Sashe 29
Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wuraren 4 na yamma Alhaji yashigo gidan, ana budemai mota ya sauko daga motan yana gyara zaman babban rigan dake jikinshi, direct side din Zayn yawuce bodyguards dake tsare gaban side din Dad yakalla tareda amsa gaisuwansu sanan yashiga flat din Zayn dake wani kalan lafiyayen kamshi ga sanyin AC tako’ina daidai lokacin kuma Zayn dake sanye da bathrobe fari yadaure igiyan agaban rigan kafanshi sanye da bathroom slippers yafito daga kitchen dinshi da glass of milk a hannunshi yana kurba dasauri Alhaji yace “why are you getting milk dakanka bayan kanada masu maka”? Dan yatsine fuska yayi yana shigowa cikin falon, kan kujera yazauna tareda daura kafanshi daya kan dayan ahankali yace “I want to start doing everything myself from now, daga yanzu su daina shigomin cikin daki su tsaya nan bakin kofa” dan murmushi Alhaji yayi yana kallonshi trying to read something yace “ohh that’s new” zama yayi kusada Zayn din yana kallon farin glasses din da akamai na hospital dayake sanye dashi shi, glass din yamai kyau ba kadan ba, baki yabude zaiyi magana Zayn yarigashi ahankali yace “Papa” yay maganan yana ijiye glass na milk din kan coffee table sanan yadago, ahankali Alhaji daya tattaro duka natsuwanshi yace “Na’am Zayn menene me kakeso”? Dan juyowa Zayn yayi yakalli Baban nashi kallon daya dade baimaiba murya chan kasa yace “Dad am I being immature”? Yanayin fuskanshi kadai Dad yagani yagane he’s serious da tambayan baki yabude zaiyi magana cikin yanayi na baison yamai karya Zayn yace “don’t you dare lie to me Dad kafada min gaskiya please, I don’t have anybody, you are my best friend Dad, am I being immature”? Tsayawa Alhaji yayi yana kallon Zayn kalman best friend daya kirashi dashi wanda Zayn baitaba kiranshi dashiba yasa yaji kaman yay kuka, gently ya gyadama Zayn kai yace “yes! But just a little Son, I guess u just 26 still a kid that’s why” girgiza kai Zayn yayi tareda dan juya idanu irin na sangartattun yaran nan yace “no Dad, I think I am being incentive Dad, I am selfish and extremely rude” dasauri Dad yace “noooo Zayn kada ka kara kiran kanka haka, Zayn you are one sweet Human da duk wanda zai zauna dakai saiya soka, you are just being yourself, chasing your likes abubuwan dakakeso, and you are one reserve person baka shiga rayuwan kowa, shiru shiru, you are just the way you are, and being the way one is doesn’t mean he’s rude or incentive or even selfish, you are Zayn, my only son, abin alfaharina, kyautan da Allah yamin” yay maganan yana kama hannunshi mai lafiya trying to assure him abinda yafadamai gaskiya ne, shiru Zayn yayi yana kallon Babban shi na kusan 2min kaman yanda Baban nashi ke kallonshi, ahankali yace “Dad” ahankali shima Alhaji yace “na’am Zayn dina meke damunka haka nafara shiga damuwa wlh, menene talk to me, kome kakeso consider it done” dan ijiyan zuciya Zayn yasauke sanan yakalli hannunshi dake nan adaure yana kallon igiyoyin dan kwallin Farrah data dauremai hannunshi dashi, yatsanshi yakai kan igiyan yana tabawa murya chan kasa kaman mai tunani yace “When those goons kidnapped me Dad I went through a whole lot, I lost all hopes, was thirsty, hungry, ga karaya ga idanuna ga lot of spiders Dad at that point everything was a thing for me, I looked up to the sky nace Allah ya taimaken, then that gurl came from nowhere kaman daga sama aka jefota” yadanyi shiru yana kallon hannun nashi still in a very very low tone yace “Dad that girl protected me with all she got, at first I thought she was an angel, Dad kasan dan kwalinta tayaga ta dauremin hannun nan” yay maganan ahankali yana shafa hannunshi saikuma yadan yatsine fuska ahankali yace “Dad kasan I couldn’t thank her, whenever I looked at her sainaji she’s too small nace mata thank you and I am not use to thanking anybody” yadanyi maganan yana murmushi iya lebe kafin ahankali yace “Dad jikina is telling me I need to do morethan a thank you, she saved my life nima I should save her life and even give her a better life, education, da sauransu, Dad ina Uncle dinta kasa an daukoshi?” Dad na kallonshi right in the eye ya gyadamai kai, ahankali yace “tun around 3 chopper su yasauka, suna biyeda ni maybe ma yanzu haka sun shigo gidan nan” shiru Zayn yayi yana kallon mahaifinshi, lips dinshi ne yashiga rawa kaman yana fighting da abinda yakeso yafadi dan lumshe idanu yayi sanan yabude su yadaura su kan Dad ahankali yace “Dad can you adopt the girl please?”! Shi kanshi Alhaji saida yakara kallon Zayn maganan tazomai wani bagtatan bawai adopting yarinyar ne matsalan shiba ko kadan but this is the first time in history Zayn yacemai please kan wani abu mamaki ma hanashi magana yayi, ahankali Zayn yakai hannunshi yadaura kan na Alhaji yace “Dad lokacin da Mami tace the girl has been abused I felt so so guilty, bansan anything akanta ba but I know batada iyaye, and I know her uncle ran away they don’t like the girl, she’s like a burden, let’s call our lawyer muyi adopting nata idan ma so suke mukara musu wani kudi zamu kara, Dad I want to sponsor her education with my money not your own just to repay her kaji Dad” yakarashe maganan yana jijjiga hannun Alhaji, wani kalan sassanyar ajiyan zuciya Alhaji yasauke yana kallon fuskan Zayn din sanan yace “duk wanda cannot see beyond this your face da ake gani kaman u are rude is blind cus this your heart” Alhaji yakai hannunshi kan kirjin Zayn yace “is made from gold” dan murmushi Zayn yasaki, dan hararanshi Alhaji yayi yace “what are you waiting for, jeka saka kaya karakani nayi adopting yarinya ta Farrah” dan murmushi Zayn yayi yatashi glass cup nashi yafara dauka ya shanye milk din ciki sanan yawuce sama bai wani dade ba wani dark blue hoodie yasaka da gajeren wando iya gwuiwa milk, ya sanya eye glasses dinshi sanan ya feffesa turare yafito kafafunshi sanye cikin wasu navy blue designers crocs simple kayan zZama gida but still ka kalleshi saika kara kalloOnshi suka fito daga side din Zayn din tare.
2️⃣0️⃣
Side din Mami suka wuce, Mami na zaune a falo tana magana da Mama awaya suka shigo ganinsu tare yasa ta hararesu tacigaba da wayanta zama kusada Mami Alhaji yayi yana kallonta sabida tai kyau taci gayu sosai cikin kace kai kyau, katse wayan tayi takalleshi tace “ne kake kallona haka” cikeda tsokana yace “wai ke baki tsufa ne jibeki saikace ba kene kika haifi wannan gansamemen saurayin ba” yanuna Zayn, dan dariya Mami tayi tace “I take that as a compliment” “ina Farrah”? Alhaji ya tambayeta anatse, murmushi tayi tace “tana sama nabarta cartoon take kallo a IPad dina, you need to see yanda maganan ta ke improving Alhaji, one thing I like about her is she is fearless tanada kwazo da jajircewa” murmushi Alhaji yayi yace “kiramin ita” tashi Mami tayi tai sama bata wani jimaba suka shiga saukowa tareda Farrah, tana sanye da doguwan riga na atampa brown dinkin yamata das das ajiki sai dan kwalinshi data daura aka kanta na kasa wani kunya taji tanaji ita Mami tafiso da Mami kawai tasaki jiki saukowa kasa sukayi Mami ta zaunar da ita kan kujera kusada ita kasa zama tayi tazame jikinta ta zauna akasa da sauri kanta na kasa tashiga wasa da yatsunta Dan dariyan manya Alhaji yayi yace “Farrah yaya jikin? Wajen dinkin yadaina zafi”? Gyadama Alhaji kai tayi ahankali cikin zazzakan muryanta tace “eh…..Ab….ba” jinjina kai Alhaji yayi yana murmushi yace “Masha Allah, ga muryanki nan Tubarkallah Allah kara sauki” “Farrah” yasake kiranta anatse hakan yasa ahankali tadago kanta ta kalleshi, ajiyan zuciya Alhaji yasaki, yace “kingan ni nine mahaifin Zayn, mijin Mamin ku, da Mariya da Fatima da Maryam, Zayn kadai Allah yabani, rana daya kuma Allah yakawoki cikin rayuwan mu, akwai abinda yasa nasaka aka kiraki, inaso na tambayeki ne naji amsanki kafin nai komi” yasakeyin shiru sanan ahankali yace “Farrah kawunki ya sanar damu ke marainya ce, matata nan Maman Zayn likita ce, itace tamiki aiki a operation, taga tabo da dama ajikinki wanda yake nuna na alamun duka ne, yanzu inaso namiki wani tambaya banso kimin karya kinji” gyadama Alhaji kai tayi ahankali, anatse Alhaji yace “wanene yasamiki garwashin wuta abaki?” Shiru tayi gabanta nafaduwa dum dum, dafata Mami tayi ahankali tace “kada kiji tsoro ki yayi gaskiya kinji” gyadama Mami kai tayi sanan takalli Dad, batasan ya akayiba kasa karya tayi ahankali tace “In…na” “Matar kawunki”? Gyadama Alhaji kai tayi tace “eh””ita ke dukanki ma”? Gyadama Alhaji kai tayi takai bayan hannunta dasauri tashare hawayen daya zubomata, shiru dakin yayi Alhaji na kallonta, murya chan kasa yace “akwai abinda ake cema adoption aturence, yana nufin zaki dawo diyata ni da Mami da kotu tabamu mune custodian naki, kula dake yafita daga hannun su kawunki yadawo hannunmu dundundun ki dawo yarmu musaki amakaranta da sauran su, nakira lawyer na halama ya iso yanzu, yanzu hakama kawunki da matarshi na gidan nan chan bangaren baki, amman so naki nafara jin bakin ki kafin nasa akawo kowa nan, Farrah” Alhaji yakirata ahankali murya chan kasa tace “Na’am” ahankali yace “kin yarda ni da Mami muzama iyayenki?” Wasu kalan hawaye ne suka cika idanunta, tunda take baa taba bata daraja da mahimmaci dahar za’a zaunar da ita atamabayi yardanta Awani abu ba sai yau, tunda tahadu da mutanen nan sunada kirki sosai, batada kowa aduniyan nan banda kawu shi kadai gareta amman shima baya sonta baya kaunarta agabanshi aka kashe mata yar uwa baice komiba, dafata Mami tayi dasauri ta kalli Mami, Gyadamata kai Mami tayi alamun tace “eh” ahankali tace “eh Abba” rungumeta Mami tayi tana share mata fuska tace “daina kuka to” sai alokacin Zayn yadan saci kallonta, fuskanta na jikin Mami tana goge hawayen dasuka zubomata kaman ance ta kalleshi hada idanu sukayi da Zayn din hararanshi tayi tareda dauke kai.
Dauke kai shima Zayn yayi dasauri yana regretting kallonta ma dayayi waya Alhaji yayi sanan ya katse wayan yakalli Mami yace “tafi da ita sama”.