← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 94

Sashe 28

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Parking tayi abangarenta tafito, wata doguwan kyakkyawan budurwa ce tafito daga babban flat dinta, fara ce ita kal yarinyar tana sanye da jeans da riga babu dan kwali akanta tayi kitso da aka kara da attachment kalan blond daya sauko har waist nata, tana zuwa batai wata wata ba ta rungume Hajiya Mariya tace “oyoyooo Mommy” rungumeta back hajiyan tayi tace “oyoyo my baby girl, my Lailarosh, how are you”? Murmushi tayi tabude baki zatai magana aka bude gate din gidan, kallo daya Hajiya tama motar Mami tadauke kai tacigaba da kallon Layla tace “how was your flight”? Murmushi tayi tace “fine” daidai motan Mami yay parking kusada na Hajiya saukowa bodyguard yayi yazo dasauri yabude ma Mami kofa tafito Farrah ma na fitowa, daidai lokacin kuma motan Zayn ya dannokai cikin gidan shima, ganin Hajiya Mariya yasa Mami data kama hannun Farrah wacce daga Hajiya har Layla kallonta suke tace “Hajiya barka da rana” murmushi Hajiya ta kakalo tace “Barkan mu dai Mami ya Zayn da jiki hope bai makance ba” dan murmushi Mami tayi tace “Alhamdulillah komi yazo dasauki” kallo Hajiya tabi Farrah dashi tace “wanan kuma fa daga ina” tama Farrah wani kallon wulakanci, Farrah Mami takalla tana murmushi tace “itace Farrah, yarinyar data taimaki Zayn, she is going to stay damu for now, she don’t speak hakanan” jan Farrah Mami tayi ajikinta cikeda so tace “Farrah gaida Hajiya” ahankali Farrah kanta akasa dan batasan mesaba batason kallon da Hajiya kemata tace “i……i….ina…….yi…ni” Zayn da fitowanshi daga motanshi kenan dan satan kallon Farrah yayi dayaji tai magana da kyar baisan mesa ba but har cikin zuciyanshi yaji muryan nata, dauke kai yayi batare daya kara kallonsu ba yawuce zaije side nashi kaman jira Hajiya Mariya take tace “Zayn ga friend namaka her name is Layla” wani kalan juyowa yayi yakalli Hajiya yatsine fuska yayi irin nagayamiki I need friend ne sanan yajuya cikeda bacin rai zai wuce, da kakkausan murya Mami tace “Zayn” chak ya tsaya sanan yajuyo ahankali sai alokacin yadan kalli Layla dake kallonshi kaman zata cinyeshi batare dayay magana ba, dasauri hajiya ta tabata tace “bazaki gaida yayanki ba” murmushi Layla tayi cikeda siyasa tace “Hello Zayn” adikile yace “Hey” sanan yajuya yawuce, murmushi Hajiya tayi tace “itace diyar kanina daya rasu yabari shes 21 tagama school a england” kallonta Mami tayi kana ganin Layla kasan tafi 21, kabata 25/26 dan zata iya zama mate din Zayn kawai Zayn yafita girman jiki ne, dan murmushi Mami tayi tace “bari nakai mara lafiya ciki” takalli Layla cikeda wasa tace “sai kinzo tayani hira” sanan takama Farrah dakebin gidan da kallo tawuce side dinsu.

Side dinsu suka shiga wanan karan Mami saida tai dariyan yanda Farrah ke kallon komi kamata tayi sukai sama tace “muje nakaiki dakin ki saiki wanka, za’a kawomiki abinci, kika gama zanzo nabaki magani da allura, kome kikeso kifada min zan sa amiki, ki dauki gidan nan kaman gidanku sanan kidauke ni kaman mahaifiyar ki ki saki jikinki kinji” sukai maganan daidai suna shiga wani lafiyayyen daki mai bala’in kyau kan gado takai Farrah tace “nan ne dakin ki, ga bayi nan” Mami ta nuna mata bayin, sanan tanuna mata wardrobe tace “kowani kalan kaya kikeso kisa yana nan, yau dasafe nasa aka sayo kaya aka sassaka miki aciki, bari naje nabaki wuri ko, kiyi sauri ki gama kisha magani” Mami tai maganan tana juyawa zata fita, wani abu Farrah taji ya tsayamata awuya, ahankali tashiga bude bakinta dake wani kalan rawa yana shaking murya chan kasa sosai tace “Maaaami” for the first time Mami taji muryan Farrah yadaki zuciyanta dawani kalan sauri Mami tajuyo, hawaye taga Farrah tasa hannu tashare daga kan fuskanta sanan ahankali tamike daga kan gadon, dawani kalan sauri tazo wajen Mami batai wata wata ba tawani fada jikin Mami sai kuka, sosai take kuka har saida Mami ta tsorata tace “Subhanallahi Farrah menene kike kuka haka” kankameta Farrah tayi tana kuka sosai, fuskanta na jikinta ahankali tace “Mami naa…….gode” hawaye Mami taji sunzo mata idanu dasauri ta hadiye hawayen taciro Farrah daga jikinta, hararan fuskan Farrah tayi sanan tasa hannunta ta goge hawayen dasuka jika mata fuska, bawasa kan fuskanta tace “koda wasa kada ki kara cemin kin gode Farrah ni Maman kice, badan sabida ki taimaki Zayn nake all this ba, hakanan ko Allah yaga zuciyata kawai ina sonki Farrah, I look at you kaman baby girl dana dade nake kwadayi Allah yabani finally yakawomin ke, sOo yanzu imaza maza kiyi wanka” Mami tai maganan tana kama hannunta zuwa bayJi, kunna mata ruwa tayi sanan tafice.

1️⃣9️⃣
Tsaf tayi wanka dan tanada karfin hali, tariga tasaba duk dukkan daza’amata dole tai aiki, fitowa tayi daga bayin ta shirya, dadduman dataga an shimfida mata yana kallon gabas tahau ta tafara salla addu’a tayi cikin salla kan Allah ya zaba mata abinda yami mata alkhairi arayuwanta.
Chapter 28 · 0% Book details