← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 94

Sashe 79

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk suna zaune afalon aka bude kofan falon ahankali da sauri kowa yadaga kanshi yakalli kofan Layla ce idanunta sunyi jajir ga fuskanta har yanzu shaida mari watsa watsa akai, kallo daya Dad yamata zaiyi magana Mami dake kallonta tarigata tace “meyasameki Layla”? Dasauri Dad yace “what happen to your face like this? Shigo kin tsaya agaban kofa” shigowa dakin tayi ahankali tamaida kofan ta rufe, kallo daya Farrah tamata tadauke kai wani abu na tsayamata awuya, karasowa ciki Layla tayi ahankali ta zauna atsakiyan falon kaman mai bara tahade hannayenta biyu zatai magana Dad Ya ijiye bowl don hannunshi dasauri yajuyo yakalleta yace “meyafaru wayadakeki haka”? Baki Layla tabude zatai magana saikuma tafashe dawani kalan mugun kuka tama kasa magana, ijiye Littafin datake karantawa Mami tayi itama tazubama Laylan ido, what happen take kuka haka kuma Layla bata taba shigowa side dinta ba, anatse tace “meya faru Layla?” Wani kalan ijiyan zuciya Layla ta sauke sannan takalli Mami ahankali tace “Mami” sannan takalli Dad tace “Dady” bayan hannunta takai tashare idanunta tace “Dad yau nazo nagaya muku gaskiya ne tsakanina ga Allah dan ina bala’in, ina matukar so dakuma kaunar Zayn Dady, I love Zayn alot!” Wani kalan kwarewa Farrah tayi da pepper soup din datakesha tashiga tari sosai dayasa Layla tai shiru kowa na dakin yajuyo yana kallon Farrah, Shafa tamika mata ruwa tace “sannu” wani kalan kabar da ruwan da Shafa ke bata Farrah tayi cikeda haushi sannan tamike tayi sama da gudu both Mami da Dad suka biya da kallo Shafa ta tashi tabita abaya, dan ijiyan zuciya Dad yasauke Ya hade rai yakalli Layla yace “did you realize what u are saying Layla akanme zakizo agaban matan mutum kina cewa kinason mijinta ba kunya” hawaye Layla ta share cikin wata kalan raunanniyan murya tace “Dady wlh inason Zayn kuma inason shi da aure idan nan auri Zayn ba zan mutu, yanzu bama wannan ba Dad call Zayn duk inda yake rayuwanshi nacikin gagarumin Xhatsari za’a kasheshi!”

7️⃣3️⃣

Wani kalan zabura Dad yayi yamike tsaye dasauri yanadan zaro idanu zaimayi maganan maganan ta makale Layla ta gyadamai kai tace “believe me Dad, just call Zayn yadawo koma ina yaje yadawo gida I need to know Zayn dina is safe kafin nafada muku abubuwan danakeso nafada muku” tabe taben Aljihu Dad yashigayi baiji wayanshi ba dasauri yakalli Mami da wayanta ke kusadashi yace “kiramin d’ana Mami yisauri” wayanta Mami ta dauka tai dialing number Zayn, ringing daya ya dauka Mami nakokarin magana Dad ya fizge wayan yakara akunnenshi yace “Z……Zayn, where are you my Son”? “I’m outside jogging Dad” dasauri Dad yace “kadawo gida yanzun nan come to me kaji” jin yanda muryan Baban nashi kenan ba lafiya yasa yace “okay” dasauri Dad yafita bodyguards dinshi ya tattara kusan 14 sukai waje daidai Zayn nashigowa gidan yana sanye da kayan gym nashi wani kalan rungumeshi Dad yayi ahankali yace “Alhamdulillah” dan tureshi Zayn yayi yace “lafiya Dad” hannunshi Dad yakama gamgam yakalli head na bodyguard nashi yace “double d security na gidan nan call IG na police kacemai I need police around my entire house front and back” dasauri Zayn dake kallon Baban nashi yace “what’s happening Dad” hannunshi Dad yaja yace “let’s go” sukai dakin Mami suna shiga ganin Layla atsakiyan dakin tana share hawaye har lokacin yasa ranshi yabaci, Dad yakalli Layla dake kallon Zayn yace “ga Zayn dinnan he’s safe tell me everything” gyadamai kai tayi Dad na zama yanajan Zayn dake tsaye hakan yasa yazauna kusada shi yanama Layla mugun kallo.
Anatse tace “Dad da ina UK mom was seriously disturbing me kan nakare project dina and take the next available jirgi nadawo naija dan plan nasu has failed nine her best option now, nace wani plan tace idan nazo zata fadamin shine nazo naija” tadanyi shiru Dad da kafarshi ke shaking jin ana magana kan Hajiya Mariya yace “saime yafaru”? Ahankali tace “dana dawo take sanar dani sun sa anyi kidnapping Zayn, sunaso akashe Zayn but Zayn was able to escape, gashi yanzu kayi doubling security da guards nashi babu ta yanda zasu cimma burinsu she wants me to get close to Zayn dan no one will suspect me, idan Zayn yasaki jiki dani zata bani poison nabashi yasha yamutu” hawaye suka gangaro daga idanunta, ahankali tace “Dad I will not lie I wanted to do it cus bawai nasan Zayn sosai bane dan baya zama agidan nan a kasan waje yake I became close to Zayn and just fall in love with him Dad nakasa komi, infact sabida ban iya nacika musu burinsu bane yasa tamin wannan dukan she called wasu agabana kan akashe Zayn yau yanzu ma tafita” wani kalan ijiyan zuciya Dad ke saukewa yana kallon Layla kana ganinshi kasan ranshi a bala’in bace yake, anatse Dad yace “kinata cewa su su, da Hajiya Mariya da waye keson kashemin yaro”? Kallon Dad tayi ahankali tace “da Mommy, da Hajiya Fatima, dakuma Uncle!” Wani kalan mikewa tsaye zumbur Dad yayi yana kallonta yana zaro idanu yace “Layla!” Saida gidan ya amsa sabida yanda Dad yay ihu, cikin tsananin fushi yace “da farko na fara yarda da abubuwan dakike fadi but dakika kira sunan kanin uwa daya uba daya jinina yasa nasan karya kikeyi duk plan na Hakiya Mariya ne kizo kifadamin haka kihadani da yan uwana” cikide da tuhuma Mami tace “are you lying to us Layla? Kina kokarin raba yan uwa ne menene amfanin irin wannan shairin”? Fashewa da kuka sosai Layla tayi tace “wlh wlh na rantse da Allah, idan karya na muku Allah yasa nafadi na mutu anan wlh ba karya nayiba, Uncle natare dasu Momy tare suke planning komi tundaga farko, akwai gidan da suke haduwa ma, shi bayason akashe Zayn koda akai kidnapping Zayn Uncle ne ma yasa akai delaying komi da tuni su Momy sunsa akanshe shi danshi Uncle gabaki dayan dukiyanka yakeso, komi da komi, yaji bakin cikin yanda kabarma Zayn komi, Uncle dukiyanka da companies naka yakeso ya mallaka ya tattara yabar kasan da family dinshi saisa shida su Mommy sukai teaming up” baya Dad yayi zai fadi dasauri Zayn yatareshi ahankali yace “calm down Dad” kanshi Dad yanuna yace “Zayn ni, ni, ni kanina zai jona baki da makiyana adaukemini yaron dayasan nafi kowa so aduniya? Yarona ya wahala, yarona ya karye, wacce ta ceceka saida aka harbeta, Zayn da gaske Uncle dinka is among them ko karya yarinyan nan kemini” lumshe idanu Zayn yayi yabude yasha ganin Uncle taredasu Hajiya Mariya but ko ajikinshi, saisa he believe all abinda Layla tafadi, Mami karan kanta jikinta yay wani kalan sanyi, zaunar da Dad kan kujera Zayn yayi Mami takawo ruwa mai sanyi a cup tabashi yasha tace “calm down Alhaji” ajiyan zuciya Dad yasauke yay shiru na kusan 20min sannan yakalli Mami yace “lokacin data fara gayamin maganan I wanted nasa akama su Hajiya adaure for attempt murder na dana dakuma kidnapping but yanzu data fadi har dan uwana I cannot do anything” yasakeyin shiru sannan yakalli Zayn yace “kawomin journal dina da pen” tashi Zayn yayi yay sama agaban bene yaga Farrah tsaye idanunta sunyi ja, Shafa ma haka” wucesu yayi zuwa dakin Dad yadauko journal yadawo kasa yabama Dad atake yarubutama kowaccen su saki bibbiyu daman duk yataba musu saki daddaya sabida Zayn yanzu yabasu biyun daya rage, sannan yay waya yasa aturomai manya manyan trailer da ma’aikata yanason duka kayayyakinsu afitarmai dasu daga gida harta plate na Dakinsu baiso abari sannan ya ijiye wayan ahankali yasake sauke ijiyan zuciya yakalli Mami yace “zaki iya rike Layla tunda batada iyaye”? Shiru Mami tayi batace komiba hakan yasa da sauri Layla tahade hannayen ta biyu tana kallon Zayn da Dad tace “Dad the greatest gift dazaka bani aduniyan nan shine Auren danka, Dad inason Zayn kaman zuciyata zata buga, wlh idan ban auri Zayn ba zan iya mutuwa, dan Allah Dad kurufamin asiri” ta wutsiyar idanu Zayn yakalli Farrah dake tsaye sama gaban bene tana kallon Layla idanunta sunyi jaa gawani kalan wutan kishi daya hango cikinsu dan murmushi yayi azuciyanshi, baki Dad yabude zaiyi magana Zayn yace “I will marry you Layla!” wani mugun bugawa gaban Farrah yayi saida tai wani baya zata fadi da bala’in sauri Shafa ta tareta, Zayn yakalli daga Dad har Mami dake kallonshi baki sake yace “Dad arrange the marriage inaso muyi aure nan da 7days” ganin yanda Dad da Mami ke kallonshi baki sake yace “chill after all she just saved yaronku from those evil people she betray her Mommy for me kodan hakan ta canchanci na aureta dan haka I will marry her” yatashi daga kan kujeran zuwa inda Layla take zaune akasa ahankali yadaura both hands nashi kan kafadarta yadagota tamike tsaye yace “daga yanzu you will be staying here har zuwa rannan aurenmu akaiki gidana okay” wani kalan gyadamai kai Layla tayi tana kuka sosai hannunshi yadaura kan lips nashi yace “shiiiiiii” dawani kalan rinanun idanu Farrah takalleshi daga sama tana tuna yanda yake cemata shiiiii harma yadaura hannunshi akan lips nata, ahankali yace “let’s go lemme take u to your room” ahankali yana rikeda kafadarta yay stairs da ita suna hawa ahankali suna sama, ko kallon inda Farrah take baiyiba yawuce da ita dakin dayake gaban na Farrah wanda daga dakin Farrah sai dakin yabude ahankali yashiga da ita har zuwa gaban gado, dan kallon kofan yayi hakanan yanaji ajikinshi Farrah zatazo inhar tazo tanason shi inhar batazo ba dagaske bata sonshi.
Chapter 79 · 0% Book details