← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 94

Sashe 25

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bude musu bayan motan bodyguards sukayi, ahankali yasauko daga motan yana sanye da Greg Lauren horizon print crew neck t-shirt, black color ne t-shirt din dakeda zanen rana ajiki da color na sunset, yasaka wani jean na Ksubi, frescobol Carioca round toe espadrilles (takalmi) yasaka, yauma wani Rick Owens sarka yasaka daya fito dashi yasauka agaban riganshi yana kyalli kana gani kaga dimond, fuskanshi har wani sheki yakeyi idanunshi sanye da bakin glasses na police sabida plastan dayake idanunshi, duk wanda ya kalleshi saiya sake juyowa ka kalleshi zaka dauka wani musician ne yazo, agogon dake hannunshi ya kalla na Horus, ganin 11:15AM yasa yadanja gajeren tsaki, bayanda zaiyi ne yazo hospital dinan all he needs right now is to smoke and yasami mace, rabonshi dayasha taba tun ranan nan, fitowa Dad shima yayi daga motan waya a kunnenshi yana magana awaya sanan yasa hannunshi yaciro wani katon teddy babba na lion king mai remote, idan kadanna remote din zaka dauka live lion ne yana tafiya sanan yay haushi, karasowa gaban Zayn yayi sanan yace “hold on Barrister lemme talk to my Son” cire wayan daga kunenshi yayi yakalli Zayn din, teddy yasamai a hannu yace “ga teddy daka sayama patient dinmu, jeka sami Mami ka Dr ka will see u daga nan I need to rush, one of the kidnappers da aka kama yay magana I need to go” yakalli bodyguard dinshi yana daya magana yace “go with Zayn” sanan yashafa fuskan Zayn din yace “bye son” ahankali yace “bye” sanan yawuce yana tafiya ahankali har zuwa gaban dakin da Farrah keciki, bodyguard din dake biyedashi yakalla yace “get me a pack of cigarettes” batare daya jira amsan shiba yabude kofan dakin yashiga ciki, jin anbude kofa an shigo dakin yasa Farrah tadago kanta da wuri hada idanu sukayi da Zayn daya kallo gadon dudda idanunshi nacikin bakin glasses but tsaf kallo daya Farrah tamai ta ganeshi, kafeshi tayi da idanu bata ko kyaftawa tana kallonshi kaman yanzu tafara ganinshi ganin ya chanza mata kaman ba mutumin jiya ba dahar kuka yake, yawani kara zama mata babba sosai a idanu kuma yay wani kalan kyau kara kallonshi take sabida sarkan dataga yasaka kaman mace, wani zirrrrrr yaji ajikinshi sabida yanda take Farrah ke kallonshi da manyan idanuwabta dake nan kar kar kaman madara dawani kalan sauri yadauke kanshi yakarasa shiga cikin dakin sanan yawani kalan defa mata teddy lion din akan gado tawajen kafafunta dasauri takalli teddy sanan ya jefa mata remote dinma da mistakenly ya danna remote din ya kunna teddy, Farrah dake kallon teddy ita Allah yasan bama tasan akwai abu kaman haka aduniyan nan ba, gani tayi teddy dake kwance kafanta yawani tashi tsaye lion din yana kallonta in the eyes, bala’in faduwa gabanta yayi, ganin yafara nishi yana bude bakinshi yay wani kuka tareda tsalle gabaki daya yasa daga pad da drink din datake sha duka tawani watsar dasu kan gado ta kurma ihu da Zayn dake zaune kan kujera yaciro wayanshi yana dannawa baimasan abinda ke faruwa ba yadago kanshi dasauri. “Aahhhhhh” wani kalan tsalle tayi ta dirko daga gadon tama manta tanada ciwo shima lion din tsalle yayo zai fado kanta wani wawan ihu tayi tama rasa inda zata fadawa kan dogon coach din da Zayn kezaune tayi tawani kalan fada jikinshi daga ita harshi fadawa sukayi flat kan kujeran yana kwance tana kwance saman jikinshi ta kankameshi gam gam jikinta nawani kalan rawa ta kulle idanunta, sake tsalle lion din yayi tareda haushi zaiyo kansu hannunshi da baida lpy Zayn yasa chak yakama lion din yana kallon fuskanta yanda lips dinta ke bari, gabaki dayan hanuwanta ta rirrikeshi dasu, kafe fuskanta yayi da idanu yana kallonta is she scared? Ya tambayi zuciyanshi, tureta yashigayi daga jikinshi kin sauka tayi taki bude idanunta ta makalemai wuya alamun barata sauka ba, baki yadan bude cikeda kulewa yace “sauka daga jikina” kaman wacce ke tsoroOOn bude idanunta tabudesu tadaura idanunta kan fuskanshi hakanan jJi tayi gabanta yafadi dum!….

EPISODE 1️⃣6️⃣
Dudda yana sanye da black glasses bata ganin kwayar idanunshi amman wani kalan cika mata idanu yayi gashi yana wani kalan kamshi da takeji kaman kada tasakeshi tunda take aduniyan nan bata tabajin irin kamshin dayakeyi ba Subhanallahi kamshin dadi, ganin yanda yabata rai yana jiranta ta sauka daga jikinshi yasa ahankali tashiga dagashi tana satan kallon lion din dataga yarike a hannunshi, komawa gefen kujeran tayi ta nannade kanta cikeda tsoro tana kallon hannun nashi dake rikeda lion din sai yanzu ma taji inda aka mata dinki namata ciwo, tashi Zayn yayi ranshi bace, kayan jikinshi ya kalla ganin yanda suka yamutse dudda bawani yamutsewan kirki bane amman jiyayi ranshi yabaci kallon Farrah yayi da itama daidai lokacin tasaci kallonshi wani dan iskan tsaki yaji. “Mtswwww stupid girl” yafadi ahankali ware idanu Farrah tayi jin yazageta bata wani jin turenci but tasan stupid tun a kauyen su wucewa yayi fuuu yafita daga dakin da teddy a hannunshi daidai bodyguard din daya aika siyomai taba nadawowa teddy yamikamai cikeda masifa yace “donate this teddy to children ward, apparently the stupid girl na tsoronshi” yay maganan yana fizge kwalin tabanshi yawuce waje jikinshi har tsuma yake yakosa yasha taban.

Shigowa dakin Mami tayi ganin Farrah zaune kan kujera yasa tace “Iyye kin sauko”? Kai Farrah tadaga zata gyadama Mami, Mami tai mata kallon no, hakan yasa tadan runtse idanunta tace “e……h” murmushi Mami tayi sanan yawo wajenta gefen kujeran ta zauna hannunta takama tace “nasan yanda kikeji, but idan zaki magana, relax, take it easy, kiyi maganan a sannu akuma hankali batare dakinyi tunanin komi ba, once kika koyama kanki kina amsawa da maganan nan da 2days zaki fara magana lafiya lau kinji” wanan karan bata lumtse idanu ba ahankali tace “ehhh” murmushi Mami tamata tace “ina Zayn, Dr shi na jiranshi” ahankali tana kallon Mami tace “f…….iiii…ta” “okay yafita waje, bari naje nakirashi muje ganin Dr, I am coming idan nadawo zamuje gida, zakije gidana”? Mami tamata tambayan cikeda so, wani cute smile tama Mami ahankali tace “eh” wucewa Mami tayi tafita daga dakin tana murmushi she so much love Farrah bama tasan mesaba.
Chapter 25 · 0% Book details