← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 172

Sashe 78

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kit Nana ta katse kiran kana ta kashe wayar gaba daya tana jin wani sabon kuka na taso mata. Saurin maida wayar tai kasan fillon ta sauko kasa ta saka talkaminta na bedroom ta fice daga dakin sanye da kayan bachi, kanta ba ko dakwali. Ta jidadin samun falon babu kowa hakan ya bata dama fita ta fadar Ammy ta sauka kasa ta nufi bangaren Hajiya. Tana kokarin hawa stairs din ta hango Hajiya na saukowa tare da Jarma, hakan yasa taja ta tsaya har sai da Hajiya ta sauko kasa.

“Daughter har kin tashi?�

“Eh Good morning�

“How was your night?�

Cewar Hajiya tana sakar mata murmushi, Nana ta juya ta gaishe da Jarma.

“Baba ina kwana?�

“Lafiya Kalau Mamana�

Ya kiranta da irin sunan da Mai Martaba yake kiranta da shi, sannan ya kalli Hajiya.

“To ni na wuce sai an jima�

“Tau a gaishe da gida�

Sai da ya wuce sannan Nana ta kalli Hajiya da fuskar tausayi kamin tace komai Hajiya ta tari numfashinta.

“Daughter yanzu Jarma yake fada min ya gano inda yaron nan yake, yana cid, amman wai sun ce ba za su bada shi ba sai sun gama bincike ki kwantar da hankalinki zai fito soon kin ji�

Nana ta masa cewa sai kasa tai da kai, bata son ta nunawa Hajiya cewar ta ji abun da take fada jiya saboda tana jin nauyin Hajiya sosai kuma tana sonta fiye da Ammy, gaba daya ma ta rasa gane miyasa Hajiya tai kalaman jiya. Juyawa tai ta fara tafiya zuwa part dinsu ba tare da tace wa Hajiya komai ba. Dakinta ta koma ta zauna bakin gadonta tana ta tunanin halin da AA zai kasance, kamar an tsikareta ta mike tsaye ta bude wardrobe dinta ta dauko after dress ta saka saman kayan bachinta ta dauki mask dinta ta saka ta saka hijabinta ta nufi kofa, sai da ta fara lekawa falon ta ga babu kowa sannan ta fito da saurinta ta fice ta kofar gaba, kasa ta sauko gaba daya kamin ta isa gurin da tasan direbobin gidan na zama har da hadawa da gudu dan kar Ammy ko wani ya ganta. Direban Ammy na hangota ta doso gurin ya taso ya nufota da sauri.

“Almu, fita zaka yi da ni akwai key a hannunka?�

“Eh�

“Mu tafi�

Tun kan su karasa kusa da motar ya danna key hannunsa motar ta fita lock, da sauri Nana ta bude baya ta shiga shi kuma ya shiga driver side ya kunna motar yai warming dinta, sannan yai reverse ya fita harabar, kamin su isa gate Nana har ta matsu, sai da suka hau titi unguwar sannan hankalinta ya soma kwantawa.

“Gimbiya ina zamu je?�

“Cid�

“Police station Gimbiya?�

“Eh�

Daga haka bata sake cewa komai ba har suka isa, daga waje ya faka motar sai ta bude ta fito.

“Ka jirani a nan na dawo�

“Tau�

Ta doshi cikin cid din duk kuwa da kasancewar bata taba zuwa ba, gabanta sai faduwa yake kar ta hadu da wanda ta sani ko ya santa. Kai tsaye ta nufin cikin gurin ta shiga, gamin yawan police da kuma mutanen da suke tsaye dan shigar da kara ko sasanci sai yasa ta ji wani iri, sai da ta dake sosai sannan ta isa gabansu.

“Dan Allah ina neman Sardauna�

“Sardauna Sardauna, yaushe aka kawo shi nan?�

“Jiya da dare�

“Daga ina?�

“X&L Hotel�

Police din ya dauko wani littafi dake saman gurin yana dubawa.

“Ahmad Aminu Sardauna ko?�

“Eh eh..�

Ta amsa ba dan tana da tabbacin hakan ne cikakaken sunansa ba. Sai police din ya dauko keys ya mikawa na kasa da shi.

“Fito da Sardauna�

Police din ya karbi key din ya nufi cell din dake ta warin fitsari. Nana na tsaye aka fito da AA sanye da farar vest sai dan guntun wando, fuskarsa ta kumbure idonsa daya ma ya rufe baya iya gani da shi, kafarsa ta dama ma tsikarata yake yana takawa daker, kana ganinsa kasan ba karamar wahala ya sha ba. Wani sabon hawaye ne ya cika idon Nana tana ta kallonsa har ya karaso inda take tsaye. Yana ganinta ya gane ta, ga mamakinta sai ya sakar mata murmushin karfin hali da fuskarsa da ta kara bayyana ramarsa daman can ba wata ki bar kirki ce a jikinsa ba. Sai Nana ta rasa kalmomin da zata hada tai masa magana, har sai da ya fara mata.

“Nana...�

“Na'am dan Allah kai hakuri, laifi na ne�

“No haka Allah ya rubuto, don't say that da ace ke aka kama kara ni, daman ni dan talaka ne, na san zai taba mutumci na amman ba kamar ke ba, just ki yi wani abu a fitar da ni daga nn pls na san hankalin Antina yana can ya tashi�

“Ban san me zan yi ba, ba zan iya yin komai ba, Hajiya Babba ce kawai take taimaka min, ita kuma naji tana fadar ai tana son a juyar da case din zuwa kisan kai, Hajiya Karama kuma bata nan, Ammy kuma ba ta saurareni ba har marina tai jiya�

AA ya ziro mata kai jin ance ana son juyar da case din zuwa kisan kai.

“Kisan kai fa kika ce Nana? Miyasa me nai? Miyasa zata min haka? Baki fada mata gaskiya ba?�

“Na fada mata, ni ma ban san abun da yasa zatai haka ba, na ji tana fada a waya ban san da wa take wayar ba amman na ji, kuma na ji tana cewa har abun da ya fi sata sai na yi, kuma sai Ammy ta yi kuka da idonta, i don't know why Hajiya ta fadi haka�

“Waya haife ki tsakanin Ammy da Hajiya Babba?�

Ya tambaya duk kuwa da kasancewar be sansu a fuska ba sai a suna shi ma ta bakin Nana.

“Ammy amman Hajiya Babba ta fi so na, komai na ke so tana min kuma ita bata min fada bata kyamata kamar Ammy�

“So Hajiya Babba is your step mother right?�

“Yes kuma she is my mother in-law, saboda dan ta zan aura....�

Shiru yai yana kallonta, indai har haka ne miyasa zata ji dadin lalacewar Nana? Miyasa ba zata jidadin abun da yai ba sai ma ta nemi juyar da abun?

“Ammy tana miki fada akan zuwa makaranta right? While Hajiya Babba bata miki fada? Ammy tana miki fadan kashe kudi Hajiya Babba bata yi?�

Duk abun da ya fada sai ta daga masa kai.

“And tana so na sosai fiye da Ammy komai nake so tana min, har lallaba ni take na auri Sirleem danta�

“Kishiyar uwa bata taba son da fiye da uwar da ta haifi dan ba Nana, Hajiya Babba ba son ki take ba, wata kila tana miki komai ne saboda tana son rayuwarki ta lalace, kuma tana son ki auri danta ne saboda wata manufa, indai har tana son ki ba zata tai wannan furucin ba, kuma zata ji dadin abun da nai, ba wai ta juyar da abun ya zama babba ba�

Ya karasa hawaye na sauko masa, sam be dauka abun zai zama haka ba, be ji nadamar aikata abun da ya aikata ba sai yanzu, ya jefa kansa da yar'uwarsa a matsala bayan duk gargadin da tai masa.

“Amman zan fito da kai, zan yi wani abu, ban san miyasa na aikata ba, i regret this, duk laifina ne�

Nana ta fada tana kuka ganin hawaye na zuba a fuskarta AA. Hannu ya saka ya share hawayensa yana kallonta, duk sai ya ji tausayinta ya rufe shi, for what he understand Nana tana da damuwa amman a a saurarenta, tana son gata da rayuwar morewa amman ba a tsara mata rayuwar yadda zata jidadinta ba, sannan hankalinta da natsuwarta bata cika kamar na sauran yan mata sa'aninta ba, ga kuma abun da ta aikata jiya, da ace ba tare yake da ita ba da ta kunyata fiye da kima, and if he can remember ta fada masa bata san abunda ya saka yayi ba hannunta kawai yake kaikayi, ga kuma rashin son zuwa makaranta da take wanda shine silar haduwarsu, wanda be san dalilinta na kin makaranta ba.

“Nana�

Ta kalleshi da idonta da suka gama ja tun kukan data sha jiya.

“Promise me something�

“What it's?�

Ta tambaya daker saboda kukan da take mutane dake gurin sai kallonta suke.

“Matso da kunnenki�

Ta matsar da kunnenta kusa da shi.

“Ki min alkawari ba zaki sake fashin zuwa makaranta ba, kuma ki min alkawarin ba zaki sake daukar abun wani ba, ko da kuwa na Ammy ne ko na Hajiya, kuma ki min alkawari ba zaki sake zuwa bangaren Hajiya ba, komai ta baki ba zaki karba ba, and no matter how hannunki yake miki kaikaiyi karki dauki abun wani, ki bar wajen, kuma zaki yi ma Ammy biyayya a matsayinta na mahaifiyarki, ki cire cewar Hajiya tana son ki a zuciyarki ki aje gefe�

“Amman bana son makaranta�

“Ba zaki iya min wannan ba? Ba zaki iya daukar min alkawari ba? Ni da nai miki wannan abun kuma na shiga wannan halin saboda ke? Kuma kin ji sun ce case din zai juya zuwa kisan kai ne? Ba zaki iya zama yarinyar kirki saboda ni ba?�

“Na dauka na maka alkawari, zan yi duk abun da ka ce, kuma ba zan bari su juyar da abun ba, na san yadda zan yi, i will talk to Sirleem�

“Who?�

“Her son my boyfriend�

“Dan ta ne, karki sake kula shi ki samu wata hanyar ba wannan ba, wata kila a da hadin kansa ake komai, karki sake kula shi okay�

Ta daga mishi kai.

“I will find another way, and i will fulfill your promises�

“Thank Youu�

“Zan tafi�

“Karki karya min alkawari�

Ta gyada kai tana kura masa ido kamin ta juya ta fara tafiya tana ta sake-saken hanyar da zata fi ta fitar da AA daga wannan halin. Cikin motar ta koma ta shiga direban ya kama hanyar gida.

“Bangaren Hajiya zaka sauke ni�

Ta fada ganin sun doshi masarautar gadan-gadan.

FALMATA POV.
Chapter 78 · 0% Book details