← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 94

Sashe 24

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

EPISODE 1️⃣5️⃣
Wuraren 6 nasafiya tashiga bude idanunta dasuka mata nauyi sosai sunyi tsami, da kyar take budesu kafin takarasa budesu gabaki daya tanabin saman dakin datake da kallo dakeda haske mai kyau, kodai tamutu ne ta tambayi kanta tana sake kulle idanunta sanan tabudesu ahankali kaman wacce ke kokarin tantance abu, ganin still dakin take yasa ta juyarda kanta tabi ruwan da ake kara mata da kallo zuwa hannunta da ake karama ruwan, yunkurawa tayi zata tashi zaune amman takasa sabida zafin dataji agefen kirjinta batasan lokacin data saki wani malalacin kara ba. “Asshhh” dagokai Mami dake kan dadduma tana lazimi tayi ganin Farrah ta farka yasa tai murmushi, shafe addu’an datakeyi tayi sanan ta mike tsaye ta taho gaban gadon, tunda tafara tafiya tana tahowa Farrah dake kwance akan gadon ta tsare Mami da idanunta dan ganin wata faran kyakkyawan mata tayi tanada dan jiki ba yarinya bace, tanada kyau na gaske kaman wata Yar arab, gawani lafiyayyen murmushi kwance kan fuskan matan tana kallon Farrah itama hakan yasa Farrah tace “to kodai tana aljanna ne” tsayawa Mami tayi gaban gadon daidai saitin kan Farrah sanan takai yatsunta biyu tadaura kan saman goshinta tana duba temperature dinta ahankali tace “kin tashi”? gyadamata kai Farrah tayi ahankali tana kallonta still kana ganin kallon kasan kallon na wanda bata sani bane kallon sabuwan fuska, ganin yanda Farrah ke kallonta yasa Mami tai murmushi tace “zaki zauna”? Gyadamata kai Farrah tayi dasauri hakan yasa Mami ta taba wani abu gadon yadago Farrah ta zauna tana dan yatsine fuska sabida tsami da jikinta yayi, “jikin ki na ciwo”? Mami ta tambayeta ahankali, dagokai tayi ta kalli Mami batasan mesa ba samin kanta tayi da gyadamata kai ashagwabe kaman zatai kuka, murmushi Mami tayi takai hannunta guda biyu tai cupping face nata murya chan kasa tace “duk zai daina nan bada jimawa ba, yanzu zakiyi wanka saiki salla, saikici abinci saina baki magani, kinajin fitsari”? Dasauri Farrah ta gyadamata kai, murmushi Mami tasakeyi tabata hannunta tace “sauko to muje” da taimakon Mami ta sauka daga gadon ahankali, slippers Mami tabata tasaka sanan suka shiga bayi, dakanta Mami ta hada mata ruwan zafi na wanka, sanan tasamata toothpaste a sabon brush dake bayin tace “ki brush saiki wanka, ina zuwa” Mami tafito daga bayin, fita tayi daga dakin tasauka kasa wani boutique dasuke dashi a asibitin tashiga, tundaga kan pant, wani pink gown, da black hula, da after dress Mami tasaya mata da cream, tabiya kudin ta taho, bra ne kawai batasaya ba shima dan bazata iya sawa yanzu bane sabida aikin da akamata, komawa dakin tayi, landline na dakin ta dauka tamusu order lafiyayyen breakfast asibitin babban gaske ne kaman hotel yanda zakai order abinci a restaurant na hotel haka asibitin ma yake, ijiye komi tayi sanan tawuce gaban bathroom din knocking tayi tace “kin gama”? Jin shiru yasa tashiga bayin tana zaune tagama wankan amman takasa daukan towel, kare kirjinta tayi a kunyace, towel Mami ta dauka sanan tazo inda take lullubeta da towel din tayi sanan ta dagata tashi tayi ahankali tarike Mami batada karfi ko kadan, fito da ita Mami tayi da taimakonta ta shiryata tsaf sai kunya takeji, pink gown din Mami tasamata daya amsheta da black hula, Mami tace “kinyi kyau” sata tayi tai salla azaune kafin ta idar an kawo musu abinci, gado ta dawo zama tayi Mami tabata tea ahankali ta karbi cup din tana kallon Mami, murmushi Mami tayi tace “baki sanni ba ko” Gyadamata kai Farrah tayi, murmushi Mami tasakeyi tace “sunana Mami” anatse tace “nine mahaifiyar Zayn, yaron dakika taimakamawa har aka harbeki tasanadin hakan, munzo dake asibiti nan Abuja tareda mahaifinki Baffan ki amman shi yatafi, yanzu kina wajena har kiji sauki karkiji tsoro kinji zan kula dake ni Maman kine kinji” Gyadamata kai tayi ahankali, murmushi Mami tayi tace “sha tea dinki to” tea takai bakinta saida ta tada kofin sanan tacire daga bakinta tabama Mami kofin, wani irin tausayinta Mami taji tace “nakara miki tea”? Gyadama Mami kai tayi dasauri, tea dinta Mami tamika mata karba tayi shima ta kwankwade, ahankali Mami tace “nasa akawo miki wani”? Girgiza ma Mami kai tayi alamun ta koshi, ajiye cup din Mami tayi sanan takalleta tace “fadamin sunan ki” kai tazo zata girgiza Mami tace “a’a bude bakin ki kifadamin da baki, naduba bakin ki jiya nasamiki magani, muryanki yadawo zaki iya kina magana yanzu, fadamin sunanki naji” ahankali tabude bakinta tana kallon Mami kaman yanda Mami ke kallonta, da duka karfinta da tsantsan kwazo da struggling da kai kanka dake kallonta zaka iya gani a kwayan idanunta ta danne idanunta tace “F…….Ffffff…………Farrrr……” bude idanunta tayi da sauri hardan zufa ya keto mata a goshi tsabagen kokari, murmushi Mami tayi sosai tace “sannu kinji, all you need is just a little therapy, amman kina magana, ke ba kurma bace, u can speak, karasa fadamin sunan naki inji” ahankali tace “Farrrrrr………..r……….rahhh” wani kalan huge smile Mami tayi tace “wowwww” itama Farrah murmushi tayi takai hannunta kan bakinta tana shafawa dudda sunan ararrabe takira but she was able tafadi sunanta yau, Shafa kadai take iya kira, itama da kyar take fadi, but yanzun nan tafadi ma Matar nan sunanta. “Kinji dadi?” Mami tamata tambayan ganin yanda take murmushi takira sunanta, kai ta daga zata gyadama Mami dasauri Mami tace “no, dabaki zaki amsani” dan runtse idanu tayi kaman yanda mai in’i’na keyi tace “e….h” murmushi sosai Mami tayi tace “good girl” wani strawberry smoothie dake cikin wani fine bottle da straw dinshi tadauka tasamata straw din tabata, ahankali tasa hannu ta karba cikeda dason gwada magana kuma tace “n……….a……g…..de” dan murmushi Mami tayi tana saka labcoat nata tace “kigodema Allah” tab dinta ta dauka ganin zata barta ita kadai yasa ta shiga YouTube wani cartoon movie tasa mata sanan tabata, ahankali Farrah tasa hannun ta daya ta amsa dan sayan tana rikeda smoothie Mami tace “kiyi kallo bari naje naduba wasu patient ko, yanzun nan zan dawo kinji” zata gyadama Mami kai Mami ta girgiza mata kai alamun no hakan yasa tace “tttttt….o” murmushi Mami tayi tajuya tafita daga dakin, saida tamaida kofan tarufe sanan tasaukar da kanta ahankali bayan Shafa wanan ce mata tabiyu dake sonta aduniya, Matan kaman Maman ta, hawaye ne suka zubo mata daga ido dasauri tasa hannunta ta share sanan takai goran smoothie baki tafara zuka dadin dataji yasa tahau sha sosai tana kallon cartoon dinta ita kaman ma abarta a asibitin taitai zama.
Chapter 24 · 0% Book details