Sashe 20
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan ma alamar kurame tai mata, sai Falmata ta juya ta shige cikin dakin ta dauki wasu tufafin ta saka ta saka hijabinta ta fara sallah.
Bayan ta gama tai addu'ointa kamar yadda ta saba sannan ta fito ta gyara ko'ina na gidan tai wanke wanke, ba ta ko tsaya tambayar abincinta ba ta fice da zimmar zuwa gurin aikin karya.
Tana tafe tana nemawa kanta mafita, ta sake komawa gidansu Khadija ko kuma dai ta koma gurin aikin ta sake ba su hakuri? Domin idan wata yayi Tumba zata tambayi kudinta na albashi to me za ta ce mata? To idan ma ta koma za su karbe ta ne? Sai ta rasa wanda za tai, daga karshe dai ta yanke shawarar zuwa gidansu Khadija domin har ga Allah ita yanzu tsoron zuwa gidan can take, abun da bata sani ba Naja na biye da ita a baya tana lekenta kamar yadda Tumba ta saka ta. Sai dai ita bata lura ba har ta shige cikin gidansu Khadija. Yau kan bata samu Khadija a gidan ba dan ta tafi islamiyar safe kasancewar yau Sunday, Maman Khadija bata tsaya komai ba ta zubo mata abinci, Falmata ta zauna ta ci sai da ta koshi sannan ta nemi guri ta kwanta tai ta bachinta. Sai kusan azahar sannan Khadija ta tashe ta, firgigit ta mike tsaye dan lokacin komawarta gida yayi har ma ya dan gota.
Duk yadda Maman Khadija da ita Khadijar kanta suka so Falmata ta tsaya ta ci abinci sai ta ki gaba daya hankalinta ya tashi kar ta koma late Tumba ta doketa.
“Ko na zuba miki a leda?�
“Idan ta gani zata iya min fada�
Duk da rada Khadija take mata maganar. Bata jira abunda Khadija zata sake cewa ba ta fice daga gidan hankalinta a tashe, da sallama ta shiga gidan Naja ta amsa mata tana tabe baki.
“Ashe idan an tura ki aiki gidansu Khadija kike zuwa kina zaunawa ko? Ai na biki dazun na gani�
Naja ta fada cikin daga murya ta yadda Falmata zata iya jinta. Wani irin bugawa gabanta yai da karfi, da zaro ido tana kallon kofar dakin Tumba sai ta nufo gurin Naja ta riketa.
“Dan Allah Naja karki fada, dan Allah ki rufa min asiri�
Tana rufe baki Tumba na fitowa daga dakinta ta tsaya bakin kofa rike da kunkuru tana hararar Falmata, da sauri Falmata ta mike tsaye ta fashe da kuka, a take tsoro ya kamata ta rika ganin kamar Tumba dukanta za tai sai ta fara ja da baya baya tana ganin Tumba ta motsa ta fice daga gidan da sauri. Komawa tai gidansu Khadija ta zauna, a can ta wuni har dare ba ta fada musu abun da yasa ta gudo ba, sai dai suna ganin yadda hankalinta ya tashi sun ssn ba lafiya ba. Sai bayan sallah isha'i Naja ta zo kiranta, cikin rashin kuzari ta tashi suka fita daga gidan tare tun kan su karasa gida ta fara kuka.
Suna shiga cikin gidan fara rabawa jikin gina tana kallon mahaifinta dake watso mata harara.
“Gata nan ashe idan an turata aiki gidansu Khadija take shiga, yau aikin komai ba tai ba can ta wuni, ni dai dan Allah ka yi mata tsakani da yarinyar ba ma yarinyar kirki bace Wallahi�
Tumba ta fada tana narke murya kamar gaske.
“Wato Falmata duk abun da za a fada miki ba kya ji ko? Kullum sai kin tsiro wani bakin hali ko?�
Bata ji abunda Tumba ta fada ba amman ta ji abunda mahaifinta yace shi da yake da tsawa yake mata magana.
“Zo nan....�
“Baba dan Allah ka yi hakuri sun kore ni kuma ina tsoron komawa gidan da? Allah kai hakuri gobe zan je�
Ta fada cikin kuka.
“Zo na ce....�
Ta fara tafiya tana kuka tana kallon Tumba tana jin kamar ta taso ta zo ta cece ta, irin yadda mahaifiyarta take mata idan za a doke ta, gabansa taje ta tsaya ta rika hannunta ya murde iya kar karfinsa sai da ta fasa wani irin ihun ta fadi kasa.
“Wayyo Baba Wayyo Baba dan Allah kayi hakuri, ka yafe min Baba karka kashe ni dan Allah�
Sakin hannun nata yai ya rika hijabinta yaja ta daga inda take kwance har gurin da tumakinsu suke daure, ya kwance igiya daya ya daure mata kafa tamau, zai juya ta riko kafarsa.
“Dan Allah Baba ka yi hakuri, karka ba ni na kwana a cikin tumaki dan Allah Baba�
Kasa juyowa yai kuma ya kasa tafiya har cikin ransa yake jin kukan yarsa idonsa suka cika da hawaye, amman sai ya ji ba zai iya mata komai ba bayan haka, fisge kafarsa yai ya fice daga gurin ya barta tana ta kuka. Tun tana kukan tana kiran sunansa tana bashi hakuri har koma kiran Tumba tana bata hakuri daga kashe sai ta hakura ta kwanta a gurin tana ta hawaye, ba hawayen kwana a gurin kadai ba har da hannunta da take jin kamar ya karye saboda mugun rikon da Baba yai ma hannun nata, ga kafarta da ya daure da karfen rodi ya tsuke mata kafar sosai.
Ba tai wani bachi kirki ba saboda kuka da ciwon hannu da kafa da kuma warin fitsarin dabbobin dake gurin, sai da rana ta fara fitowa sannan Tumba ta zo ta kwance ta.
“Na gode�
Falmata ta fada tana kallon Tumba da idanuwanta da suka kankance tsabar kuka da wahala, ba ta yi zaton za ta kwance ta wuri haka ba ya dauka ko sai ta kwana biyu ko fiye ma.
“Tashi kije ki shirya ki tafi gurin aikin�
“To�
Ta fada jikinta na ta rawa wani irin sanyi take ji yana ratsata kamar zazzabi na son rufe ta. Duk yadda ta so tai wanka kamin ta fara yin sallah sai ta kasa saboda hannunta bata iya komai da shi ga kafarta ma dingishi take, haka nan dai ta wanke jikinta sannan tai alwala ta shiga dakinsu ta saka wasu tufafin tai sallah ta fito tana jin jiri na dibarta ta durkusa a wahale ta gaishe da mahaifinta.
“Baba ina kwana?�
Be amsa ba daman yana tsaye ne yana sauraren abunda Tumba take fada masa akan Khadija cikin tsawa ya ce.
“Babu ke babu Khadija daga yau, balle har ki je gidansu, na miki tsakani da ita�
“To Baba�
Ta amsa masa tana jin kamar ba zata iya numfashi ba, ga idonta sai ciwo yake, mikewa tai tsaye bayan ta gaishe da Tumba ta nufi kofar fita kamar wata musaka ta fice daga gidan. Da kallo Baba ya fita har ta fice sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali ta yadda Tumba ba zata ji ya juya ya koma cikin dakinta.
Kai tsaye Masarautar Falmata ta nufa a ranta tana ta addu'ar Allah yasa su karbe ba, domin idan ba su karbe ta ba bata san yadda zata yi ba, kamar yadda ta saba sai ta gaishe da kowa take shiga ciki, sai dai bata tsaya jiran su amsa tun da ko sun amsa idan ba su kwarai ba ba ji za tai ba. Sai da ta kawo gate din da zai sadata da bangren Ammy cikin rashin sa'a ta hango Iya tsaye ita da wasu matan gidan tana magana, a take jikinta yai sanyi, ta san ko kowa zai ji rokonta ya karbi uzurinta ban da Iya, duk da baya san wacece ita ba amman ta lura da bata son ta tun farkon zuwanta gidan, bayan Iya akwai Zainab da Shattima su ma tana tsironsu ba ma kamar Shattima da shi ya kamata da kansa tana taba masa ya.
 Ji tai ba zata iya karasawa ciki ba ba kuma zata iya komawa gida ba, sai kawai ta koma gurin kofar babban gate na uku ta zauna tana ta kukanta marar sauti.
*****Â Â Â *****Â Â Â Â *****Â Â Â *****
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un�
Shi ne abun da kowa yake fada, Ammy ta karbe ta daga hannun Baaba tana jirgizawa, amman babu alamar rai a tare da ita
“Hajiya a kira likita�
“Ko kuma a je asibiti kai tsaye ba�
Ammy ta hada hankalinta a tashe, Iya ce ta karaso gurin tana tambayar abun da ya faru.
“Wallahi Luna ce, ta buga kwallowa, tana ta ihu ko da muka daukota jikin yayi zafi kamar wuta, daga nan bata sake motsi ba�
“Innalillahi�
Iya ta fada tana karbarta daga hannun Ammy.
“Ayi sauri a tafi asibiti ai ba tsayawa za ayi ba�
Ammy da kanta ta shiga ta dauko mayafinta ita da Baaba da Iya suka nufi asbitin. A lokacin ne labarin ya karade Masarautar kowa ya san abun da ake ciki ban da Nana da hankalinta be kai can ba, domin tana bangaren Hajiya kuma Hajiya ba ta yi magana a gabanta ba ita kadai ce a falon tana ta kallon Tv duk da hankalinta baya wajen.
Ta kusan minti talatin a falon sannan ta taso ta dawo bangarensu, ta tararda manyan masu hidimar gidan zaune a falon cikin har da wasu kanen mahaifinta mata da suke zaune cikin masarautar, amman Nana bata tsaya ta kula kowa ba balle ma ta tambayi abun da yake faruwa. Kai tsaye ta wuce dakinta ta shige da rufo kofar ta hau saman gado ta kwanta, jikinta na bata ba lafiya ba amman ba zata iya tambaya ba.
Sai da ta ji hayaniyar na so ma yawa har da masu kuka sannan ta fito ta tsaya jikin kofar dakinta tana kallon Hajiya Karama dake kuka sosai ita da sauran matan, Shattima na zaune kan cushion kansa a kasa Iya kuma na zaune kasa tana kusar kuka kamar ba gobe. Sai a lokacin gabanta ya so ma faduwa, kar dai Mai Martaba ya rasu? Da sauri ta karasa fitowa ta nufo gurin da Shattima yake zaune ta zauna tana tambayarsa.
“Ya miya faru why kowa yake kuka?�
“We lost Luna�
Ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba. A take ita ma ta fashe da kuka ta riko shi.
“Ya How?�
Dagowa yai ya kalleta da idonsa da suka rine su kai ja, kana ganin kasan ransa a bace yake.
“Lokacinta ne yai�
“Ita take?�
“Tana ciki za a mata sutura�