Sashe 37
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
‘Ni ma idan na yi aure haka zan yi, sai na yi girki nai komai irin na mata, kuma na haihu ni ma�
Ta saka a ranta tana shafa cikinta murmushi ya wanke fuskarta. Mikewa tai tsaye ta nufi gurin ruwa ta dauko wani tulun.
“Ina zaki je?�
“Ruwa zan debo�
“Aa ba yanzu ba, jiya jiya kika je kika kwashe aiki yanzu kuma kice zaki je, a a ban yarda ba, waya sani ko gulbin ne ke da aljanunn�
Amo dake cikin daki ta fito tana amsawa Inna.
“Lallai kam indan ruwa bari Hajjo ta debo sai ta cika mana gidan�
Ba dan ranta ya so ba ta aje tulu ta koma ta zauna ta fara motsa kokon tana ta tunanin abun da zata yi ta fita. Bata sha rabin kokon ba sai ga Ma'u ta shigo gidan bakinta har rawa yake sai dai gani Inna yasa tai shiru bata ce komai ba bayan gaishe da ita da tai sai kuma ya jikin da tai mata. Can dai Ma'u ta tashi tana kyafta ma Fadime ido.
“Na tafi Fulani Allah kara sauke�
Sai Fadime ta mike tsaye tana satar kallon Inna.
“To bari na rakaki�
Har sauri saurin take ta riga Ma'u fita daga gidan. Suna fitowa Ma'u taja ta gafe
“Fulani Wallahi naje na fadawa Inna Bubakar kin ce mijinta zai kara aure nan da kwana biyu�
Fadime ta zaro ido.
“Miyasa kika fada ba nace miki sirri ba ne�
“Dan dan ta tabbatar idan da gaske ne kuma ni na tabbatar, yanzu ta aiko tace a kira ki�
“Wallahi ba zan je ba, dan ta karyata ta ni ko? Ko taja Bappa yai min duka�
“Ba duka zata ja miki ba, kika san ko kudin zata baki tace ki fada mata wani abun�
Duk yadda Ma'u ta so taje kiran da Matar take mata sai Fadime ta ki saboda ta san bata da gaskiya, idan aka ce waya fada mata dole tace aljannun ne kuma tasan Bappa zai iya dukanta ko ya sake mata wani karatun.
“Ki ce mata anjima zan zo�
Ta juya ta koma ba tare da jira abunda Ma'u zata fada ba. Dawowa tai ta zauna, da an yi sallah sai ta ji gabanta ya fadi dan gani take kamar matarce zata so ta fadi maganar a gaban Inna. Can dai ta tashi ta shiga daki ta rubuta abunda ya faru jiya tun daga kan yadda su kai da Wasim har zuwa karatun da akai mata da aljanun karya da tai. Ana gama sallah la'asar Fadime ta kwance shanu wai zata je gurin kiwo.
“Fulani kin san yadda kika yi jiya, ki bar zuwa kiwon nan sai gaba idan kin samu lafiya�
“Ni lafiya ta kalau, idan ina zaune ma sai na ji kamar nai ihu ai kara naje dajin dai�
Duk yadda Inna ta so Han Fadime zuwa kiwo a yau abu ya ci tura, dan Fadime tsayawa tai kai da fata akan sai taje ganin Bappa ya tafi gari, ta sani idan shi ne bata isa ta musa masa ba duk kuwa da irin son da yake mata.
Haka ta kora shanun suna gaba taba biye har suka isa cikin daji, a iya alkawarin da tai a yau ba zata yi magana da Wasim ba, kuma ba zata sake kusantar inda yake ba, duk kuwa da irin burin da take da shi na wani taimako da take son yai mata, kin magana da shi na nuna fushinta ne, ta dayan bangaren kuma tana jin tsoronshi, dan ta san duk mutunen da zai iya dabon maciji a take ba karamin matsafi ba ne.
A inda ta saba zama ta zauna, tana ayyana cewar ko ta ji busarsa ba zata leka ba, zuciyarta na raya mata dole zai zo inda take. Kamar yadda ta saka haka ta faru tana jin takun mutum a gefenta ta ki ta daga kai ta kalli gefen dan ita ala dole tana fushi. Murmushi ne mai kama da dariya a fuskarsa, ya zauna kusa da ita yana kallonta, sai ta ki ta juyo balle ta san da mutum a gurin, dauke kai yai yana cigaba da murmushin mai kama da dariya yana cin guava dake hannunsa, can kuma ya leko fuskarsa wacce ita ce tafi komai daukar masa hankali a cikin hallitarta, bayan kyau da fari da gashi Fadime bata da wani abu da za a kalleta da shi a ce ana sonta, domin kirjinta da shi da babu duk daya, balle ayi maganar mazaunai.
Wata uwar harara ta watsa masa, har ga Allah haushinshi take ji kuma da ace ba shi bane tabbas da mai raba su a yau sai Allah, amman tana tsoron tai masa wata rashin kunyar ko wani sherin yai mata wanda ya ci uban nata.
“Ina ta tunaninki tun jiya�
Ya fada yana kokarin danne dariyarsa, domin babu abun da be sani ba na isa da tai da maciji a kanta. Ta masa banza tana son ta harare shi ba dama tun da tana tsoro. Ya mika mata guava hannunsa.
“Karbi ki ci�
Ta yatsina fuska alamar kyama, daman can bata jin ragin kowa ciki har da Babanta da Inna balle kuma shi. Dan karamin bakinta ta kurawa ido yana ta kallonsa sai ta soma jin halshenta na motsawa, ta kalle shi da sauri.
“Me ka min?�
Ba shiri ta rufe bakin jin muryata kamar ta wani kwaro. Ta mike tsaye da sauri tana zaro ido.
“Wayyo Bapppa�
Kamar wani karamin kwaro na magana haka muryarta ta zama, zata ranta ana kare ya riko ta.
“Zaki min magana?�
Ta gyada kai da sauri hawaye na sauko mata, sai yai murmushi yana kallon fuskarta yana jin kamar ya hade ta, duk wani motsi nata burgeshi yake. Bakinta ya sake kurawa ido sai ya halshenta ya sake motsawa bata bari ya kara ta sa hannu ta rufe baki tana fashewa da kuka, sai ya kara rike ta gam yana dariya domin fisge fisgen take tana son ta subuce daga rikon da yai mata.
“Ki zauna idan ba haka ba, ba zan gyara miki halshen ba, kuma zaki tafi da shi gida a haka, zaki zauna�
Ta gyada kai da sauri, sai ya sake ta har lokacin dariya yake, ta zauna saman karamin dutsen sai ya mika mata guava daya bata dazun ta ki karba, kamin yace komai ta karba ta saka a baki ba ta ma wani tsaya taunawa da kyau ba ta hade.
“Na hade�
Sai ta ji muryar kamar duro, a take ta fashe da wani irin kuka, sai kuma tai saurin yin shiru ta rufe bakinta domin ita ma kanta tsoron muryar take, ji take kamar kukan da muryar ba a bakinta suke fitowa ba. Ta fara masa na kurame alamar roko tana nuna masa bakinta. Sai ta sake jin halshen ya motsa zata saka hannu ta rufe ya rike mata hannun. Wani uban ihu tai shi kanshi sai da ya duke kanshi ya runtse ido saboda kyakyar muryarta har cikin kai take shiga.
Wani mamaki ne ya cika ta jin muryarta ta dawo daidai, sai tai dan murmushin tsoro tana kallonshi.
“Dan Allah da gaske kai ba aljani ba ne?�
Ya zauna kusa da ita yana ta kallonta.
“Ni mutum ne mana, bana fada miki muna tsafi ba�
“Na yarda...�
Ta fada cikin tsananin mamaki tana kallonsa.
“Miyasa kake kallo?�
“Burgeni kike�
Ya ansa mata still yana kallonta, sai ta nuna kanta.
“Kana so na kenan?�
Sai ya dauke kai yana murmushi, ita kuma ta ji kunya ta rufe ta, ai be kamata ta tambaya, idan yana sonta shi ya kamata ya fada, ba ita ba. Ta sinne kai kasa tana yan zanezane.
“Ba ni labari�
Ta dago kai amman sai ta kasa kallonshi saboda kunyar maganar dazun.
“Ba ni da labari... �
Ta yi shiru, shi dai sai kallonta yake can kuma tace.
“Kishiyar Innata tace ta min miji a birni, amman har yanzu be zo ba�
“Aure za a miki?�
Ta yi shiru ita dai kam tana son aure a rayuwarta, da za a mata auren ma a take da ta huta. Ta kalleshi
“Zaka iya min tsafi na gan shi? Ko ka kira shi ya zo?�
Yayi murmushi yana kallon cikin idonta.
“Kina son ki san mijinki?�
Ta daga kai ta sauri.
“Eh�
Ya mika mata hannunsa.
“Kawo hannunki�
Sai ta miko masa hannun, ya dora saman tafin hannunsa yana kallon idonta.
“Washhhh sanyi hannu sanyi sanyi�
Ta fada tana saurin janyewa.
“To duk namiji da ya taba hannunki kika sake jin irin wannan sanyin shine mijinki�
Da dan bude ido tana kallon hannun nata.
“Da gaske? To mu gaisa�
“Idan kika ji sanyi a hannunki fa?�
“Shikenan kai ne mijin�
“Idan kuma ba kiji ba fa?�
“Shikenan ba kai ba ne�
Ya mike tsaye yana murmushi ya ciro guava a yar karamar jakar da ke kugunsa, sai tai saurin kai hannu ta taba hannunshi, saurin fisgewa yai.
“Tafin hannunsa zaki taba ko ya taba naki, idan tafin hannunki da hannun wani namiji su kai taba juna kika ji sanyi to shine mijinki�
Yana fadar hakan ya fara tafiya yana cin guava.
“Ina zaka je?�
“Garin mu�
Tayi shiru tana kallonshi.
“Miyasa jiya nan kai min tsafin maciji a nan ba a gida ba?�
“Ba ke kike ce a miki ba�
“Amman ai ban ce a nan ba, a gida na ce�
“Ina son ki ba ni nishadi ne shiyasa�
Ya fada yana ta kallonta. Sai tai dariya.
“Har da karyar aljanu nai nace sunan aljanina Sama'ila, kuma sunan Bappa na ne�
Shi ma dariyar yai, ya sake kai guava bakinsa sannan ya mika mara ragowar. Sai ta girgiza kai alamar a'a tana kyankyami, be ce mata komai ba yai murmushi ya juya ya cigaba da tafiyarsa har ya haye saman dutsen ya dago mata hannu ita ma ta daga masa, sannan ta sauke tana kallon hannun na shi.
“Yana zuwa zan taba h.... �