← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 94

Sashe 56

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Wasu kuloli Mami tanuna mata hakan yasa tadinga daukowa tana kawosu dinning itakuma Mami tafito falon, zama tayi kan one sitter tana kallon yanda Zayn kecin abincin agajiye hakan yasa tace “kagama aikin”? Gyadamata kai yayi ahankali yana kai abinci baki, ahankali Mami tace “babanka yace idan kadawo kada kaje ko’ina kajirashi” Gyadamata kai yayi ahankali yana ture abincin dako 4 spoons baiciba zai tashi Mami tace “koma ka zauna” komawa yayi ya zauna tashi tayi ahankali kaman bataso tazo kusadashi yazauna, plate na abincin ta dauka tace “tun safe ace mutum baici abincin kirki ba kuma yanzu kadan tsakuri abinci kaci zaka tashi bude bakinka” tai maganan tanakai abinci bakinshi dan murmushi kadan yayi ganin tasoma hucewa da fushin datake wato tsakanin uwa da da sai Allah, ahankali yabude bakin takai abincin yakarba ahankali daidai Farrah nafitowa daga kitchen dauke da kula baki tabude kaman wawiya tana kallon yanda ake bama katon namiji abinci, ahankali takarasa gaban dining ta ijiye kulan sanan tadago tareda juyowa ta rungume hannayenta aciki tana kallon yanda Zayn ke karban abincin da Mami kebashi awani kalan shagwabe, bata taba ganin bad boy irin Zayn ba malalaci sangartaccen banza kawai. Tai tsaki azuciyanta takaraso cikin falon ko kallon inda take batayiba tasa hannunta tadauki littafi ta da IPad din zata juya Zayn yace “pack the clothes naki ne Ke” kallon kayan Mami tayi sanan takalli Zayn din daya dauki glass cup na juice zaisha tace “kaika siyamata kaya” gyadama Mami kai yayi yana kai juice din bakinshi, itama Farrah dan satan kallon babban ledan tayi saikuma takalli Mami, Mami dake kallonta tace “yayanki yasiya miki kaya dauka kiyi godiya” ahankali kaman bataso takaraso tasa hannu tadauka murya chan kasa tace “nagode Ya Zayn” ko jiran reply dinshi batayiba tajuya tai stairs Mami tabita da kallo sannan tajuyo takalli Zayn dakeshan juice abinshi, saida ya kwalwale tass sanan ya ijiye yamike tsaye yana shafa cikinshi ahankali yace “Mami zakisa nafara tara fat ajiki, I am okay” abincin Mami takalla rabi yaci dududu ta tabe baki tace “nidai wuce kaje kai wanka kashirya masallaci” dan juya idanunshi yayi yace “yes Mom” sanan yadauki laptop dinshi yawuce yafita daga dakin Mami tabishi da kallo, she is happy Allah ma yasani dan fushin dasukayi dashi &na kwana biyu yasa yadan natsu Allah yasa natsuwan ya dore haka.

4️⃣9️⃣

Around 7 Dad yashigo gidan shida Uncle, Uncle na shigowa motanshi yawuce yace “Yaya nawuce gida saida safe” binshi da kallo Dad yayi yace “don’t forget to come early gobe duk kayi wani iri jeka kahuta” Dad na maganan yay hanyar flat din Mami burinshi duk inda zaije yadawo kawai ya sauka dakin Mami dan yasan zai sami lafiyayyen abinci da ita tagirka daki mai kamshi dayaji kamshin turaren wuta ko kwayan datti bazai taka ba, sannan ita kadai ke komi nata sai yanzu da Farrah ke komi dudda haka bata barinma Farrah girkin dazaici saidai suyi tare, da sallama yashiga falon wani lafiyayen kamshi yadaki hancinshi babu kowa a falon hakan yasa yawuce sama dakin Mami yabude tana kan dadduma hakan yasa yay murmushi yawuce dakin Farrah dashima yabude da sallama itama tana zaune kan dadduma murmushi yayi yawuce dakinshi wanka yayi yafito ya shirya cikin jallabiya fara kal sanan yadauki charbi yabude kofa yafito daidai Mami na shirin shigowa dakin ganin yasa tace “zaka masallaci” Gyadamata kai yayi yace “eh kaimin abincina sama nadawo asama zanci abinci nai sauri kada jam’i yawuceni” yay maganan yana wucewa hakan yasa Mami itama tawuce saida tafara bude kofan dakin Farrah ganinta tana salla yasa tasauka kasa abincin Dad takaimai dakinshi sanan tawuce dakinta.

Ana idar da salla yadanyi azkar kadan sanan yatashi gamamakin shi Zayn yagani a sahun farko inda yake yana zaune yay shiru wani tattausan murmushi yasaki sanan yajuya batare dayamai magana koyama bari yaganshi ba yafito yawuce gida, a falo yaga Farrah zaune da littafi a hannunta tana ganinshi ta ijiye littafin tana murmushi tace “Dad sannu da zuwa, Dady ina kaje banganka yau” dan dariya yayi yana karasowa inda take kanta yashafa cikeda wasa yace “garinku naje yau” zaro idanu tayi tana murmushi zata karamai tambaya yace “yi karatu kije ki kwanta you have exam tommorow yarinya na” murmushi tayi tace “Dad daman sabida kai na sauko kasa naganka idan kadawo nagama yanzu zanje na kwanta, Dad nagaji yau banyi baccin rana ba saida na koyi all the drawings da labelling nasu” baki Dad yatabe yace “Allah yasoni banyi science ba” Mami data fito daga kitchen rikeda jug tace “saisa kai missing ai” Farrah tahau dariya itama Mami na dariya Dad yace “Au taron dangi zakumini keda diyarki Allah yasoni nima inada Zayn dina shima dan art ne kaman babanshi” tashi Farrah tayi tace “Mami bacci saida safe” Mami tace “mu kwana lafiya sarkin baccin wuri, muje Alhaji kaci abinci” tashi Dad yayi yabi Mami zuwa daki, saida yaci abinci yay nak sannan takwaso komi tafito dashi zuwa kitchen sannan tadawo dakin zaune taga Dad bakin gado gefenshi yanuna mata hakan yasa tamaida kofan ahankali tarufe takaraso ciki anatse ganin kaman akwai abinda yakeso yafadi mata ta sauka kusa dashi.
Chapter 56 · 0% Book details