiya na gaba suna binta a baya har suka iso gaban Shattima, ta risina kasa tana fada masa cewar sun bincika ko'ina ba su ga yarinyar ba.

“Amman Hajiya Karama ta ce a sanar maka, wai wani Wasim ya ce a fada maka kar a taba idonta kuma wai akwai masu son cutar da ita komai ya fara kar a ace za a bata magani ko ayi mata wani abu�

Shattima ya kurawa Jekadiya ido yana mata kallon fahimta.

“Waya fada miki wannan?�

“Hajiya Karama�

“Je ku ta ho min da ita�

Ya fada kai tsaye sai ta mike da sauri tana fadin.

“An gama ranka ya dade�
Chapter 127 · 0% Book details