← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 172

Sashe 125

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Tun farko ita ya kamata ace na fara kamawa, da yanzu bata samu damar yin wannan abun ba, na yanzu tana can kwance tana jinya kamar mijinta, amman saboda na kyale ta har ta samu damar yi min haka? Ta tona min asiri a cikin Masarautar nan?�

Ta mike tsaye tana jin kamar ana sukanta a zaunen da take.

“Ko da yake ba laifin Ammy ne kadai ba, har da laifin yarinyar nan Fadime? Amman na san maganin abun�

Ta fada zuciyarta na raya mata ta yanke kurwar Maijidda tun a yanzu ba sai biki ya matso ba ko kuma an yi aure kamar yadda take yi ma sauran, domin idan tai tun a yanzu babu wanda zai zargeta kuma hankalin Ammy zai koma a can, sannan bata san abun da aka shirya mata ba a nan gaba.

FADIME POV.

Wata hadimar ce ta shigo falon da su Bappa suke tana sinne kai kasa ta ce.

“Shattima ya turo na tafi da Fadime idan kun kallama�

“Ki tafi da ita ina zaki kaita?�

Bappa ya tambaya, kamin hadimar ta amsa Fadime ta mike tsaye tana fadin.

“Cikin gida can gurin matar sarkin, ai a can nake zaune�

“To yayi kyau, kuma idan kin je ki yi musu shirme da kika saba, Wallahi ki kwantar da hankali ki san irin abubuwan da zaki fada ko ki yi, kina yin wasa Wallahi za su daure ki, kuma Wallahi kin dauro har abada, dan sarki babu ruwansa da makantarki�

“Bappa wai sarki ne babba?�

Fadime ta tambaya jin yadda Bappa yake tsoratata.

“Sarki ne babba, garin Yola fa gaba daya, kamar ace sarkin Katsina�

Ta zaro ido tana jin wani irin kimar Shattima da kwarjininsa suna kankwaro mata, sai a yanzu ta gane ya sarautarsu ta ci uban ta su Wasim da take gani da girma, sai a yanzu ta gane dalilin da ya saka baya son yawan magana kuma yake dadewa kamin ya bata amsa wani lokaci.
Ta mika hannunta ta inda take zaton hadimar na gefen.

“Mu tafi�

Hadimar ta kama hannunta suka fice daga falon Bappa sai nanata mata yake ta bi a hankali da yaren fulatanci. Suna tafiya Fadime na tuna abubuwan da suka faru tsakaninta da Shattima, ita ma ai ya kamata ta gane babbar Sarauta ce tun daga jin gidan sama da suke da kuma yadda suke da yawan hadimai, kuma ga sanyi ac da kayan dadi a ko'ina.
Har cikin fadar Ammy Hadimar ta shiga ta ita sannan ta saki hannunta.

“Ina za ki je?�

Bata samu damar amsa mata ba sakamakon hannun da Shattima ya daga mata sai tai saurin ficewa ta tare da tace da Fadime komai ba.

“Ke ina kika kawo ni�

“Wani guri�

Ta ji muryar Shattima daf da ita, shiru tai kamar ba ita ba tana jin girmasan da kwarjininsa na kamata, sai ta ji ta kamar yar wata kudan zuma a wata duniyar babbar duniya, gabanta ya shiga bugawa da karfi abun da bata saba ba.

“Kin ga Babanki?�

“Eh Ranka ya dade�

Ya wara yana murmushi.

“Ni ne ranka ya dade a yau kuma?�

“Dan Allah ka yi hakuri da duk abubuwan da na yi maka�

Ya juyo da ita tana fuskantarsa duk da kasancewar bata ganinsa.

“Me kika min?�

“Abubuwa da yawa ba za su kirgu ba�

“Baki min komai ba, na san ai ba ki san komai ba, kuma ko kin sani rayuwarki ki simple ba lallai ne komai ya burge ki ba�

Shiru tai ta natsu sosai tana saurarensa kamar ba ita ba.

“Ina son nai miki sallama ne, na siya muku ticket jirginku zai tashi 7am ba lallai ne na shigo gida kamin lokacin ba, so i wanted to say goodbye�

Ta yi shiru tana wani abu na rashin jindadi yana ziyartarta duk da kasancewar tana son gida kuma tana son kasancewa tare da Bappa da Inna da kauyenta, sai dai a yanzu da Shattima yai mata wannan maganar sai ta ji kewarsa da dan sabon da tai tare da Nana ga dadin da take ci kullum.

“Ranka ya dade, yanzu shikenan ba zan sake ganinka ba?�

Ya lakace hancinta yana murmushi.

“Daman kin gan ni ne?�

“Ina nufi ba zan sake jin muryarka ba?�

“Yes ni ma ba zan sake ganinki ba, zai je ki cigaba da rayuwarki kamar yadda kika saba, kuma i hope idonki zai bude soon i mean very soon�

Ta kasa cewa komai sai saurarensa take tana jin kamar ta fashe da kuka. Ya cire agogon hannunsa ya kama hannunta ya saka mata.

“Ga wannan ki rika tunawa da ni, ban taba haduwar da macen da na ji bana son rabuwa da ita ba irinki, tun a ganin farko da na yi miki a Katsina kika kwanta min a rai, to be frank komai na ki yana burgeni i like you�

Ya fada yana kallon cikin idonta dake cike da kwalla. Ya dade yana kallonta kamin ya kai bakinsa saitin kunnenta ya rada mata.

“Bye Allah ya tsare hanya�

Lumshe ido tai hawayen idonta suka sauko, kashe kunne tai tana sauraren sawun kafarsa har ya fice daga falon, sai ta rage tsawonta ta zauna a gurin ta share hawayen da bata san dalilin zubarsu ba. After like 5 min ta ji sallamar Jekadiya ta shigo gurin sannan ta kama hannunta.

“Ta so mu je yace za ki yi ma Ammy sallama, sai na maida ke daki�

Fadime ta mike tsaye tana jin kamar a barta tai ta zama a gidan duk bata iya shaidar fuskar kowa a gidan saboda bata gani. Babu abunda take sai saurare har suka isa dakin Ammy, tana Jekadiya ta rage tsawo ita ma ta rage ta zauna kasa.

“Ammy Shattima ne ya ce na kawo ta ta yi muku sallama�

Ammy dake kishimgide ta dago tana dubanta tare da cire gilashin idonta tana murmushi.

“Yarinyar mai abun al'ajabi, ki zo mana da abubuwa zuwanki ya zama mana alheri, yaushe za ku tafi?�

“Gobe ya ce, da karfe bakwai za mu hau jirgin sama�

“Yayi kyau Allah ya tsare hanya, kamin ku tafi Jekadiya zata ba ki tsabarki�

“Na gode ranki ya dade Allah ya saka da alheri�

“Godiya take, godiya take Ammy Allah kara miki lafiya�

Jekadiya ta fada da dariya sannan ta sake rikon hannun Fadime suka fito daga dakin. Dakin Nana ta sake maida ita, dakin da take komai a ciki wanka abinci canja tufafi duk a dakin take, Nana ta bata kusan kala biyar duka sabon kaya da zata rika canjawa idan ta yi wanka.
A dakin ta wuni, abincin ta na dare ma a dakin aka kawo mata, sai dai bata wani ci da yawa ba, kadan ta ci ta bar sauran, ta tashi da kanta ta shiga bandaki ba tare da ta yi addu'a ba, daman can addu'a bata dame ta ba, tana tura kofar bandakin ta shiga sai ta ji wani irin iska da yanayi kamar ba a bandaki ba, juyowa tai ta zimmar fitowa sai ta ji ta taka abu kamar titi juyowa ta sake yi ta taka gaba sai ta sake jin abun, ta kara yin baya sai ta sake jin abun. Can kuma ta ji wani irin kara ya cika mata kunne gashi bata ganin komai sai duhu, tsaye tai a gurin kamar an dasata. tana ta sauraren karar da bata san ko na minene ba, sai dai tana jin sautin kamar ya mata yawa a kunne, can ta soma jin sautin bugun wani abu kamin ta fara jin sautin muryar mace.

“Lalalala...lafiya ...kika tsaya a tsakiyar titi?�

“Titi�

Fadime ta maimaita tana juyo ta inda take jin sautin muryar matar, kamin matar ta sake magana mijinta ya karaso ya jata ya maida bayansa da dayan hannunsa yayinda dayan yake rike da jariri.

“A ina nake?�

Ta tambaya tana jin kamar ta taba jin abun da ake kira da titi. Matar ta kalli mijinta mijin ma ya kalleta.

“Bana ganin komai sai duhu dan Allah a ina nake?�

Fadime ta sake tambaya, sai matar ta waiga tana karewa unguwar dake cike da haske a ko'ina kamar ba dare ba.

“Daga ina kika zo nan? Waya kawo ki nan?�

“Ni ma ban sani ba, ban sani ba�

Ta fada hawaye na sauko mata.

“Ya sunanki?�

“Ban sani ba, ya sunana to?�

Ta dafe kai.

“Miyasa na ake jin kaina kamar ba komai ciki? Miyasa bana ganin komai sai duhu a ina nake?�

Ta fashe da kuka ta durshe a gurin. Matar ta kalli mijinta cike da tausayi.

“We need to help her�

Wani kallo yai mata na mamaki, kana ganinsa kasan irin miskilan mazan nan ne da magana ke musu wahala.

“Aliyu bana son na ga mutum a cikin damuwa ban taimaka masa ba, na san yadda ake ji, ni ma babu irin wahalar da ban sha ba kamin rayuwa ta kawo ni a nan, har bara na yi, ko ka manta? Babu irin wahalar da ban yi ba babu irin wulakancin da ban gani ba, bana son na ga wani a cikin damuwa na kasa taimaka masa�

Dauke kai Aliyu yai ko kadan baya son tunawa da halin da matarsa ta shiga a baya, domin har yanzu yana ganin shi ne silar komai saboda dashen kodar mahaifiyarta da akai ma matarsa uwargidansa, his late wife Rahma.

“Fine idan kuma ba mutum ba ce ba? Ataa think please�

Ya fada kamar ana matso maganar daga bakinsa.

“Daga gani mutum ce, aljana ta yi wuri ta fito mana haka, ko isha'i fa ba a gama ba wani gurin, idan mu ka tafi muka bar ta nan zata sha wahala kamin ta samu taimako, ka san unguwar nan fa kowa na cikin gidansa, kamin ka ga wulgawar mota ma aiki ne, ko ma dai wacece mu da zuciya daya zamu yi mata taimako, Allah ba zai bata ikon cutar da mu ba�

Kallonta kawai yake yana gyara takwaransa dake kafadarsa. Sai ta saka hannayenta biyu ta rike kunnenta.

“Please Hamma na....�

Uffan be ce mata ba, daman can kowa ya san Aliyu ya san magana ma wahala take masa, juyawa yai ya koma gurin motar ya bude mata back seat alamar ya aminta kenan.

“Yauwa dan wajen Mama Fulani i love you�
Chapter 125 · 0% Book details