Sashe 33
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da tunani kala biyu Falmata ta isa gida, tunanin saukin kai da jindadin kadeta da M2 yai ga kuma kiranta da Ammy tai ta mata tambayoyi, ko miyasa tai mata haka oho. Sosai ta so ta biya ta gidansu kawarta Khadija ta labarta mata yadda ta ga M2 sai ta tuna da Baba ya mata iyaka da gidan. Hakan yasa tai hanzarin cira kafa ta isa gida, da zimmar ta gama aikinta dan ta samu isa Islamiya da wuri ta labarta musu. Ko da ta isa gida har Gambo ta sanar da sakon Ammy ta bar gidan dan ita abun hawa ta hau ba kamar Falmata ba da take tafiya a kafa.
Falmata na isa ta manta da wani kunci da tsoron fada ko wani abu, ta hau bawa Naja labarin yadda ta ga M2.
“Dan Allah matsa can mahaukaciya, hala M2 ne banza da zaki ganshi a bagas, sannu kakar farin jini, dan kin ji ana cewa kina da farinjini shine kike wani karya kin ga M2 mahaukaciya�
Ko kadan bata ji abun da Naja ta fada ba, amman a yanayin yadda take harararta take jan tsaki tasan karyarta tayi, hakan yasa Falmata ta kara boye hular da ya bata a cikin jikinta ta mike tsaye cikin rashin jindadi ta nufi dakinsu. Tumba dake zaune bakin kofar dakinta ta bushe da dariya.
“Wallahi yarinyar can ta fara haukacewa, mugun son M2 da take ne yasa ta fara ganin mutane na zame mata haka�
Naja ta ja tsaki.
“Ko mai wankewa M2 takalmi ta isa ta gani balle M2, ita fa yadda ake fadar tana da farin jinin nan wani jin kanta take�
“Kira min ita�
Tumba ta fada tana dariya, daga inda Naja take zaune ta kwala mata kira.
“Ke kurma zo ana kiranki�
Falmata har cikin ranta ta ji sunan, wani abu na rashin jindadi ya ratsa zuciyarta, ta saka hular M2 can ciki bakkon kayanta sannan ta fito ta tsaya bakin kofa jiki ba gwari tun da babu wani abincin kirki a ciki.
“Ke yar kurma, dazun Gambo ta zo tace zaki rika wuni can kina rainon yara�
Tumba ta fada mata tana mata alama irin na kurame. Naja ta saka dariya.
“Ban cin kurmanta har da hauka na son kamaki, kin fara ganin mutane kina ce musu M2 ko?�
A nan ma Tumba ta saka mata dariya, a gurin Falmata ta duka ta fashe da kuka, ba karyatata da suke take ji ma ciwo ba, kiran da kurma da suke a yanzu.
“Ji munafuka salon a shigo ace wani abu Umma tai miki kike kuka mu kuke dariya ko? Da shegen baki kamar zunubi�
Naja ta fada cikin tsawa, sai Falmata ta mike tsaye ta shige dakinsu ta cigaba da kuka tana rufe bakinta dan kar sautin kukanta ya fito.
Sai da tai mai isarta sannan ta fito ta zuba surfe ta fara, sai da ta surfe tiya da rabi sannan ta shiga tai wanka ta saka uniform dinta na Islamiya ta dauko qur'ane ta da littafai ta fice.
Kusan kullum cikin rashin jindadi taje zuwa makaranta, saboda rashin jin da take a yanzu, idan akai karatu sai Khadija ko wata ta rada mata abun da Malam ya fada a kunne sannan ta ji, sai kuma idan Malamin yayi da karfi, Falmata ba yarinya ce mai yawan surutu ba, amman hakan be hanata fadawa yan ajin su cewar ta hadu da M2 ba, most of them sun karyatata wasu na fadin dan dai tana son shi sosai ne yasa ta ga mai kama da shi.
Haka dai ta bar Islamiya cikin rashin jindadin yadda suka karyarta daman ta san ba za su yarda ba, ita ma dai a lokacin ta fara kwankwanto da gaske M2 ta gani ko mai kama da shi?
Ko da ta iso gida sai ta tararda wani tashin hankali, yaron da aka aiko yana tsaye yana jiran dawowarta Tumba kuma ta yi wani shegen zama tana rawa da kafa. Ta shigo da sallama Tumba ta hau ta da matsifa.
“Ashe Falmata zuwa kike kina cin bashin garin kwaki a shago da sunana?�
Dakan shida-shida gabana yai, ta sani yau asirinta ya tonu, tabbas tana zuwa karba kuma idan ta je Tumba take cewa saboda tana jin kunyar tace ita zai bawa bashin gari.
“Saboda asan ba a baki abinci ko kuma dan ki bata min suna ni da ubanki? To ya aiko yace a bashi kudinshi bari ubanki ya dawo sai kin fadi dalilinki na bata min suna�
Kamar an tureta haka ta fadi gaban Tumba kamar mai neman gafara hawaye sai sallama suke a fuskarta.
“Dan Allah dan darajar Annabi karki fadawa Baba Umma, ki rufa min asiri, zan samu kudinsa yanzu na bashi, ki yi hakuri Umma ba zan, idan na sake ki kashe ni, Umma wallahi yunwa take damuna shiyasa na ci bashin amman daga yanzu ko zan mutu ba zan sake ba, na rantse da Allah Umma, dan manzon Rahama ki rufa min asiri Umma ba zan sake ba har abada�
Tumba ta fisge kafarta tana kallon.
“Tafi idan Babanta ya dawo za a fada masa�
Yaron ya juya ya fice, sai Falmata ta mike tsaye da sauri.
“Na bani na lalace na shiga uku wayyo ni Allah na Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un�
Ta furta ta karfi kuka na subuce mata, sai ta saka hannunta da sauri ta rufe bakinta, da gudu ta shiga dakinsu ta fada kan shimfidar da take kwana.
“Wayyo ni Allah na yau asiri na ya bonu, wayyo Mama Mama ina ma ni na mutu ba ke ba, Allah ka karbi raina kamin Baba ya dawo Allah na shiga uku�
Ta fada tana yarfe hannunta hawaye sai zubo mata suke kamar ba gobe.
ZAINAB POV.
Ta dan yi shiru sannan tace.
“Na ce mishi ya bari har na dawo daga tafiyar da zan yi�
Ammy ta kalleta.
“Ni fa ina tsoron lafiyar nan Zainab, kin san kasar ba wani tsoro kuma ki ce za ki je garin cikin mutanen da ake fadar basa saka tufafi? Kina ganin ma za su aminta ki dauke su hoto ne?�
“No ba wai kai tsaye zanje can ba, zan sauka garin dake kusa da su ne, nai magana da mutanen tukuna sai na isa garin, kuma ko ban samu zuwa can ba ai ance akwai manyan duwatsu a kusa da su da ruwa, kuma ance akwai Fulani irin masu yin bukka da gidan zana su zauna a kusa da su, ko da ban samu isa can ba na san ba zan sara abun dauka ba�
“To Allah dai ya tsare�
“Amin, Ammy dan Allah ki mata magana, ban zan abun da mutunen nan yai mata ba, ta ki ta saurare ni, ni kuma ina son shi, shi yanzu yace yana son ya turo kuma ya sanar a gidansu amman sai ya samu tabbaci daga gareni�
Ammy ta yi murmushi.
“Karki samu damuwa, zan yi magana da ita, idan ta aminta sai a sanarwa yan'uwan mahaifinki�
“Na gode Ammy�
Mikewa tai tsaye tana sanye da riga da wando English wears, kanta sanye da dankwalin nan da ake yayi blue.
“Bari na duba dakinta idan tana nan sai na turo miki ita�
Kai kawai Ammy ta daga mata, ta maida dubanta gurin tv dake dakinta, kallon kawai take amman hankalinta baya can, bata da damuwar da ta wuce ta Mai Martaba a yanzu, a iya tunaninta ta rasa gane abun da yake damunsa, gashi idan an gwada yi masa na hausa sai abu ya karu a maimakon raguwa. Kiran wayarta nd ya katse mata tunanin da take, sai ta mika hannu ta dauka.
“Assalamu Alaikum�
Ra'ees ya amsa daga dayan bangaren.
“Wa'alaiki-Assalam, Ammy barka da yamma�
“Yauwa Ra'ees ya gida�
Ta fada cike da kasaitar da ta zame mata jiki.
“Al-hamdulillah Ammy an samu wata, amman dai ba mu je, sai dai marikiyar yarinyar tace zata iya aura masa ita�
“Ka fada mata matsalar sa ne?�
“Eh ta ji komai, firar ma ta ji muna yi shine tace tana da ƴa zata ba shi, amman dai ba mu je ba tukuna�
“To yayi kyau, amman fa ba sai kun bayyana dan wane ba, kuma ka yi duk abun da ya dace, karka bari Shattima ya ji komai, sai an kammala yadda ba zai iya ce mana aa ba�
“In-Sha-Allah Ammy�
“Na gode Allah ya maka albarka�
“Ameen�
Tana kokarin aje wayar aka kwankwaso kofar dakin kamin a turo a shigo. Hajiya Balki ce Nana na biye da ita a baya, a baki kofa ta tsaya tana kallon Ammy sai cika take tana batsewa.
“Yanzu an kyauta kenan? Sai a dauke yarinya akaita gurin Waziri bayan kin san ita da Waziri ba jituwa suke ba?�
Ammy ta kalleta da mamaki kamar ba zata ce komai ba.
“An kaita gidan Waziri kamar wacce aka kai gidan yari? Kanen ubanta ne fa�
“Na san kanen ubanta ne ai, amman tun da bata son zuwa ai sai a kyaleta�
Ammy ta dauke kai bata sake ce mata komai ba. Ganin hakan yasa ta juya ta fita Nana kuma ta zauna saman kujera tana matsar yatsun hannunta tana kallon Ammy. Ko da wasa Ammy bata kalle inda take ba har ta gaji dan kanta tace.
“I'm sorry�
Ammy ta watsa mata wani mugun harara.
“Dakinki dai kike so ko? To gashi can idan kin mutu a haka rame a saka ki a ciki, tashi ki fata�
“Ammy ki yi hakuri....�
Bata karasa ba Ammy ta daka mata tsawa.
“Get out�
Ba shiri ta mike tsaye jikinta na rawa ta fice daga dakin tana fashewa da kuka.
_________________
Al-hamdulillah, a nan na kawo karshen free pages, duk mai son cigaban wannan labarin ya biya 300. Pages din da za su biyo bayan wannan na kudi ne ba kyauta ba, ko kun ganshi a waje na sata ne.
Patronize me if ku masoyana ne na gaskiya, show me that love.
Son so Fisabilillah.
*FULANI -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence to 08036126660 Æ´an nijar za ku tura 500cf to +22790165991*