Sashe 136
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Kana sonta kake bari tana cutuwa? Ka nisanta da iyayenta? Ka kaita inda aka gusar da hankalinta? Kuma ka saka take kokarin rasa idonta? Wanda kake so za kai masa fatan samun farinciki ko kuwa farincikinsa na nufin bakincikinka ne�
Ya lumshe ido yana jin wani irin kalar yanayi da be taba jin irinsa ba, yana tuna kalaman Zainab.
“Wani lokacin dole ne mu sadaukar da farincikin mu saboda wadanda mu ke so su samu farinciki...�
Kansa ya daga sama sai ga hawaye sun sauko masa ta gefen idon, wani irin zafi da radadi yake ji idan yai yunkurin tunanin rabuwa da Fadime.
“Rabuwa da Fadime ba shi yake nufin na auri Liya ba, kuma ba zan taba barinta ta samu farinciki ba�
“Kana da damar auren wanda kake so matukar jininmu ce, amman wacan yarinyar idan za ka kashe maza dubu ka zata yi mu'amala da su, ba za ta taba aurenka ba�
Hannunsa ya daga sama ya daki tsakiyar kansa da dukan karfinsa ya rufe ido yana girgiza kai. Mikewa yai tsaye yana wani irin huci kirjinsa har wani sama yake kamar sai yi tsalle.
“Zan rabu da ita, amman sai na taba mutanen da suka taba ta, sai sun shiga kunci fiye da ita�
“Wannan kuma aikin duna ne, zan zan nemo shi... Na ka aikin ka tafi gurin shugaba ka fada masa ka yarda da dokinsa, ni kuma zan bude idanunta�
Kakansa ya fada da yarensu, sai Wasim ya kalli inda Fadime ta ke yawan zauna a lokacin da ta zauna dakin kakansa. Matse hannayensa yai yana jin rabuwa da ita kamar fitar rai ne daga jikinsa, kai ya girgiza ya koma ya zauna.
“Ba zan iya ba, wata kila ka fada min haka ne saboda ku cin ma burinku a kaina�
Kakan yayi murmushi.
“Lallai kana sonta sosai tun da har ka iya karyata ni, amman bari mu gani daga nan zuwa jibi idanuwanta za su bude ne ko kuwa za su tabbata har a bada a rufe? Amman ka sani daga lokacin ni da kai babu abun da zamu iya yi domin dawowa da idanuwanta....�
HAJIYA BABBA POV.
“Amin wa'alaikissalam�
Ta amsa sallamar da Hajiya Zariya tai mata a yayinda ta kara kunnen a wayarta.
“Hajiya ina yini ya gida ya Mai Martaba da jikin�
“Alhamdulillahi�
Ta amsa cike da kasaita kamar ba yar'uwarta ba.
“Hajiya na ce ko Sirleem yayi aure ne ba a fada mana ba�
“Wane Sirleem kuma?�
“Sirleem dai na ki, na wuce ne jiya ta gaban gidansa da yake nan kusa da mu na ga mutane na fitowa na tambaya aka ce min walima ake wai Amarya aka kawo, shi ne abun ya ba ni mamaki na ce to ko anyi bikin ne ba a sanar mana ba�
Hajiya Babba ta aje farantin dankalin jos dake hannunta.
“Aa ai ke ma kin san ba zai yiyu ba, Sirleem yai aure ba ki sani ba, ko da ba a fada miki ba ai duk garin nan sai ya dauka, shi kadai ya rage min fa namiji, kuma aurensa da yar sarautar ai dole ne ma duniya ta sani�
“Ni kaina na yi mamaki, tun jiya abun ya tsaya min a rai ina ta son na kira dai ban samu dama ba, mutanen ma da na ga suna fitowa daga gidan ba wasu na azo a gani ba ne, ko dai haya ya bada gidan ne?�
“No gidansa da ke kusa da unguwarku ai yafi ko wane gida nasa kyau da tsaruwa, ba zai bada hayarsa ba, kuma bana jin zai arawa wani, Amman kin shiga cikin gidan kuwa?�
“Aa wannan dabarar bata zo min ba, ban yi wannan tunanin ba�
Shiru Hajiya Babba tai tana nazari.
“Zan bincike shi idan ya shigo�
“To Hajiya sai an jima a gaishe da su Kausar�
“Za su ji�
Hajiya ta sauke wayar cikin tsananin mamaki, anya ma kuwa gidan ne? Ta tambayi kanta sai dai bata jin Hajiyar Zariya za tai kuren fahimta domin ta san gidan ba ita kadai ba ma yawancin mutanen unguwar sun shaida gidan saboda tsaruwarsa gashi farin gida mai bakin gate sai daukar hankali, sai dai ba kowa ya san cewa na Sirleem ba ne sai daidaikun mutane yan'uwa da kuma wadanda suke kusa da shi sosai.
Tunawa da tai da zancen da yai mata shekaranjiya na cewar zai kwana a can saboda baya jin dadi da kuma jiya da yace mata yana son komawa can so that ya samu damar maida hankali kan harkokinsa yasa gabanta mugun faduwa. Har ta dauko wayarta ta kira shi sai kuma wata zuciyar ta hana ta, da sauri ta mike tsaye ta nufi inda mayafanta suke ta dauko farin gyale ta saka ta nufo gurin da aka jekara takalminta ta saka ta dauki jakarta tare da wayarta ta fito falo.
“Juwairiyya�
“Jurry bata nan�
Karima ta amsa.
“Ke tashi ki kai ni gidan Sirleem da ke 300 houses yanzu nan�
“Okay, amman Hajiya lafiya?"
“Ita na ke son na tabbatar�
Ganin yadda hankalin mahaifiyarta yake a tashe yasa tai saurin dauko mayafinta ta fito rike da makullin motarta, har suka saukon ta shiga motar mamakin abun da ya faru take, ko dai minene ta san abu ne da yake son sirri shiyasa ta zabi ta kaita a maimakon direbobinsu da suke gidan.
Suna isa unguwar Hajiya ta saka tai bakin nesa da gidan sannan suka fito suka taka da kafa har gaban gidan, Karima ta kwankwasa gate din sai mai gadin ya leko. Karima za tai magana Hajiya ta tari numfashinta
“Amarya na nan?�
“Eh suna nan Hajiya Bismillah ku�
Ya bude musu gate din, suka shiga ciki hango motar Sirleem da Hajiya tai ya fi komai kayar mata da gaba, Rima kam tana gefenta da mamakin jin abun da Hajiya ta fada, suka nufi hanyar shiga falon zuciyar Hajiya sai bugawa take kamar zata fasa kirjinta ta fito, sai da ta fara tura kofar ta ji ta a rufe bata ko tsaya duba inda door bell din yake ba ta kwankwasa. Jin shiru ba a bude ba yasa ta sake kwankwasawa. Sirleem ne ya bude kofar yana sanye da jallabiya milk color.
“Hajiya....�
Ya fada kamar wanda ya rude. Tura kofar falon tai ta wuce ciki falon, sai tai arba da abun da bata yi zato ba, wato Falmata tana sanye da doguwar rigar atamfa hannunta rike da dankwali, daga bakin Hajiya har hancinta da idonta kallon Falmata yake with shock, can kuma ta juyo ta kalli Sirleem baki sake ta nuna shi da yatsa, sai kuma ta kasa magana, ta sake juyowa ta kalli Falmata ta daka mata tsawa idonta na cika da kwalla.
“Me kike yi a nan?�
Falmata ta kasa cewa komai jikinta sai rawa yake, Sirleem yayi saurin nufar inda take yana kallon Hajiya.
“Sirleemmmmmm.....�
Hajiya ta kira sunansa daker sannan ta ce
“Dadiro kuke yi?�
“No Hajiya Subhanallahi, she's my wife�
Wife wife wife wife wife wife wife wife wife.... Haka kalmar tai ta maimaita kanta a kunnen Hajiya, nuna shi tai ta nuna Falmata sai kuma ta nuna kanta kamin ta fadi kasa zaune saman tile din. Sirleem na ganin haka yai saurin kama hannun Falmata suka fice daga falon cikin sauri, motarsa ya nufa da ita Rima ta bi su da kallon mamaki ido bude. Sai da ya taba motar ya ji a rufe, sai ya rasa yadda zai yi baya son komawa ciki saboda zuciyarsa na raya masa Hajiya zata iya cewa sai ya sak Falmata a take. Hannunta ya kama be ko kula da dankwalinta dake hannunta ba suka fice daga gidan gaba daya, Falmata kuka kawai take jikinta na rawa kamar mazari. Suna fita su kai sa'a da Napep, cikin sauri Sirleem ya tare Napep din dake tare da wata mata suka shiga, yana fada masa inda zai kaisu.
Sai da suka bar unguwar sannan Falmata ta lulluba dankwalin da ke kanta, mai Napep kam sai mamakin wanda ya dauko yake a zahiri dai fuskar Sirleem yake gani fitaccen mawaki sai dai ba shi da tabbacin shi din ne ko waninsa. A gaban gidan Momy ya sauke su Sirleem ya fito yana fadin.
“Jira ni ina fitowa�
Ya buga gate din gidan mai gadin na budewa yaja hannun Falmata suka shiga ciki, yana isa bakin kofar falon Momy ya buga kofar da mugun karfi, hakan yasa Momy tai saurin budewa hankali tashe. Ganin Sirleem da Falmata ya bata mugun mamaki.
“Sirleem�
“Momy dan Allah ki boye min yarinyar�
“Lafiya?�
“Dan Allah ki boye min ita yanzu yanzu, zan dawo ki saka a daki ki kulle dan Allah kowa ya zo karki fito da ita�
Momy ta nuna Falmata da mamaki.
“Wannan ba Falmata ba ce?�
“Ita ce Momy please ki boye min ita�
Ya fada cikin tashin hankali, saurin kama hannun Falmata tai ta shiga da ita ciki shi kuma ya juya ya koma, upstairs Momy ta nufa da Falmata da ke kuka ta bude dakin Ameer ta saka ta ciki ta rufe ta makulli ta sauko kasa da mamaki kala kala.
Bakin kofar dakin Falmata ta zauna ta fashe da wani irin kuka marar misaltuwa, sai ta ji kamar bata taba fuskantar tashin hankali irin wannan ba, kuka take sosai tun tana yi ba sauti har sautinta ya fara fitowa, kuka tai bana wasa ba har sai da idanuwanta suka fara kumbura, hawayen suka daina zubo mata. Mikewa tai tsaye tana goge idonta da dankwalinta, kamar ance mata juyo ki kalli gefe, tana juyowa sai tai arba da wani tsohon hoton mahaifiyarta, an fadadashi har ya kusan tsawonta, an ajeshi a tsaye yana fuskantarsa, mutuwar tsaye tai tana kallon hoton with shock.