← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 172

Sashe 152

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ya daga mata kai tana jin kamar ya hana ta zuwa, da farko be yi niyar rakata airport ba sai dai ganin yadda take kuka yasa ya rakata airport din, da katuwar jakar kayan da ya saka ka siya mata masu tsada. Motarsa dabam ya shiga ita kuma ta shiga motar su Baba Waziri da mutanen biyu da suke tare da shi, suna isa airport ko minti talatin ba su ba jirginsu ya daga zuwa Katsina. Kusan duk wanda be saba shiga Jirgi ba zaka tarar yana jin tsoro a shigarsa ta farko da ta biyu har zuwa lokacin da zai saba, amman ban da Fadime ko wa can zuwan da su kai da Mama Fulani bata wani tsorata ba, kawai saboda tana cikin damuwa ne yasa bata maida hankali sosai a kai tafiyar ba, yanzu kan har dadi take ji a zaunar da ita kusa da window jirgin tana hangen waje, ta soma daukar hoto da wayarta har mutanen da ke cikin jirgin dauka take. Suna sauka Katsina zuciyarta ta fara kewar Shattima ta dayan bangaren kuma tana mata zillon na son ganin Bappa da Innarta. Ko da suka sauka airport din Motocin Mai Martaba na harabar da ake aje mota suna jiransu, a Front seat ta zauna mutumen da ke tare da Baba Waziri ya shiga gidan baya, cikin motar ma tana ta daukar reban da kanta. Masarautar Katsina suka sauka akai musu tarba ta ta musamman, sai da suka ci suka sha wannan aka hada su da wata tawagar da zata yi musu rakiya har garin Bandalo. Kamin a isa garin Fadime har ta ayyana yadda zata rika kallon kowa, domin tana jin kamar ta fi kowa dace saboda ta je Masarautar Garuk, da ta Yola haka ma Katsina. Tun daga shigowar manyan motocin guda hudu mutanen garin suka fara kallo suna mamaki wane babban mutum ne ya shigo garin, ita tai ta kwantance hanyar da za abi a isa gidansu a lokacin da ta suka shigo garin Bandalo. Kamar taron kasuwa haka kaiwa kofar gidan Bappa da fifi ana kallon manyan mutane da mamakin su waye a ciki, wasu dai sai fadin suke Fadime ta janyo musu da mata rigimar wasu kuma na fadi daga Katsina aka aiko a tafi da Bappa kowa dai da abunda yake fada, dogaran dake tare da Baba Waziri ne suka fita suka isa bakin kofar gidan Bappa suna masa sallama irin wanda dogarai suke yi a kofar gidan talaka. Inna ce ta fito jiki na rawa tana amsawa domin Bappa yana gurin sana'arsa a lokacin, daman abu ne mai wahala ka tararda shi a gida irin wannan lokacin. Fadime na ganin Inna ta yi saurin bude motar ta fito, Inna ma tsaye tai tana kallonta sai hankalinta ya bar gurin dogarawan da take musu bayanin cewar Bappa ba ya gida.

“Inna�

Fadime ta fada tana fashewa da kuka, sai Inna ta rufe baki jikinta na rawa kamar zata fadi a gurin, da gudu Fadime ta je ta rumgume ta, jamar'ar gari suka hau leke kowa na mamaki, kuka sosai Inna da Fadime suka yi, sannan ta rika hannu Fadime suka shiga gida, makota da yan uwa kusa ne suka fara shigowa suna mata barka, wani makocinsu ne ya hau babur dinsa ya isa har inda Bappa yake ya sanar masa dawowar Fadime da kuma motacin da aka shigo garin da su tare da ita, take Bappa ya rufe shagonsa ya hau Babur din mutanen suka kamo hanyar dawowa gida da tunani kala kala a ransa, shi dai tsoro ya fi kama shi sama a lokacin da yai arba da manyan motocin, fargabarsa daya kar ace wata jamgwal din ce Fadime ta sake janyo musu. Sai a lokacin ne Baba Waziri ya fito daga motar bayan an gabatar masa da Bappa a matsayin mahaifin Fadime, Bappa faduwa yai kasa yana kwasar gaisuwa jikinsa sai rawa yake, ko mutumen birni ya yaji a gaban sarki balle na kauye, da sauri fadawan da suke tare da Waziri suka zo suna gyara masa rigarsa suna masa kirari, gaisawa yai da Bappa sannan ya gabatar masa da kansa sannan ya isar masa da sakon Mai Martaba na kudi da kuma gaisuwa, daga bisani kuma ya gabatar masa da albishir din Shattima na gidanda ya siya masa a Kt, daya daga cikin mutanen da suke tare da Wazari ne suka kira Shattima yai magana da Bappa a waya sannan ya kara tabbatarsa masa da abun da Baba Waziri ya fada, kuma ya fada masa cewar idan ya kimtsa yai masa magana a waya zai turo Ra'ees ya dauke shi ya kai shi har inda gidan ya ke kuma ya hannanta masa komai, Bappa sai ya rasa bakin magana ko godiya sai kuka, yana ganin komai kamar a mafarki.

_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Khadeeja Candy*

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Chapter 152 · 0% Book details