← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 172

Sashe 59

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ku ce wacan mutumen ya yafe min dan Allah, Wallahi ba zan sake ba, jama'a wuta a cikina, na ci Tanin na ci Murja yar gidan Almajiri, daga na aike ta na tankwashi kanta na kama kurwarta na cinye ta, na ci yar gidan Hajiya Ayawa ta birni na kama mai gadinsu, kurwarsa na cikin dakina�

Kusan duk wanda ta ci ko ta kama sai da ta fada, ta saka hannu biyu ta dafe cikinta sai kuka take, idan tai yunkuri kuma sai aman jinin. Sosai mutanen da take fadar ta ci yayansu suka so afka mata da duka Dattijawan da suke gurin suka hana, Wani makocinsu ne ya hau babur dinsa dan zuwa fadawa Bappa halin da ake ciki. Ba iya mutanen da ta ci ba har mutanen da suke maitar tare sai da Amo ta fada. Hajjo na tsaye ta rasa inda zata saka kanta sai kuka take.

“Kaka ta bawa uwata Maitar nan, uwata ta ba ni, ni kuma na bawa tun da ban haifa ba? Yau na yi leke na ga mugun abu, wuta ce a cikin tana ta ci kun ganta�

Sai nunawa mutane cikinta take tana ta tarin jini, kowa sai matsawa yake nesa da ita.

“Ina zama mage ina zama doki har kadangare ina zama, ina zama jaki ina zama bakin kare, idan dare yayi a filin can nake rawa, jama'a wuta a cikina�

Ta karasa a galabaice. Inna dai na tsaye tana kallon ikon Allah hawaye sai zuba suke mata, bata jin dacin wata magana kamar wacce ta ji daga bakin Amo ba a yau, ta cinye mata É—a tara, saboda ita bata taba haihuwa ba bata san zafin haihuwa ba, ka dauki ciki wata tara ka haihu, wasu ta yi rainonsu wasu kuma tun suna kanana suke mutuwa, ko da rana daya Amo bata tausaya mata ba Fadime ma dan ta gagareta ci ne.
Juyawa Inna tai ta koma cikin gida tana jin wani irin zafi da bakinciki a ranta, uwa ce kadai kan iya labarta yadda bakinciki rasa da yake, balle ita data rasa yara har tara, zaunawa tai a kujerar dake tsakar gidan ta fashe da wani irin kuka, ta sani ko da zata yanka Amo a yanzu ta gasa namanta, ta soyata ba yaranta ba za su dawo ba, kuma ba zai goge bakincikin dake ranta ba. Tun ba yau Inna ta dade tana zargin Amo da maita tun a wani lokacin da suna fira take fada mata suna da maita gado ga kuma mafarkai da take kala-kala akan amman bata taba tabbatarwa ba sai a yau da idonta ya gani zahiri, hannu ta saka ta dafe zuciyarta tana jin wani irin zafi a kirjinta, ta haifi yara goma sai Fadime ce ta tsaya, kuka sosai Inna take tana ayyana yadda wasu yaran suke mutuwa a hannunta da irin azabar da suke sha kamin su mutu, da kuma ita ma irin wahalar da take da wasu. Shigowar wasu makotan ne yasa ta tsagaita kukan da take tana jin wani irin son Fadime na kara fadada a kirjinta ganin ita kadai ta rage mata a rayuwa.

“Ki yi hakuri Allah ya saka miki Allah ya isar miki�

Shi ne mafi yawan abun da mutanen ke fada, ita kam ta kasa ce musu komai, kukan kawai take hawaye na mata zuba domin ita kadai tasan zafin da take ji a ranta. Da yamma lis, Bappa ya iso, shi ya riko Amo ya shigo da ita cikin gidan, kana ganin fuskarsa kasan babu walwala a tare da shi, domin ko baka son mace baka son ta fita waje daga ita sai dan kanfai balle matarka ta sunna ga kuma tonon asirin da take ta yi ma kanta. A tsakar gidan ta fadi tana ta ihu har lokacin ta kasa dawowa hayyacinta tana ta faman rikon ciki tana fadin wuta, har kamo hannun Hajjo take tana kaiwa a cikin nata.

“Allah ka yafe min na tuba Allah, ba zan kara ba, wayyo wuta wuta a cikina na shiga uku, Fulani ki yafe min ki ce masa na bari�

Babu irin tambayar da Bappa be mata ba ina ta samo ciwon me ke damunta? Amman ta kasa bashi amsa sai fadin take wuta a cikinta domin bata cikin hayyacinta. Can ya koma gurin Fadime ganin tana ta ambatar sunanta.

“Ke kin san wani abu ne?�

Fadime ta yi saurin daga hannunta sama.

“Aa ni ban san komai ba, Allah ya tsare�

Yadda tai da ido sai ka rantse da Allah bata san komai ba, bayan labarin na kasan halshenta, sai dai tana tsoron fada kar ta sha duka gurin Bappa.
           Bappa fita yai daga gidan gaba daya ya koma can gefe ya kira wani Kawunta bugu biyu ya dauka.

“Assalamu Alaikum Kawu Manu�

“Wa'alaikassalam, Sama'ila ya gidan ya kowa?�

“To Alhamdulillah, Kawo ina bukatar ganinka yanzu idan kana da dama ka zo dan Allah�

“Lafiya dai?�

“Lafiya amman ba lau ba ka daure ka zo dan Allah�

“Dare ya fara yanzu haka na yi alwala sallah magariba, indai ba wata matsala ce babba ba ka bari har gobe biyo mota na zo�

“Aa ka zo dai yanzu Kawu�

“To shikenan idan mun gama sallah zan kamo hanya yanzu�

“To Allah kawo ku lafiya�

Bappa ya sauke wayar daga kunnensa tare da sauke ajiyar zuciya, sam be ji dadin abunda ya faru ba sai dai be isa ya hana komai ba, ba tun yau Inna ta dade tana masa maganar zargin da take na Amo shi kansa ya dade da sanin abun da take sai dan gudun kar ya budewa Inna da take kishiyarta da kuma sauran mutane damar fada ko aikata wani abu yasa be taba nuna yana zarginta ba idan ma Inna tai sai ya kwatsuleta saboda be taba gani da idonsa ba, sai dai irin tonon asirin da tai wa kanta a yau da kuma fadar irin mutanen da ta ci ya canja masa tunani, an labarta masa komai tun kamin ya iso bayan ya iso kuma ya ga komai a idonsa. Dawowa yai cikin gidan a lokacin Inna na tsugune tana alwala Fadime kuma na zaune gefen bukkar Inna ta rafka uban tagumi tana kallon Amo dake ta dalalar da jini a baki ta rike ciki sai kuka take muryarta ma bata fita. Inna sai da ta gama alwalarta sannan ta zubawa Bapppa ruwa a butar ta kawo gabansa ta aje, fuskarta kawai yake kallo yadda idonta ya kumbura kana ganin kasan ba karamin kuka ta sha ba.

Shi kansa da yake uba abun be masa dadi ba balle kuma ita da take uwa ta san zafin daukar ciki da haihuwa. Bukkarta ta shiga ta dauko tabarma ta shimfida waje ta saka hijabinta ta fara sallah magariba. Fadime na ganin haka ta tashi itama ta dauki wata karamar buta tai alwala ta shiga bukkarta ta dauko hijabinta ta saka ta tsaya kusa da Inna ta kabbarta sallah.

Daga garin Dan-isa zuwa garin Bandalo tafiyar awa daya ce har da yan mintuna a mota, balle kuma su Kawu Manu da suka hau babur din dansa suka kamo hanya saboda babu motar da zata je garin Bandalo a yanzu. Tara saura kwata suka iso garin, ba shi da aka kawo ba har dansa daya goyosa a babur din zullum abun da za su ji ko su tarar yake, sun sani duk abun da zai saka Bappa ya nemi ganinsa ba karamin abu ba ne a matsayinsa na uban daya rage ma Amo a yanzu. Ko da suka iso Bappa na tsaye bakin kofar gidan tare da wasu abokaninsa biyu, sai da ya mika musu hannu suka gaisa sannan yai musu iso.

“Kawo Manu Bismillah�

Bappa ne a gaba Kawu Manu na bayansa tare da dansa suka shiga cikin gidan, tun kan Bappa ya labarta masa komai ya fahimci ba lafiya ba, ganin Amo a tsakar gidan Hajjo na gafenta tana kuka, Inna da Fadime kuma suna kan tabarma zaune fitilar aci balbal na gafensu. Amo na ganin Kawu Manu tai saurin mikewa tsaye ta nufo inda yake tana fadin.

“Kawu ka fada ma Fulani ta fada masa na daina dan Allah ta cire min wutar nan, ba zan sake maitar ba zan daina Wallahi�

A take gumi ya karyo masa, ya juya ya kalli Bappa sai kuma ya saka hannunsa aljihu ya haska Amo, gaba daya ta fita daga kamaninta ta canja kamar ba ita ba ga wata uwar ramar wahala da tai har lokacin kuma idan tai tarin sai jini ya fito ta bakinta, sai wani leko halshe take waje tana zaro ido kamar sabuwar mahaukaciya, tun da take a rayuwarta bata taba shan wahala ko shiga jalala irin wannan ba. A tsanake Bappa ya labarta Kawu Manu komai sannan ya dora da cewar.

“Ban san abun da ya faru ba, Aisha ta fada min cewar daga bandaki ta fito wahale tana ta aman jini tana ihun wuta a cikinta kamin ta fara tonawa kanta asiri, daman kuma ba tun ba na dade da fahimtar abun da Amo take yi, sai dai ba ni da hujjar fadin hakan saboda ban gata ido da ido ba, amman yanzu ita da kanta ta tonawa kanta asiri�

Kawu Manu ya gyara tsayuwarsa yana kallon Amo kamin ya haske Fadime da fitilarsa mai shegen haske.

“To ita wannan da take ambatar sunanta bata san komai ba?�

Inna kamar tana jira ta mike tsaye tana nuna shi da yatsa.

“Kurwar Fulani kur Wallahi sai dai ku ci kanku, kuma duk abun da Amo tai min na bar ta da Allah shi zai saka min�

Inna ta karasa cikin kuka tana jin wani irin zafin a ranta, wani murmushi Kawu Manu yai ya tabe baki har lokacin fitilarsa na haska Fadime.

“Inna ki yi shiru, Allah shi zai saka miki Allah ya isar miki�

Fadime ta fada tana sharewa Inna hawayenta, ita kuma tana wasu hawayen ganin zubar hawayen Inna yasa ta ji wani irin no matter how mother is É—a ko Æ´a baya son ganin kukan uwarsa, ganin yadda yake ta kallon Fadime yasa Inna ta mai ita bayanta.

“Fulani bata ciyuwa Wallahi sai gani sai bari, kurwarta kur mugun abu ya bi dare ku ga abun ku a kanku�
Chapter 59 · 0% Book details