← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 172

Sashe 1

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

03/12/2021, 08:04 - Messages and calls are end-to-end encrypted. No one outside of this chat, not even WhatsApp, can read or listen to them. Tap to learn more.
03/12/2021, 08:06 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄*

By Khadeeja Candy

1

_©®Hakkin mallaka nawa ne ni kadai, ban yadda a saffaramin labari ta kowace siga ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba a kiyaye⚠_

*FICTION.*

FREE PAGE.

FALMATA POV.

Yola...

Tun tana surfen da kuzari har ta kai bata iya daga tabaryar da karfi, babu komai a tare da ita sai tarin yunwa da gajiya ga wani uban ciwon kai da ya saka ta gaba. Cike da dauriya ta
karasa surfen sannan ta risina tana kwashewa tana zubawa a kwayar da ke gefen turmen, sai da ta kwashe shi tas sannan ta hade da sauran da ta surfe, mikewa tai tsaye tana rike da surfen ta nufi gurin tukuyar ruwansu.

"To mai kunne kashi ban fada miki idan kika yi surfenki ki rika zuwa bohal kina debo ruwanki ba? Ke wai Fulani sau nawa za ayi miki magana ne?"

A wahale Falmata ta kalli Tumba wacce ke mata maganar, ta amsa mata tana jin kamar ta fadi a tsakar ranar da ke dukan kanta.

"Inna idan na gama zan je na debo wasu sai na cika"

"Ban yarda ba, kije ki fara debowa ki yi abunda za ki yi wannan wanda kike debo mana na aiki ne bana wankewa wasu banza surfe ba"

Uffan bata sake ce mata ba, sai ta nufi gindin bishiyar dogon yaro ta aje surfen, sannan ta sake komawa ta dauko wani katon bokoti ta riko shi a hannu ta nufi kofar fita jiki ba gwari, tafiya take a hankali kanta a kasa bata kallon kowa sai hanya, gaisuwar girmama ce abunda yake fitowa daga bakinta sa'adda duk tai arba da sa'ar iyayenta. A yayinda ta isa bohal din sai ta nemi guri ta tsaya tana ta kallon yadda fanfon bohal din yake cike da mutane yara da manya. Matsawa ta kara can gefe tana daga zanenta kamar mai kyankyamin ruwan da ke zube a kasa.
Kallo daya za ka yi mata ka karancin irin natsuwa da tarbiyar dake tare da ita, sa'aninta na gaban fonfon suna gogoriyon dibar ruwa ita kuma tana tsaye gefe abunta tana kallonsu kamar ba diban ruwan ta zo yi ba.

"Falmata kawo na baki bokiti daya"

Cewar Khadija kawarta, abun ka da mai nema sai tai saurin cira kafa ta isa gurin da Khadija take tsaye rike da kan fonfon ta mika mata bokitinta.

"Na gode kawata"

"Karki damu, indai akwai mu ba kya rasa komai kawata"

Khadija ta fada tana daga mata gira, murmushi ne ya fadada kansa a fuskar Falmata ya bayyana fararen hakoranta wanda ya karawa bakar fatarta sheki.

"Yau ba za ki je gidan Sarki ba? Kin san fa ke ce mai gyara dakin yan uku da kula da su"

Khadija ta tambaya tana daga muryar wai dan mutane da ke gurin su san kawarta na aiki a gidan Sarki. Wata irin kunya ce ta rufe Falmata abun ka da bakauyen mutum sai duk ta ji ta muzanta.

"Ke Madam ba za ki ba yau?"

"Na tafi, har na dawo sai kuma gobe"

Ta amsa mata kamar ana matso maganar daga bakinta, gaba daya kunya ta gama rufe ta, kamin bokitin ruwan ya cika duk ta tsawwala, bokitin na cika Khadija ta kama mata ta dora a kai sannan ita ma ta dora nata suka kamo hanya tare.

"Mtswwwww Wallahi Falmata ba ki hadu ba, wai ina son ayi kurin nan ke kuma kin wani noke ba ki ma son amsawa"

Abun nan dai da ya zame mata al'ada ta yabawa fuskarta, wato murmushi sannan ta soma magana da muryarta mai taushi da dadin sauraro.

"Khadija kunya na ke ji"

Wani banzan kallo Khadija tai mata.

"Kunyar me? Aikin a gidan sarki? Allah ya kai Khadija Wallahi har tafiya sai na sauya"

Wannan karon dariyar marar sauti Falmata tai, tana jinjina lamarin kawarta, daman can indai kaudi ne da iyayi da ba ni na iya ba dai Khadija ba.

"To ai na ga ni ban wani dade da fara aikin ba, da har za a ce na fara kuri wannan zuwan da nai dazun fa shi ne zuwana na uku, kuma ni na ga..... "

Sai kuma yai shiru bata karasa ba, sai dai karara yanayinta ya nuna akwai damuwa a tare da ita kamar yadda fuskarta ta nuna akwai tarin maganganu a kasan halshenta.

"Miya faru?"

Tsayawa tai tana kallon Khadija kamar yadda Khadijar ma ta tsaya tana kallonta.

"Sai na ke ganin kamar ba su yarda da ni ba...."

Fuskar Mamaki Khadija tai.

"Ban gane ba?"

"Kin ga tun da aka dauke ni aikin, har yanzu ban ga yaran ba, sai dai na gyara dakinsu, kuma idan zan gyara sai a saka dogari ko wata baiwa sun tsayaa dakin har nai na gama"

"Suna da wulakanci ne?"

"Aa har yanzu ba a taba min ba, ban ga alamun hakan a iyalan gidanba, sai dai da alama suna da wuyar aminta da mutum"

Hannu daya Khadija ta saka ta daga kafadarta.

"Karki damu, daman su yan sarauta basa saurin aminta da mutun, amman dai da sannu za su fahimci kawata mutuniyar kirkice su aminta da ita"

Ta karasa tana dariya tare da rika fuskarta.

"To Allah yasa"

"Amin, kuma bari na fada miki ba wai saboda wannan bakar Tumba ta tura ki aiki dan ki samo mata kudi ba, ba wai duk abunda aka ba ki za ki bata ba, albashin ma rabi za ki bata ki boye rabi, dan alherin idan kin samo karki kuskura ki bari ta gani, ke abinci wannan ma da ki kawo mata Wallahi kara ki ɓarar dashi a akwata"

Har wani yatsine fuska Khadija take tana jin kamar ace ita ce a matakin Falmata take da step mother kamar Tumba da Allah kadai ya san irin sherin da zata kulla mata.

"Mahaifina yace idan ban mata biyayah ba be yafe min ba, ko da ace bata san yawan kudin aikin ba zan bata dika balle kuma ta riga ta sani, idan ma na hana ta zata iya duka ko taja Baba da kansa ya doke ni, ba ni da wani yanci a gidan nan Khadija kin sani"

"Hmm ai har da ke Wallahi da kike biye mata, ke ko yar ketar nan ba ki iya ba, Wallahi da ni ce da sai ta sha wuya, shiyasa na tsani shegiyar matar nan bakar Tumba kawai"

Falmata da dai bata ce mata komai ba, ta cigaba da tafiyarta, sanin kanta ne idan zata ce Khadija ta daina kiran Step mom dinta gatsasa sau hansin sai Khadija ta aikata sau dari biyu.

"Ki duba ki ga fa saboda ki Wahala ta tura ki aiki a gidan, ga yayanta, muna wai dan tsabar zalinci tace ita zata karbe albashin, bayan babu abunda take tsinana miki"

Tafiya suke Khadija na jifar Tumba da kalamai marasa dadi, Falmata dai bata ce mata uffan ba har suka raba hanya, kowa ya dauki hanyar gidansu. Da sallama ta shigo cikin gidan amman aka rasa mai amsa mata kamar masu gaba da ita ko kuma wadanda ba su ji sallamar ba. Ko kadan hakan be dame ta ba, inda da sabo kusan ta saba da wannan rayuwar. Kallo daya tai ma Naja ta dauke kai ta hade wani abu daya tsaya mata a makoshi, yar gata kenan masu yin yadda suke so a gida ba kamar ita ba, wacce aka hana wanke surfen da ruwan da ita da kanta tai aikin jigilar debo su da safe, an bar yar gaban goshi tana wanki da su.

Sai da ta sauke ruwan sannan ta nufi gurin da surfen yake ta dauko ta wanke, ragowar ruwan ta juye a karamin bokiti ta shiga bandaki tai wanka, dakinsu ta nufa ta shafa mai abun ka da mai son kwaliya sai ta dauko ragaggin kayan kwaliyarta ta tai kwaliya har da su jan baki. Ta yi kyau sosai duk kuwa da kasancewar ta baka sai dai bakin be rage ta da komai ba daga kyaun sura kwarjini ta halitta da kuma cikar sura da zati irin na ya mace. Baka ce amman ba mummuna ba, baka ce kyakkyawa irin kyau ne mai shining. Bakinta mai kyau ne wanda ya kara fito da manyan idonta kuma farare tas, sai dai bayan ido da hakora da tafin hannunta da na kafa babu sauran wani gurin da fari ya bayyana a jikinta. Yana daya daga cikin dalilin da ya saka Falmata bata sha'awar saka bakin kaya, domin ganin take ita da tufafin za su saje ne.
Bayan ta gama shiryawa ta mike tsaye tana cigaba da kallon kanta a madubi kamin ta maida dan karamin madubin a mazauninsa da ke cikin kayan kwaliyarta.
Tsakar gidan ta fito ta nufi kitchen dinsu ta dauko abinci da ke rufe a langa (Kwano) ta zauna jikin kitchen din ta soma ci tana ta kallon awakin gidan da ke ta aikin kuka suna fada da junansu, sun ɓata turkensu sun masa kacha-kacha kamar ba dazun ta gama gyara shi ba. Can kuma ta maida dubanta gurin mayan shanun da ke daure guda biyu a gafen garken awakin.

"Idan kin gama ki taso ga surfen masarar nan ki surfa ko tiya daya ne"

Kam ta gama cin abinci Tumba tai mata furucin, a take yanayinta ya canja tai narai narai da fuska kamar ta fasa kuka.

"Inna ba kin ce sai gobe ba"

"To masu masarar yau suke son abunsu, kuma da safe ai sai dabobi su samu abunda za su ci"
Chapter 1 · 0% Book details