Sashe 15
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya sinne kai kasa, ya kasa cewa komai gabansa sai bugawa yake da karfi. Wata irin tsawa ta daka masa rai bace
“Waye miye hadin Bayarabiya da bafullatani ne Sirleem? Me ta baka ka sha da baka iya rabuwa da ita? Ni uwarka ban isa na ce ka fita hanyar Mansura ka fita ba? Me yake damunka ne?�
Dagowa yai ya kalleta cike da ladabi ya ce.
“Hajiya ba fa cewa nai zan auri Mansura ba, Mansura kawata ce kawai, i think Nana kike so na aura ai�
“Yes wannan kuma dole ne, auren Nana ya zame maka wajibi matukar ina raye, yaushe rabon da ka je ka dauki Nana ku fita ko na kira a waya? Amman ka zauna kana video call da wata yar iskar yarinya marar tarbiya, kuma a cikin falona�
Cikin wata kalar murya dake nuna bacin ranta ta karashe maganar tana nuna shi da yatsanta da ke rawa kamar zata doke shi.
“I'm sorry�
Shine abunda ya fada ya mike tsaye ya dauki system dinsa ya fice daga falon. Zaunawa tai saman kujerar tana kokarin daidaita fushinta.
AMMY POV.
Bayan Waziri ya gama zayyana mata komai, sai ta amsa masa da.
“Okay babu wata matsalar zan saka Shattima ko Jarma ya wakilce shi tun da kai ba zaka samu zuwa ba�
“Jarman ma yafi dacewa tun da shine Dattijo kuma kin ga abu ne na manyan mutane�
“To sai a yi ma Jarma magana da wuri ya shirya komai kamin lokacin�
“Zan sanar da shi�
Waziri ya fada yana karantar yanayin matar dan'uwan nasa. Har ya mike tsaye da zimmar yai mata sallama ya fice sai kuma ya koma ya zauna ya kalleta.
“Hajiya ko dai akwai wata matsalar ne?�
Ammy ta sauke ajiyar zuciya, daga inda take zaune ta saka hannunta na dama ta rike kanta, a take idonta ya cika da hawaye abun ka da mai neman kuka an fada masa mutuwa.
“Ina cikin damuwa Waziri, na rasa da wanne zan ji, matsalar Nana ko ta Mai Martaba ko kuma ta maganganun da suke tasowa a masautar nan?�
“Matsalar Mai Martaba tana damun kowa, addu'a yake bukata da kuma kulawa, gulma kuma ta daina damunki daman duk daukaka ta gaji haka, za ka samu akwai hassada da kiyayya da kananan maganganu, sai dai Nana nake son na ji abunda ya same ta?�
“Abubuwan da take min bana jindadinsu, tun jiya take damuna da zancen sai an canja mata driver yau da safe har tsawa ta daka min akan haka, taya yarinyar da ke neman albarka za ta yi ma mahaifiyarta haka? Yanzu kuma na duba drawer dubu dari uku da saba'in na aje a ciki yanzu na duba na ga babu kudin sai dubu talatin da biyu suka rage, abubuwan da Nana take suna tsorata, kuma suna damuna, ba a nan kadai ba Nana ko dakin Mai Martaba ta shiga indai idonta ya ga kudi sai ta saka yadda tai ta dauke su, ina tsoron kar wannan abun ya zame mata hali, ga shi bata da natsuwa duk wani abu na masu hankali Nana ba ta yinsa....�
Ta karasa hawaye na sauko mata, ba dan komai ta tsaya ta fada ma Waziri damuwarta akan Nana ba sai dan sanin shi ne kadai mutumen da zai tsawatarwa Nana ta ji kuma shine mutumen da idan ta fada masa damuwarta ko damuwar Masarautar nan yake fadi tashin ganin ya same mata mafita.
Waziri ya kankance ido irin na su na manya yana mamaki.
“Me take yi da kudin da take dauka?�
“Wallahi ban sani ba, amman kai kanka kasan babu abunda Nana ta nema ta rasa�
“Zan daukar mata mataki kuwa, amman duk da haka ki rika gamawa da addu'a ta tsari da kuma ta shiriya�
Sosai Ammy ta jidadin maganar Waziri domin tana ji a ranta kamar ba zata iya da Nana ita kadai ba. Har ta bude baki ta yi magana sai ta Yusra ta shigo dakin da gudu har tana haki.
“Ammy Nana ta fadi ta ji ciwo gata can an kawo ta....�
Tun kan ta karasa Ammy ta mike tsaye hankalinta a tashe ita da Waziri suka fita daga dakin. A kwance suka samu Nana saman gadonta an saka mata bandeji a kanta da kafarta da hannu, Shattima na tsaye tare da Hajiya Karama, Driver ba kuma yana daga bayansu jikinsa sai rawa yake. Da sauri Ammy ta zauna saman gadon ta taba jikinta.
“Me ya same ki Nana?�
Ta kalli Shattima da Hajiya Karama, sannan ta kalli Ammy, ko da wasa bata kalli Waziri ba domin yadda take tsoronsa ko mutuwarta albarka.
“Mai Babur ya kade ni, na fito daga school ina jiran Driver ya zo ya dauke ni be zo ba har babur ya kade ni, sai wani ya kai ni asibiti aka saka min wannan shi ne ya kawo ni nan ma da motarsa�
Nana na fadar hakan driver ya risina kasa yana rokon Ammy.
“Hajiya dan Allah dan Annabi amin afuwa, uzuri ne ya rike ni shiyasa ban samu isa da wuri ba�
Ammy bata ce komai ba sai duba jikin yarta take cike da damuwa.
“You fired, saboda ita aka dauke ka aiki, then why all this? Har mai babur ya kade ta ta ji ciwo wani dabam ya kawo ta gida�
Zainab ta fadawa driver, a take ya fara magiya yana kallon Ammy.
“An kore ka aka ce fita ka bar dakin nan�
Ganin Ammy za ta yi magana yasa Shattima ya nanata masa abunda Zainab ta fada domin abunda yake da niyar yi kenan, cikin rashin dadin rai driver ya fice daga dakin fuskarsa kamar zai fashe da kuka.
“Me kike son ki ci? I will cook for you�
Ammy ta tambaye ta cike da kulawa, sai Nana ta kawardar fuska ita aka dole har yanzu fushi take da Ammy.
“Bana son komai�
Ammy ta hade abu da karfi sannan ta mike tsaye ta nufi kofar fita sai kuma ta juyo ta kalleta fuskarta da mamaki.
“Amman ya akao kika fito ba lokacin tashi daga school ba? Ya akai suka bar ki kika fito? Yanzu fa karfe 11:40am how?�
Shattima ya kalleta.
“Ammy za mu yi wannan maganar daga baya yanzu dai ta samu lafiya�
Ammy bata sake cewa komai ba ta juya ta fice. Sai a lokacin ne Waziri yai magana.
“An kori direban ko? To kin samu abunda kike so idan ma ke kika tsara haka saboda a kore shi burinki ya cika, amman bari na fada miki daga yau school bus ce zata rika kai ki makaranta tana dauko ki, ba ki wayar ki�
Ya mika mata hannunsa sai tai saurin kallon Shattima tana son saka kuka, kai ya gyada mata alamar ta ba shi din, sannan ta kai hannu ta bude school bag dinta ta dauko wayar ta mika masa tana hawaye. Shattima ya zauna kusa da ita kenan Waziri ya ce.
“Daga yau kar wanda ya sake daukar kudi ya bata ko ya siya mata waya, daga kai har Zainab shi ma Sirleem zan masa magana�
Da mamaki Zainab ta kalleshi sai dai babu damar tambayarsa dalilin hakan dan ta fi kowa sanin waye Waziri.
“Zainab je ki kira Baaba ta zo ta bincike dakin nan duk inda kudi suke ta fito min da su, kuma ta kwashe kayan kallon nan da system din nan bana son ganinsu a nan�
Ta amsa masa ta to, sai da ta kalli Shattima sannan ta fice zuciyarta cike da tambayoyi. Waziri ya kalli Nana.
“Da kin ji sauki ke za ki fara gyara dakinki da kanki, ba za a sake miki ba, ko tufafin da ke saka miki a wardrobe daga yau ke zaki saka idan sun yi datti ki wanke da kanki�
Ta kankame Shattima tana fashewa da kuka.
“Wayyo Yaya mutuwa zan yi�
“Kin dade baki mutu ba�
Waziri ya daka mata tsawa yana matsowa kamar zai doke ta, da sauri Shattima ya mike tsaye ya tare ta.
“Ayi hakuri Baba zan mata magana�
Shi kan shi Shattima sai da Waziri ya watsa masa harara sannan ya fice daga dakin, wanda hakan yayi daidai da shigowar Baaba, a take ta hau aikinta sai da ta bincike dakin tsab ta fiddo kudi ba kanana ba har da dollars din da Nana take daukowa dakin Mai Martaba ta fito falo ta kawowa Waziri sannan ta kira Sarkin Dogarai ya cire tv da decoder da system din dake dakin. Nana na ji na gani aka kwashe kayan aka bar mata daki wayan daga gadonta sai wardrobe da dan karamin dinning dinta na karatu domin har hotunan artists da saka sai da Waziri ya saka aka cire su a lokacin da ya sake dawowa dakin dan ganin idan an yi yadda ya ce.
“Yaya Wallahi Baba Waziri da Ammy basa so na�
“Shiiiiiiiiii kar na sake jin wannan kwanta ki yi bachi idan kin tashi zan kira Doc Deen ya duba ki Okay�
Ya daga masa kai sannan ya mike tsaye ya fice daga dakin. Tai saman gadon ta fara kuka na gasken gaske tana jin kewar mhaifinta domin ta tabbatar da yana raye babu wanda ya isa ya mata haka har shi Baba Wazirin da kansa. Can kuma ta fara murmushi mai sauti tunawa da yadda AA ya rude a lokacin da suka fadi din, sai a lokacin ta soma dariyar abunda ya faru tsakaninsu tun haduwar farko har zuwa yau.
FALMATA POV.