← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 172

Sashe 51

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Falmata ta sirina tana gaishe ta amaimakon ta amsa sai ta dauke kai ta nufi hanyar dakin Ammy hannayenta rumgume a baya tana wani irin taku kamar wacce ba zata mutu a rufe da kasa ba. Bakin kofar dakin ta tsaya tana dan saurare ko zata ji Ammy na wata magana bata ji komai ba sannan tai knocking.

“Shigo�

Ammy ta fada muryarta a sanyaye kana ji ka san akwai damuwa a tare da ita. Hajiya ta tura kofar ta shiga cikin jindadin yadda ta samu Ammy da damuwa duk kuwa da kasancewar bata san minene matsakarta ba, amman tana jindadin ta ganta a damuwa ko cikin kunci. Sai da tai Bismillah sannan ta zauna tana kara kallon Ammy da kyau dan fahimtar damuwarta.

“Ya gidan?�

“Al-hamdulillah�

“Daman na zo ne akan maganar auren Rukaiya�

Ammy ta dago kai tana fuskantarta jin ta ambaci yar minitan aiyuka da za a aurar.

“Na san kusanci Alhaji Nasiru da na Mai Martaba kusanci ne sosai wanda da ace Mai Martaba yana da lafiya shi zaije da kansa ya bada auren yar aminsa, amman haka Allah ya tsara shine nake tunanin Talba sai wakilce shi yaje yai komai kamar Mai Martaba�

Wani kallon mamaki Ammy take mata.

“Wane irin Talba kuma? Ga Waziri ga Jarma ga Ubandoma ga Lado duk a rasa wanda zai wakilci Mai Martaba sai Talba? Aiko ko Shattima yai karanta balle kuma Talba da yake kannensa�

“Ai dan na ga Shattiman baya nan ne yasa na yanke shawarar kanensa ya wakilce shi�

“To gaskiya ba zai yiyu ba, mun riga mun gama magana da Waziri shi zai je ya wakilci mai martaba�

Ammy ta fada kai tsaye, daman can haka take duk abunda akai a gidan wanda take ganin be dace ba zata fito tai magana idan kuma shawarace Hajiya ta kawo ko wani shi ma idan ta ga be yi ba zata hana ko tai magana, wannan dalilin ne yasa Hajiya take mata ganin tana mulki mallaka a gidan kuma ta mallake Mai Martaba, domin lokuta da dama zata kawo shawara idan Ammy ta ga abun be dace ba zata hana ko kuma ta kawo tata shawarar kuma sai Mai Martaba ya bi, domin yana son Ammy sosai kuma yana kyautata zaton ba za yi wani abun na son kai ba. A can baya babu yadda Hajiya bata so akai Rima kasar waje karatu ba amman Ammy ta hana saboda kula da wasu halaye na banza da Rima ta tsira tun a nan, take ganin idan aka kaita can karatunta zai lalace ne haka ma rayuwarta kara dai tai karatun a nan inda ake ganinta ake saka mata ido kuma ayi mata fada idan tai ba daidai ba tsabanin can da babu mai tsawarta mata. Sai dai wannan abun ya tsayawa Hajiya a rai duk kuwa da kasancewar an kai Jurry sai take ganin kamar Ammy bata son cigabanta ne ganin ita ta haifi biyar ita kuma tana da biyu shine take mata hassada.
Dan murmushi Hajiya tai ta mike tsaye kamar ba komai.

“To Allah ya kyauta, ni zan koma bangarena�

“A huta lafiya�

Ammy ta amsa mata, sai da Hajiya tai mata wani kallon sannan ta dauke kai ta fice daga dakin tana mamakin yadda har yanzu Ammy take mallake komai bata son a san da danta a iyalin Mai Martaba.

‘Babu komai lokaci na zuwa, zaki wayi gari kina kuka da idonki, zamu gani tsakanin tawa da taki wacce zata zama karya�

Ta fada a ranta bayan ta fito daga dakin, arba da ta sake yi da Falmata ya tuna mata da sunanta na dazun.

“Falmata....�

Ta furta da muryar da ita kadai zata iya ji tana kallonta kamar a razane, tsaye tai cak tana kallon Falmata kamin ta karasa fitowa daga corridor.

“Jekadiya miye sunan yarinyar nan?�

“Falmata�

Jekadiya ta amsa mata tana kallonta Falmata dake tsaye.

“Falmata...�

Hajiya ta sake maimaitawa sannan tana kara kallonta da kyau, wani irin dogon numfashi taja ta sauke sannan ta nufi hanyar da zata fitar da ita daga falon, sai da ta isa bakin kofar sai kuma ta juyo ta kalli Falmata da mugun mamaki sannan ta juya ta fice.

‘Taya zata lalata mana shiri? Taya? Amman ga zahiri a fara gani, lallai Ammy tana mana milkin mallaka a gidan nan har a kawo wata sabuwar mai hidima ban sani ba? Na zama kashi kenan?�

A ranta take ta wannan sake-saken tana nufar bangarenta.

“Dole ne na kara mikewa tsaye, kar maganar nan ta tabbata�

Wannan karon a fili take maganar tana tura kofar katon falonta ta shiga. Sirleem na ganinta ya yanke wayar da yake da Mansura ya mike tsaye, dan ya san zai sha fada amman sai ya ga damuwa a fuskarta bata ko kula shi ba ta nufi dakinta, sai da ta shige sannan ya ciro wayar ya sake kiran line ta.

“Miyasa baki jin magana? Kin san yadda ake saka mana ido amman zaki biyo ni a nan?�

“Amman Sirleem kasan ba zan iya jure rashinka ba na tsawon kwanaki, ban san ranar dawowarka ba ba zan iya zama a can ba�

“Fine gani nan zuwa�

Ya sauke wayar tare da ajiyar zuciya, sannan ya nufi dakin mahaifiyarsa domin sanin dalilin damuwarta.

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*
03/12/2021, 09:23 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*

Cikin natsuwa Sirleem ya shiga dakin mahaifiyarsa, tana ganinsa tai saurin aje wayar hannunta.

“Ya akai?�

Kai tsaye ta tambaye shi abun da bata saba ba. Mamaki ne ya bayyana a fuskarsa.

“Na ga kamar kina ciki damuwa ne�

“Aa ba komai ka je inda zaka je waya na ke son yi�

“Amman kin tabbatar da babu wata matsala?�

“Na fada maka ba komai mana Sirleem ka tafi inda zaka je�

Ta amsa masa da dan fada domin ta matsu ya fita daga dakin. Juyawa yai cike da mamakin yadda Hajiya take masa ya fice. Mikewa tai tsaye ta isa gurin kofar ta saka mata key sannan ta dawo ta kira number Jarma, yana dagawa ta labarta masa komai shi kanshi ya cika da tsananin mamaki.

“Kin gani ba ni san mutanen nan basa taba mana karya�

“Ada can ina ganin abun kamar wasa, amman ganin wannan yarinyar ya bani tsoro kuma ya saka na yarda, yanzu miye mafita?�

“Mafita kawai a koreta daga gidan mana, babba ce?�

“Karama ce ba zata wuce warin Nana ba, ni abun ya bani mamaki ma, taya zata iya lalata mana aiki? Ko dai tana da aljanu ne?�

“Ko ma dai minene abun da nake ganin yafi kawai a koreta daga gidan, matukar tana cikin gidan nan zata bata maka lamari da tsari�

“To amman ya za ayi na koreta tun da bangarena take ba?�

“Haba Hajiya kamar ba mace ba, ki yi tunani mana, ni anjima zan shiga na gaishe da Hajiya dan na ga yarinya�

“Okay shikenan ai dole mu san abun yi kam�

Ta sauke wayar tare da sauke ajiyar zuciya tana tuna sauran abubuwan.

“Fadime Falmata Sardauna, wacece Fadime kuma? Waye Sardauna?�

Ya mike tsaye tana ta tunani.

“Sun ce akwai tafiyar da ba dawowa? Wace tafiya ce kenan? Wa zai yi? Mu ko kuma bangaren Ammy?�

Safa da marwa ta fara yi a dakin.

“Ina kyautata zaton yarinyar tana da aljanu ne wata kila zata fada ne, in ba shi ni ban ga ta inda zata iya lalata mana shiri ba? Kamata yai nai mata sanadi da gidan nan cikin ruwa sanyi ko kuma ayi mata asiri ta bar gidan gaba daya�

Sai kuma ta girgiza kai.

“No ai idan mu ka mata asirin idan tana da aljanu zata iya fadar gaskiya ta tona mana asiri�

Wayarta ta nufa ta kira Hajiya Talatu ta labarta mata abunda yake faruwa.

“Wannan maganar ba ta waya bace ranki ya dade zan shigo gobe da kaina�

Daga haka ta aje wayar, gaba daya ta rasa yadda zatai ta natsu, haka ta wuni cikin tunani kala kala ta kulla wannan ta kwance wacan ta saka wannan ta ga be yi ba, babu abun da yafi tsaya mata a rai kamar yadda Falmata zata lalata musu shiri as how kuma ta yaya? Lokaci bayan lokaci sai ta ambaci sunan Falmata Fadime Sardauna tana jinjina lamarin.

SHATTIMA POV.

A kofar gate din Hajiya a mutu ya faka motarsa duk kuwa da kasancewar Zainab ba son zuwa gidan domin yan uwan Hajiya Babba ne ita kuma ba wani shiri take da Hajiya Babba balle kuma yan'uwanta.

“Ina jin gobe zan je Yola, zan turo miki number police din da za su raka ki a can idan kin shirya kawai ki kira su zasu same ki har inda kike�

Zainab ta kalleshi.

“Amman Lafiya zaka je gobe? Ko ka sake samun hutu ne?�

“Baba Waziri ne yace yana son ganina, ya kira ni da safe yace idan zai yiyu mu hadu da a yau, nace masa sai dai gobe�

“Okay Allah ya tsare, ni ba zan dade ba, domin bana jindadi sosai kuma ina son na gama cikin kwana biyu koma�

Hannunsa ya mika ya dauko diary sa yai rubutu a kai ya cire paper ya mika mata.

“Ki ba wani ya karbo miki wannan maganin�

“Thank you�

Ta fada bayan ta karba, sannan ta bude motar ta bita, sai ya jira ta dauki akwatinta dake boot sannan yaja motarsa ya dauki hanyar asibitin, gaba daya wunin ranar daya tuna abun da Fadime ta saka Ra'ees sai yai murmushi, sai yana daf da tashi aikin sannan ya kira Ra'ees a waya bugu daya abokinsa ya amsa.

“Hello�

“Matsoraci�

“Uhmm Allah yasa kaji abun da naji, ba zaka gane ba ne Wallahi�

Shattima yai murmushi kasaita wanda ya karawa fuskarsa kyau da kwarji sannan ya sake magana a hankali.

“Gobe dai zaka yi duty na, zan leka Yola�

“Lafiya dai?�

“I don't know, Baba Waziri ke nema kuma tun har ya bukaci ganina kasan abu ne mai muhimmanci�

“Allah yasa alheri ne ya tsare�

“Amin�
Chapter 51 · 0% Book details