← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 94

Sashe 19

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Juyawa baya Farrah tayi dan hakanan jikinta yabata wani abu, wani katon dutse Lamido ya dauka yawani jefo musu yayo saitin Zayn, cikin zafin nama tasaki hannun Zayn karyayye sanan tawani fada kirjinshi ta kankame shi tareda juyarda shi ita tadawo saitin dutsen, dutsen ya sauka akan bayanta wani kalan mugun kara tayi dan har kirjinta taji dutsen ta kankame Zayn sosai dashi kanshi saida yaji yanda dutsen ya daketa akirjinshi sanan ahankali tadago fuskanta ta kalleshi hada idanu sukayi shima kallonta yayi da idanunshi daya dayake iya amfani dashi, ahankali tasakeshi sanan yafita daga kirjinshi sanan tawani juya takalli Lamido dake tahowa yana dariya yace “Au kin tsaya kin ci saa bullets dina sun kare da wlh nai wasting rayuwanki, Shegiya akwai, sai shegen wayau uwa yar dula” dan murmushi tayi da kyar sanan ta tsugunna kasa ahankali dutsen daya jefomata ta dauka sanan ta kalleshi yana dunfaro su yana tafiya yana dan dingishi saitashi tayi tadage da duka karfinta jefamai dutsen tayi dudda yaso ya kauce amman saida dutsen ya sauka akan goshinshi haba sai jini, wani kalan tsalle Farrah tayi tareda mai gwalo dayasa Zayn yadan ware idanunshi cikeda mamaki, dan juyowa tayi takalli Zayn dake tsaye yana kallonta kaman yasami tv baki tabude kaman zatamai magana jin sahun gudu yasa duk suka kalli wajen, su Oga kezuwa but still sunada nisa hannun Zayn mara lafiyan takama suka shiga gudu daga ita har shi wanan karan yamafi na dazu, sunyi gudu nakusan 10min sanan suka kai wajen wani rami da bishiyoyi suka kare bazaka taba sani da rami a wajen ba, tsayawa gaban ramin tayi tana haki sosai sanan tasaki Zayn tanunamai ramin da hannu alamun ya shiga, ramin ya kalla sanan yakalleta dan bola nema cikin ramin, sake nunamai tayi tana kallon bayansu dan yanzun nan su Oga zasu cimmusu ganin inda take kallo shima baison akamasu yasa yashiga ya tsugunna yana taushe hanci amai na tasomai, juyawa tayi da sauri ganin ya shiga ciki zuwa gaban wani bishiyan mangwaro duk Zayn na kallonta wani kalan tsalle tayi tahau bishiyan sanan ta karyo babban reshe dakeda ganyayyaki da mangwaro nunannu ajikinsu, da wasu different itace sanan ta dirko kasa ta taho da gudu fadawa cikin ramin tayi daidai su Oga sun karaso wajajen ahankali tasa reshen tarufe saman ramin dasuke ciki, ganyayyakin suka rufesu sanan ahankali tajuyo takalli fuskan Zayn dake kallonta, hannunta ahankali takai tadaura kan lips dinta alamun yay shiru, samin kanshi yayi da gyadamata kai ahankali kaman wani obedient child, sanan takalli hannunshi dataga yadaura hannunshi mai lafiya akai yarike kana gani kasan hannun azaba yakemai, ijiye itacen data karyo daga bishiyan tayi akan jikinta sanan takai hannayenta ta kwance igiyan hulanta tacire hulan shima ta ijiye akasa, ahankali tasaka hannunta tazame dan kwalin atamapan dake kanta wani kalan zubewa tulin churdadden gashinta yayi daba gyara abaya da Zayn yagani yana taba har kasan wajen dasuke zaune, ko kadan bata damuwa, yaga dan kwalin yaga tayi tararaba shi, sanan tadago kanta takalleshi hada idanu sukayi ahankali takalli monkey jacket din dake saman white shirt din dake jikinshi, da hannu ta nunamai monkey jacket din sanan tamai alamu yacire kallonta yayi dan baigane metake cewaba, hakan yasa ta daura hannunta kan jacket din tadan ja alamun yacire, dan yunkurowa yayi sanan yacire da kyar yabata, karba tayi sanan ta dukunkune rigan takai saman bakinshi duk yana binta da idanu, sanan takama hannunshi mai lafiya tadaura akan rigan asaman bakinshi sanan tanunamai saman ramin dakuma nunamai alamu yay shiru ma’ana kada yay ihu ya taushe bakinshi kada mutanen nan suzo sujisu, sanan ahankali yaga tasaka duka hannayenta kan hannunshi karyayye takama runtse idanunshi gam yayi koyaya aka taba hannun shi kadai yasan yanda yakeji, ahankali take taba hannun ta lumshe idanunta, ta iya gyara karaya awajen maman ta takoya, Mamanta na gyara karaya sosai kusan shine ma aikin datakeyi a birni ana biyanta tana dauri agida, ita kawai gani tayi ta iya a kauyen nan tama mutane biyu dauri kuma sun warke, gano karayan tayi hakan yasa ta bude idanunta tadauki itacen data ijiye akasa ta daura kan jikinta sanan tawani kalan murde hannunshi tahade kashin dayasa yay wani ihu bakinshi taushe gumi na ketomai tako’ina, sanan ta jera itacen tass kafin tasaka igiyoyin dan kwalinta ta daure hannun layi layi tam tam, sanan tasaki hannun nashi ahankali bude idanunshi yayi yakalleta harta dauki hulanta tana daurawa akanta tana kulle igiyan a gemunta, dayan igiyan daya rage ta dauka shi yanada fadi sanan ta kalleshi bayan tagama gyara zaman hulanta, tasowa tayi tazo da gabanshi takalleshi sanan tadaura hannunta daya kan idanumta, kafin ahankali takai igiyan tadaura ma idon mara lafiya tadaurea kullin abayan kanshi sanan takoma tazauna, wani kalan dadi yaji da idon namai kaman zai fadi yanzu saiyaji kaman abu yatare idon daga fadi, ahankali yakalli hannunshi dudda yanamai zugi sosai but he’s feeling much better kan dazu……… ”bazasu taba wuce nan wajen ba kuduba dajin nan tass, duk inda za’agan su agansu, inba hakaba saina kashe kowa na kauyen su dan nasan daga rugar fulanin chan take, itane kaje kagani jiya da daddare Lamido” dasauri Lamido yace “a’a Oga, ni wata bazawara nasamu Oga”.

This book is 500 VIP is 2k
3107021073 aisha Muhammad first bank pay and chat me up by clicking on this link;
wa.me/+2347012181461

💫 FARRAH💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 1️⃣1️⃣
Cikin tsananin fushi dakuma tashin hankali Oga yace “Duk inda zaku shiga ku shiga kufito min da yaron nan, that boy life is our golden ticket to paradise” baisan ya akayi ba but jiyayi yasa hannu yakama hannun Farrah gam gam atsorace jin maganan da Oga keyi kirjinshi na bugawa dum dum dum! Ahankali Farrah takalli hannunta dataji ya kama yarike kafin gently tadago manyan idanunta takalli fuskanshi, ko kadan hankalinshi baya kanta fuskanshi na kallon sama dan asaman kansu yakejin maganansu gani yake kaman zasuyi missing step kawai su taka reshen mangwaron su fado cikin ramin dasuke su gansu su kasheshi, zufan dakebin gefen fuskanshi ta kalla dan murmushi tasaki tunda tai wayau yaune rana na farko data taba haduwa da namiji matsoraci, ko Baffa dayake nan siriri baikai Inna kiba ba baida tsoro, rashin mutuncin yake surfafama Inna dudda idanma duka ne zata iya zauneshi ma amman baya tsoron ta balle uban kowa, su Moddibo dabama sukai wannan girma ba suma basuda tsoro amman jibi wanan katon yanda jikinshi ke rawa, tabe baki tayi tadauke kai batare data cire hannunshi daga kan hannunta ba ta jingina da bangon ramin hankalinta kwance ta lumshe idanu dan wani kalan baccin gajiya takeji ko minti uku batayi ba bacci yay awon gaba da ita azaunen, minsharin dayaji taja yasa dasauri yajuyo da kanshi ya kalleta bacci take azaune bayanta jingine da bango tadan dukar da kanta hakan yasa bama ya iya ganin fuskanta sai saman hulanta, mamaki ne ya kasheshi how can she sleep comfortably acikin rami akan wanan dattin? Yana nan inda yake yanajin duka neme nemen shi dasukeyi aka wani kalan tsuge da ruwan sama dayasa yaji sun kwasa dagudu, kalan azababben kishin dayakeji yasa yabude bakinshi ahankali yanajin wani iri but ji yake idan baisha ruwan nan ba zai iya mutuwa, ruwan dake tsiyaya daga ganyayyakin nashiga bakinshi yana hadiya ahaka, saukan ruwan dataji kan fuskanta yasa tabude idanunta ahankali kafin taja hulanta baya tadago kanta ta kalleshi ruwa na fesowa a fuskanta shima kallonta yake, saikuma chan yamaida bakinshi yarufe ganin kaman yanda takeshan ruwan yake kallo, dan yunkurowa kadan tayi taja reshen gefe ta lelleka ganin basanan yasa ta matsar dashi gefe tafito sanan ta tsugunna gaban ramin tamikamai hannu ahankali yakalli hannun nata sanan gently yasaka mata nashi aciki yafito ahankali da taimakonta, mangwaron su ta katse daga jikin reshen sanan tamikamai guda daya kallon mangon yayi sanan yakalli reshen da bolan da aka rufe dasu yanajin amai na zuwan mai tuna ruwan dayasha amman aman yaki zuwa sanan ya girgiza mata kai, maida mangwaron tayi tarike tafara shan nata dan rawa yafara na sanyi dan ruwa ake mai karfin gaske ita ko ajikinta, tafiya tafara da sauri shima yabita yana tafiya da sauri har zuwa gaban dutsenta hawa sukayi sanan suka shiga kogon, waje tanunamai hakan yasa ya zauna akasan ahankali fita gaban kogon tayi sai yanzun nema gabanta yafadi duka tumakan su Shanu daya kawai tagani awajen yana yawo, wani irin kalan mugun faduwa gabanta keyi, dawowa ciki tayi ta zauna sanan ta kalleshi kaman yanda yake kallonta batace mai komi ba.
Chapter 19 · 0% Book details