Sashe 11
Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****
Har sukakai kofar gidansu Shafa bata cemata komiba kan dakalin dake kofar gidan Shafa ta zauna tace “jeki juye ruwan kifito” ciki tawuce taje tajuye ruwan tafito rike da empty tulun tana kokarin daurawa aka Shafa tamike tasa hannu ta fizge tulun cikin fushi tai gaba tace “bazaki kara komawa rafin nan ba muje gidan mu nabaki ruwan mu kikai” tai gaba dasauri Farrah ke binta har zuwa gidan su babu kowa agidan ko’ina tsaf tsaf saida sukaje gaban babban randansu sanan Shafa ta sauke tulun tashiga deban ruwa tana zubawa aciki gabanta Farrah taje ahankali tamika mata biscuit din alamun ta amsa wani kalan mugun kallo Shafa ta mata saikuma cikeda masifa ta yarda kofin datake deban ruwa dashi ta kalli Farrah tace “waike maisa wawiyace ke kurma eh? Kinfiso ayita cin zalunki aduniyan nan? Maisa bazaki tsayawa kanki ba sabida kinga bakida kowa bakida gata ke barakima kanki gata ba iyye? Ni wlh abin namin ciwo idan ana cin zalinki abin namin ciwo” kawai Shafa tadaura hannuwanta biyu akan fuskanta sabida kukan dataji yazo mata dasauri bataso taga ana zaluntar Kurman nan har cikin zuciyanta takejin abin, wani irin sanyi jikin Farrah yayi ganin Shafa na kuka bata taba ganin Shafa na kuka ba sai yau yarda biscuit din tayi akasa sanan ahankali takai hannunta tacire hannun Shafa dake kan idanunta tasaukar da su kasa hawaye na fitowa daga idanunta kaman yanda Shafa itama hawaye ke zubowa daga idanunta dawani irin sauri ta rungume Shafa tana kuka sosai, sunkai kusan minti biyu dukansu suna kuka da kyar Shafa ta hadiye nata takai hannunta tashare fuskanta sanan tadago Farrah daga jikinta tana kallon yanda take kuka tace “dalla to ai nadena kukan kema kidaina” girgiza mata kai Farrah tayi tana kuka, ahankali Shafa takai hannunta tagoge mata fuska tace “karki damu watarana sai labari kinji, Allah shine masanin gobe Kurma ke marainiya ce bakida uwa bakida uba kokuma ince babu wanda yasan ubanki, duk wanda yaci zalin maraya zaiga sakayya kiyakuri kinji amman kuma daga yanzu zaki dinga tsayawa kanki kinajina” dasauri Kurman ta Gyadamata kai, hannunta Shafa takama taja zuwa dakinsu madubi tadauko suka fito waje sanan ta kama hannun Kurman tasamata madubin aciki tace “kalli kanki kurma, tunda nake akauyen nan bantaba ganin yarinya mai kyau kyakkywa datafi kowa gashi ba dudda muna karkaran fulani kowa nada gashi amman kinfi kowa tashi irin ki ba, kalli yanda suka zamar da ke, kalli jikinki” Shafa taja wuyan riganta ta bude shoulder nata duk tabon duka, tace “ke mace ce kinga Inna tana cemin baikamata diya mace nada tabo ajikinta ba sabida zatai aure, miji bayason tabo ajikin matarshi, su Rakiya da Mamanta na neman lalataki, su wulakantaki sabida sunga bakida kowa amman basusan kinada Allah ba sanan kinada ni, karki kara yarda wani yadakeki kinji, kinada wayau gaki da Basira da kwanya kurma nihar tsoro kike bani wani zubin kada ki kara bari kowa yaci zalinki kinji, inhar kina sona kimin alkawari, kinmin alkawari zaki dinga tsayawa kanki ki zama jaruma?” Dasauri Farrah ta Gyadamata kai hakan yasa Shafa tai wani murmushin jin dadi tace “kokefa, zo muje kigani” kitchen dinsu suka shiga Shafa ta kwaso barkono da attarugu duk Farrah na kallonta zubawa tayi a turmi ta daddaka yau laushi sanan takawo ruwa ta zuba itadai Farrah na kallonta Dakinsu ta shiga tadauko wata container na turare ta bude ta zubar da turaren saida Farrah tabude baki sanan ta dauko lariya ta tace kayan miyan, ruwan ta dauka ta dura a goran yacika tam sanan ta rufe ta tashi tazo tamikama Farrah tace “gashi kidinga sokewa gefen zanin ki, duk wanda zai cuceki ki dauko ki fesamai a fuska kigudu wanan shine makaminki daga yau kinji” karba tayi dasauri tana jujjuya goran tana murmushi sanan tadago takalli Shafa baki tabude zatai magana hararanta shafa tayi tace “wlh kika batamin suna saikin sani, banson godiya ni bance ki magana ba kafin dan makogoronki ya yage” dariya Farrah tayi sosai sanan tahau tsalle tana kallon goran itakuma Shafa tashiga maida komi sanan tadebo musu tuwo zama tayi taci abinci ita kanta Shafan barmata tayi ganin yanda takejin yunwa saida ta cinye sanan suka sha ruwa suka tashi Shafa tace “kome Moddibo zai baki kadaki sake kici bakisan barbaden mezai miki ba” Gyadamata kai tayi sanan Shafa ta daukan mata ruwan suka wuce suka fita awaje suka bama yara biscuit din har gida Shafa tarakata awaje tabata tulun sanan tamata saida safe itakuma ta shige gida ta juye ruwan zata kara fita Malam dake alwala yace “ke wuce gobe dasafe kya karasa cike komi mangariba tayi jeki salla” Inna dake iza wuta tai kwafa batace komiba.
.
💫 FARRAH💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 5️⃣
Gaban wani simple madaidaicin gida bodyguard din yay parking gidan nada normal kofa babu gate sanan ga dakali a kofar gidan dayasha simenti, budemai kofa bodyguard din yayi yakai kusan 10min ko motsi baiyiba sai daddanna wayanshi dayakeyi sanan daga bisani yadan yunkara yasauko ahankali sanan yashiga cikin gidan yana yatsine fuska dan gidan tsoro yake bashi sabida akwai yana yana shifa gidaje marasa kyau ba irin gidansu dayake nan glass house ba tsoro suke bashi, dayake magrib yayi duhu yasomayi duk wuta akunne suke, tsakar gidan ya shiga da tabarma kenan a shimfide babba ga dadduma akai wata mata datadan tsufa nakan dadduman zaune da hijabi da charbi a hannu saikuma wata mata haka dake goye da yaro a baya tana gaban murhu tana tuka tuwo ganin Zayn yasa tace “Zayn nake gani haka koko idanuna ne Innalillahi Zayn wai mekakeci kake kara girma haka?” Kallo daya yamata yadauke kai yakarasa inda Kakarshi take batare daya cire takalmin kafanshi ba yahau kan tabarman yakasa zama yana kallon Kakarshi dake kama da Mami shi sosai dake addu’a daidainan ta shafa sanan tadago kanta ahankali cikeda murmushi ta kalleshi cikin hali irin na manya masu kuma kamala ta jaye gefe kadan dagakan clean lallausan dadduman ta sanan ta nunamai wajen tareda mikamai hannu tace “tahonan ka zauna dan Albarka amman kada katakamini dadduma da takalmin ka” tai maganan tana kama hannunshi hakan yasa ahankali yazauna kan dadduman yana matsawa gaba da sauri dan bayason bayanshi Ya jingina da bango cikin hausanshi datake nan kaman yana turenci tsabagen gayu da zama akasan wajen yace “kidawo gidan mu old lady, this house is scary” sosai take kallonshi daga yanda yake maganan yana kalle kalle kasan dagaske gidan nabashi tsoro ko kadan Zayn baisan menene wahalan rayuwa ba gidanta gidane mai kyau tsaf tsaf Mami tayi tayi ta chanza mata gida tace “a’a ita agidan da mijinta yamutu ya barmata zata mutu itama, Mami na gyara gidan sosai gidan tsaf tsaf naida wani aibu ko makusa, tanason jikanta saisa ita karan kanta tadage da addu’a akanshi Allah ubangiji ya shiryamin mata dashi, murmushi tayi sanan takai hannunta kan fuskanshi tace “waini kazo gaidawa ko gidan nan sai wani kalle kalle kake agidan mezai zo Ya cijeka bayan ina tareda kai anan, ka gaida Lami kuwa Matar Kawu, kaga kayi kani ma, gaidata” ko kallon inda Kakan shi ke nunamai bai kalla ba, murya chan ciki yace “ina yini” dasauri matan ta amsa tace “sannu Zayn anzo lpy” bai amsata ba saima Kakannshi daya kalla yace “zan tafi Old Lady” hararanshi tayi tana dunguremai kai tace “waikai haka ake zuwa gaidani baka iya zama kaman ana koranka ka tsaya kaci abinci” girgiza mata kai yayi yana yatsine fuska y dasauri tace “namaka dambun nama fa ko har shima bakaso” for the first time tunda yashigo gidan yasaki murmushi hakan yasa ta mike tace “ai nasan Zayn da dambun nama na da aakacemin kadawo dakaina namaka dazu dan nasan zakazo duba ni bari nadauko maka” tai maganan tana shiga dakinta, wani roba ta dauko na dambun nama tafito dashi yana tsaye yana jiranta bashi tayi ahankali ya karba yana budewa yadeba yakai baki yaci yanadan murmushi batare dayace thank u ba yace “bye Old lady” ahankali tace “sai gobe Dan Albarka” tabi bayanshi da kallo harya zaure, tadade tsaye ahaka harsaida Lami tace “Mama” ajiyan zuciya tasauke sanan ta taho ahankali tazauna tace “Lami ina matukar yima Zayn addu’an shiriya, yaron nan baisan komi kan rayuwa ba banda jin dadi, bai iya godiya ba, ko daraja dan adam ba, kawai wayanda yakeso, yakuma sani aduniyan nan daga mahaifinshi sai mahaifiyar shi sai ni kuma, banda mu ukun nan kowa wulakantacce ne awajenshi, mu dinma dayake so Wanan zuwan minti dayan shine matukar so awurinshi, Lami jibi yanda jikana yakoma jibi kalan dake gemunshi jibi kalan kayan yahudawan dake jikinshi Ya Allah ka kawomana Wanan saukin jarabawan, iya abinda nasani shine tunda har mahaifinshi ya tursasashi aka dawo dashi Nigeria da karfi da yaji to shiriyan tazo kenan, Wanan shine mataki na farko ahankali ahankali zaka dawo yaro nagani Zayn, Allah ubangiji ya dubamini lamarin ka” ahankali Lami ta amsa da Ameen sanan takawo musu tuwon dan suci.
Mota yashige bodyguard suka rufe motan ko kadan he’s not happy, and nobody understands him a family shi, he don’t like Nigeria ko kadan, komi na Nigeria is boring, yariga yasaba rayuwan kasan waje, all his friends are there, gawajajen hutawa daban daban, ga mata, matan kasan waje sunfi na Nigeria yan kauye saisa bamasa burgeshi ko kadan, ya bala’in jin bakin cikin yanda Papa yasa aka je da karfi da yaji aka daukoshi aka dawo dashi Nigeria kuma saiya rama, saiya mishi abinda saiya gwammace yamaidashi kasan wajen daya zauna a Nigeria, wani kalan murmushi yayi take yaji zuciyanshi yayi wani kalan sanyi.