← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 172

Sashe 46

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bapppa ya gyada kai dan ya san daga shi sai abokin nasa su kai wannan maganar, kuma abokinsa ba sa'an Fadime ba ne balle yace shi ya fada mata, yanzu kan ya fara yarda aljanun ne sai dai ba zai yarda su cutar masa da ya ba.

“Kwarai kuwa an yi haka, wai me kuke nema a jikinta ne?�

Fadime ta yi shiru tana tunanin abun da zata fada, can ta tuno da som bada magani da take da kuma maganar wutar da Wasim ya fada mata ko ma karya ne yai mata shi yake saka mata wutar yau zata mata rana.

“Magani zamu fada, saboda akwai mayu a ko'ina masu bin mutane da wuta, kuma akwai mugayen bil'adama�

Fadime na rufe baki, Amo tai fuu ta shige bukkarta tana jin mararta na cika da fitsari, ga wani uban rawa da jikinta yake kamar mazari. Bappa ya girgiza kai.

“A a ni ƴata ba zata yi bokanci ba, haramun ne sam ba zan bari ba, ko dai ku fita daga jikinta ko nasa bulala yanzu na zaneku kuma na muku karatu na kone ku�

Fadime na jin zancen bulala ta kwanta a gurin.

“Mun tafi sai anjimanku bye bye bye�

Ko minti biyu bata yi ba ta mike tsaye wai aljanun sun tafi. Inna dai sai kallon tsoro take mata. A daren Amo kasa fita rawa tai duk kuwa da irin yadda jikinta take tsuma na son fita rawar da take, gashi gobe Bapppa zai juyo da girkinta ba damar fita tun da kwana biyu biyu suke. Haka nan dai ta daure ta fito tsakar gidan, sai ta zagaya can bandakin dan wuta har ta fara fita jikinta, tana shiga ta fara É—aye fatar jikinta ta cireta tsaf sannan ta aje a gefen wani dutse da ba za a gani ba ta fara karanta wasu abubuwa tana rawa da halshe tana birke ido, sai ta fara kankancewa tana yin kasa ta dora hannayenta a kasa irin yadda dabbobi suke yi, a take jikinta ya fara gashi hallitarta ta canja daga mutum zuwa bakar mage, tsale daya tai ta tsallake zanar da aka zagaye bandakin da ita sai gata a filin dake harabar wajen zanar, a nan ma cigaba da karanta abun da take karantawa gashin ya fara barin jikinta ta dawo a mutum sai ta mike tsaye ta fara rawa wuta na fita a jikinta idonta ta sauya kala kamar ba nata ba, halshenta sai rawa yake kamar zai zazzago kasa, sai dai kafafuwanta suna nan a na mage tana ta rawa da su tana barin sawu, can kuma ta sake zama magen ta tuma ta dafa kan bukkar Fadime tana wani iri kuka na tayardar hankali, Fadime na fara ihu ta sauka ta nufi makotansu. Sai dai bata yardar ta bar sawu a na makonta ba saboda ta san, idan maye yai rawa da dare, da safe idan aka duba inda yai rawar zaka tararda sawun irin dabbar daya zama yai rawa, idan doki ne ko zaki ko mage ko kare ko akuya ko kura ko saniya duk za a gani matukar sun yi rawar a kasa.

(Allah ka mana tsari da mayu da duk wani abu mai cutarwa, suna cikin al'umma ba iya gane su sai Addu'a)

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660 or 08061371579*
03/12/2021, 09:22 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*

Tun a jiya da Ammy ta fada mata cewar zata rika zuwa aiki 7am sai ta aje daukan ruwa, tana tashi da safe ta share ko'ina ta yi wanke wanke sannan ta shiga tai wanka, ta shirya ta saka Hijabinta ta fito garin ma be gana wayewa ba, ta fito ta saka talkaminta ta isa kofar Tumba wacce ke dunkule tana bachi.

“Umma Umma�

Sai da ta jera mata kira ya kai goma sannan ta amsa.

“Ya akai?�

Tumba ta amsa da karfi.

“Zan tafi aiki�

“To ki tafi mana ina bachi zaki wani tashe haba mana�

Falmata ta juya ta kama hanya, sai da tai addu'ar fita daga gida sanna ta fita tana tafe tana kallon unguwar ta so da mutane ba su gama fitowa ba. Idan Tsohuwa mai koko ta biya, ta shiga gidan da sallama, tsohuwa dake zaune tana kunna wuta ta amsa mata.

“Falmata ce�

Sam bata ji abun da tsohuwar tace ba sai kawai ta dora mata da gaisuwa da kuma bukatar abun da ya kawo ta.

“An tashi lafiya, Tsohuwa dan Allah kina da goro ki sammanin?�

Tsohuwa ta gyada kai tana murmushi.

“Eh ina da goro kuwa yau goro za a ci�

A nan kam ta ji abunda tsohuwa tace domin tsohuwa ta fada da karfi tana unkurin tashi.

“Eh dan kunne zan like�

Daki tsohuwa ta shiga ta dauko goro daya ta raba rabi ta mikawa Falmata.

“Gashi yar albarka�

Falmata ta saka hannu biyu ta karba.

“Na gode Allah ya saka da alheri�

Ta juya cike da jindadi ta fice daga gidan, a yau ba ta titi ta bi ba saboda tana son diban furen tunfafiya da yake a tsakankanin gidanjen da ba a gama ba na unguwar. Ta cikin unguwa take tafiya har isa gaban wani katon gida da aka fara gine ba a karasa ba, gefen gidan ciyawa ce sai tunfafiyar da ta fito da yawa wata babba wata karama, sai dai ba ko wacce ce ke da fure ba, haka ta rika bi tana dubasu har ta samu wacce ke da fure ta tsinka ta jimke tare da goron sannan ta kama hanya.
Sai kusan 7:40am ta isa, kamar kowa kowa hada hadarsa kawai yake ita kuma tana tafe tana rabon ido ko zatai yi arba da Iya, so take ta kara tabbatarwa idan har da gaske mayya ce, jiya dai kam bata ganta ba har ta bar gidan. Cikin sa'a kuwa Falmata ta hangota tana magana da suwa hadimai da alama nuna musu take inda za su gyara. Da sauri Falmata ta balla goron ta saka furen tufafiyar a baki tana taunawa, sai mulgunar baki take kamar wata tsohuwa, tana isowa gurin Gate din ta mikawa Iya gaisuwa sai kallonta take.

“Barka da safiya�

Suna hada ido Iya tai saurin kawardar kanta tana yamutsa fuska kamar wacce tai arba da kashi, ta daga mata hannu alamar ta wuce ta wuce kawai.

“Almu dauko min karen can�

Ta nuna karen iccen mangoro daya fado tana ta kokarin juyawa dan kar ta sake ganin Falmata, da sauri Falmata ta nufi karen ta dauko ta miko mata da yatsu biyu dan kara tantancewa, domin a iya saninta ba a nuna maye da yatsu biyu yatsan manuni da mai binsa ba a mika musu abu da shi ko a nune su da maye da mai sirihi donin manuni yana karya lagon mutun, Mama ta taba fada mata haka tun bata girma sosai ba. Falmata na mika mata karen Iya taja baya ta bude baki tana kallon yatsun Falmata.

“Ya haka haka? Miye haka kuma? Miyasa zaki yi haka? Amman dai baki kyauta ba, ke wai wace irin yarinya ce�

Maganar kawai take kamar wacce ta rude sai kallon karen da Falmata mika mata take ta kasa hada ido da Falmata dake ta aikin taunar goron tana kallon cikin idon Iya da mugun mamaki. Jefar da karen tai ta nufi cikin gidan tana waige Iya, a yanzu kam ta tabbatar Iya mayyace dan ga zahiri ta gani, abubuwan nan biyu da tai bayan na shekaranjiya da ta fara mata addu'a ta kawar da kai.

‘Ke nan ita din mayyace, amman su ba su sani ba�

Ta fada a ranta, tana cigaba da tafiyar tsoro na kara shigarta domin bata taba arba da maye ido da ido kamar yanzu ba. Har da isa bakin kofar tai knocking aka bude mata bata daina tunani ba. Har kasa ta kai ta gashe da Jekadiya sannan ta mike tsaye ta nufi dakin yan uku, samunsu tai a kwance suna bachi, kamar yadda aka fada mata ba a shara idan suna cikin daki dan haka ta dauki Labib a hankali ta fito da shi daga dakin ta nufi dayan dakin da aka nuna mata jiya, tana shiga ta samu babban gado da kayan wasan yara kala kala a dakin kamar wani karamin kamfani, ga fentin dakin pink, washe baki tai tana kallon yadda aka tsara dakin kamar ba a mutuwa, wai kuma nan dakin yara ne, ko da yake ko a tsarin gidan ta duba ai ta san sun isa.
Sai da ta gama bawa idonta abinci sannan ta aje Labib akan gadon dake shimfide da zanen gado dan ubansu mai taushi da laushi ga shi sai sheki yake kamar an zuba masa kyalkyali. Juyawa tai ta fita ta dauko Luma ita ta dawo da ita dakin ta kwantar kamshin dakin sai dukan hancinta yake.

Komawa tai dayan dakin ta gyara shi tsab sannan ta dawo inda suke ta tararda da sun farka har sun fara kuka, da sauri ta dauki Labib ta rarrashinsa sannan ta fita dashi daga dakin ta koma dayan dakin ta dorashi akan gadonshi ta bude wardrobe ta dauko madararsa ta dama masa da ruwan zafin dake cikin flask aka dora a dorowar, ta zuba a cikin fidarsu ta fara bashi. Sai da ta tabbatar ya koshi sannan ta dauko Luma ita ta shayar da ita, bandakinsu ta shiga ta hada musu ruwan zafi sannan ta fito ta fara cire musu tufafinsu ta saka su a cikin ruwan dumin data hada ta wanke musu kashi, ta nade su cikin wani farin tawul. Cikin kuzari Labib ta hau wasa Luma kuma tana da kuka sama sama. Kanta Falmata ta dafa ta karanta masu addu'ar tsari wacce Annabi S. A. W yake karantawa jikokinsa, sannan ta dora mata da ayatul kursiyu, sai da ta gama da Luma sannan tai wa Labib, ganin taki daina kuka yasa ta goyata da tawul tana jijjigata, tana yi ma Labib wasa daga tsayen da take.

Wata hidimar ce ta shigo dauke da babba tray ta aje wa Falmata a gabanta.
Chapter 46 · 0% Book details