Sashe 146
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
***
Karfe goma da yan mintuna direba da ya dauko Mama Fulani da Shattima da Aliyu da kuma Fadime ya faka harabar masarautar. A nan kallo ya koma sama gurin Fadime, girman masarautar da kyauta har tsoro ya bata ba dan ta san masarauta ba ce ita kan sai tai zaton unguwa ce mai zaman kanta ko wani babban kamfani. Yawan hadiman da suke ta harkokin gabansu ma kadai abun kallo ne, tafe take idonta na kalle kalle duk da kasancewar bata cikin farinciki da walwala saboda Wasim. Ita kadai aka bari baya tuni Aliyu da Muhseen sun wuce gaba sai Mama Fulani da ke binsu, sai da ta shiga bangaren Ammy ta gane bata ga komai a waje ba, domin tsaruwar falon da yadda aka kawata shi ya wuce misali, ko'ina kallo take tana bawa ido hakkinsu, sai a yanzu ta yarda wata sarautar ta fi wata lallai wani dan sarki ya fi gaban wani sarki, kamar wata kurma haka ta shiga cikin dakin Ammy sai kalle kalle take, idonta na sauka akan Ammy sai ta ji wani irin kwarjininta ya cika mata ido, gurin haske da gashin gira iri daya ne da na Shattima, sai dai Shattima ya fi ta kyau nesa ba kusa ba, zaunawa tai a kasa tana ta kallon tsadadden lace din dake jikin Ammy da ke gaisawa da Mama Fulani, jin an taba kofar dakin yasa ta juyo sai tai arba da Shattima da ya shigo sanye da farar shadda mai wani irin haske da daukar ido, bakar hular kansa ta saka fuskarsa har wani annuri take, ga dogon hancinsa ya kara fitowa kamar an ja shi, farar fatarsa ma sai shining take kamar wani balarabe, murmushin da ya yafawa fuskarsa sai ya kara fito da saka siffar zatinsa da kwarjinin da ya cika idon Fadime har ta mike tsaye tana kallonsa, gaba daya ya canja mata kamar ba shi ba, wata kila ba dan tana da tabbacin fuskarsa a wayar da tai da shi ba sai ta rantse da Allah ba shi ba ne.
“Zauna...�
Ya fada yana nuna mata gurin zaman a dai dai lokacin da kamshin turarensa ya kai mata hari a hanci. Zaunawa tai ba tare da ta dauke idonta daga gareshi ba shi kuma ya wuce inda take yana yi ma Mama Fulani sannu da zuwa.
“Mama barka da sauka�
Sai da ya gama gaisawa da ita sannan ya kalli Fadime ya sakar mata murmushi.
“Tashi ki zauna akan kujera mana�
Bata motsa ba balle tai alamar tashin sai kallonsa take tana jin zuciyarta na bugawa da mugun karfi.
“Wacan akwai rigima tun jiya kuka take ban san abun da akai mata ba, na yi tambayarta har na gaji, yau kuma da ta tashi ba ta yi ma kowa magana ba�
Mama Fulani ta fada, sai Ammy ta kalleta
“Ko bata da lafiya ne?�
“Lafiyarta kalau�
Shattima ya amsa yana kallon da tai masa mugun kyau kasancewar a cikin bakar abaya, irin kyau nan na fulanin asali masu haiba da daukar hankalin namiji.
“Ina Muhseen?�
Ya tambaya ba tare da ya dauke idonsa daga barin kallon Fadime ba, kamar yadda ita ma ta kasa dauke nata idon, sai sakwanni suke turawa junansu.
“Sun fa riga ni shigowa, na dauka ma nan suka shigo ai, maybe sun wuce gurin Mai Martaba ne, na ji Aliyu na fadin ma zai koma yau�
“Hmm dan wajen Fulani ba a son shiga mutane sai dole�
Ammy ta fada, sai Shattima ya mike tsaye.
“Fateema ya hanya? Za ki ba ni labarin jirgi dai ko?�
Ta kasa cewa komai kamar ba ita ba sai kallonsa take, daman tun a jiya bakinta ya mutu saboda Wasim, yanzu kuma da ta zo nan ta ga wata sabuwar duniya sai ta raina kanta bakin ya kara mutuwa mututus. Murmushi ya sake sakar ya kanne mata ido daya for the first time, hakan ya saka ta hade yawu da karfi ta cigaba da kallonsa har ya fice daga dakin, sannan ta kai hannu ta dafa zuciyarta.
Ta inda Mama Fulani take shiga ba nan take fita ba, ta rufe Ammy da fada kan shirun da tai bayan sanin komai, bata kara sanin Annabi a faku ba sai da Ammy ta labarta mata abun da Hajiya Babba take, kamin a jera musu abun ci da na sha ta dauki wayarsa ta kira Baba Waziri ta sanar masa sun iso kuma tana son ganinsa kamin ta iso gidansa, bata kashe wayar ba sai da ta soma lasa masa zumar abun da ya faru, ko awa daya ba kara ba sai ga Baba Waziri a gidan cikin tashin hankali, a nan Mama Fulani ta zazzage masa komai na abun da ya faru kana Ammy ta dora da nata. Ba karamin baci ran Baba Waziri yai ba kuma be ga laifin kowa ba sai Ammy.
“Amman kin ba ni mamaki Ammy, ni yar'uwa na daukeki ba matar dan'uwa ba, ta ya za a hada kai da matata a cutar da dan'uwana kuma kin sani ki kyale ba ki fada min ba? Ta ya matar dan'uwana za ta so kasheshi kuma ki zuba ido kina fadin baki da hujja, kin san abun da ake nufi da makiyi kuwa? Ashe baki dauki ran yayanki da kuma Mai Martaba a bakin komai ba kenan�
“Ato ni ma abun da na gani kenan, kasan wannan har zaka boye yanzu hakaabun da take fada min wai bata labartawa Mai Martaba abun da Hajiya Babba take ba, ta dai fada masa an kaita asibiti bata da lafiya�
Baba Waziri ya jinjina lamari.
“Ni na yi mamakin irin abun da Hajiya Talatu take yi, na san tana son Maijidda amman ba irin son da zai sakata shiga wannan halin ba saboda mutuwarta, shiyasa da aka kaita asibiti likitocin suka ce ba su ga komai ba kwakwalwarta lafiya kalau take, kuma sai sunayenku take ambata�
“Ni ma na yi mamaki sai dai na yi zaton ko saboda mutuwar ne�
Cewar Ammy tana sauke ajiyar zuciya.
“Dole ne Mai Martaba ya san da wannan maganar, kuma har abada Juwairiyya ba zata taba yin albarka ba har abada�
Baba Waziri ya fada cikin wani irin bakinciki da bacin rai marar misaltuwa.
“Kar a tsine mata abun da ta aikata kadai ya isheta�
Ammy ta fada sai Mama Fulani tai mata wani kallo.
“Allah ya tsine mata albarka, yarinya tai yi kokarin kashe mahaifinta kuma ki ce kar a tsine mata, Allah ya kwashe mata albarka ita da uwarta�
Ammy ta runtse ido tana girgiza kai ko kadan bata son abun da ya shafi tsinuwa domin ta san yadda take cin jiki da dukiyar mutum.
***
Sai dare Shattima ya sake saka Fadime a idonsa, fitar da yai dazun daga dakin Ammy gurin gaisuwa yaje be tashi ba azahar daga can kuma ya wuce asibiti zuwansa na farko tun bayan da akai masa transfer, guri shugaban asibiti ya fara zuwa suka gaisa da shi daman sun san juna yai masa maraba sannan yasa akai masa iso zuwa office dinsa, ko da isa ya samu office dinsa da komai a kintse, takardunsa da komai na sa da yake can Ra'ees ya turo masa su a nan kuma an jera masa sa komai, kwalayen da ke aje gefe ya rika budewa yana dauko abubuwan da ke ciki tare da dorasu a muhallin da yake so, a kwali na uku yai arba da littafin Fadime, murmushi yai ya zauna a saman kujerarsa yana karantawa tana da good handwriting domin duk abun da ta rubuta babu wanda be gane ba, gurin dariya sai yai murmushi, labarinta ne tun daga kan mafarkin da take har zuwa haduwarta da Wasim da abubuwan da suka faru har zuwa kadeta da Shattima yai da neman aurenta da Ra'ees yai komai sai da ta rubuta kadan ya rage littafi ya cika, samun kansa yai da dariya sosai a gurin da yake karanta karyar da yi ma su Bappa da kuma gurin da Wasim yake mata dabon maciji.
“Wow...�
Ya furta yana jinsa cikin nishadi marar misaltuwa, har ga Allah yana son Fadime ta dayan bangaren kuma yana jin dadin rabuwar da Wasim yai da ita. Ya wuni a asibiti har biyar na yamma sannan ya nufi gidansa, a nan ma sai ya rika tuna irin abubuwan da suka yi ta faruwa a lokacin da ya kawo ta gidan.
“Ko miyasa ta zama shiru yanzu�
Ya tambayi kansa yana daura tawul.
‘Maybe saboda ta rabu da Wasim�
Wani bangare na zuciyarsa ya ba shi amsa, sai ya kai hannunsa ya tura kofa bandakinsa ya shiga ya tsaya gaban madubi yana kallon kansa.
“Yes no one can take my place, ke dai kin jin kewa yarinya amman ba rabuwar kauna ba, ai ke ba ki san so ba, yanzu dai za ki sani�
Ya fada with smiling yana kallon kyakkyawar kirar mazantakan da Allah yai masa. Ya shafa kansa yana murmushi tunawa da lokacin da take cewa ina ruwanta da ko shi waye, and the time da ta rike masa kafa akan ba zai tafi ya barta a gidan Zainab ba, da kuma lokacin da take fada masa Jekadiya ta zaunar da ita a kasa.
“I like her�
Ya furta yana cire tawul din ya aje muhallinsa, sannan ya sakarwa kansa shawa ya lumshe ido yana maida numfashi a hankali. Bayan ya gama ya fito daure da tawul din ya shiga kicin cup ya dauko ya matsa lemun tsami a ciki ya saka kanwa ya zuba ruwa kadan a ciki ya sha.
Be bar gidan ba sai da akai magariba, a masallacin da ke unguwar yai sallah magariba sannan ya karasa masarautar yai isha'i a can, daman tun shigowarsa dakin Ammy ya lura Fadime bata ciki sai ya sulale ya nufi dakin Nana, duk da ba shi da tabbacin tana ciki, tura kofar dakin yai ya shiga, sai ya samu Fadime kwance a kasa gefen gadon Nana, tana ganinshi sai tai saurin tashi tana share hawaye. Karaso yai kusa da ita ta duka gabanta.
“Miyasa kika kwanta kasa�
“Gadon na Gimbiya ne ai, be kamata na hau ba�
Ta fada tana murza ido, kallon gadon yai sai kuma ya kalleta.
“No ke ma ai sarauniya ce karki sake zama kasa�