← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 94

Sashe 55

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Assalam Zayn!” Yaji anmai magana ana shafa kafadanshi dasauri yadago kanshi wani Indian imam dinsu ne na masallacin nan, yanama Dad aiki ustaz ne sosai, dan murmushi Zayn yamai batare daya amsashi ba, zama Imam din yayi agabanshi tareda lankwashe kafa yasha ganin Zayn company nan ma waye baisan labarin Zayn only yaron Ganuwa ba saidai idan baka company nan, anatse yace “what’s the matter Zayn”? Shiru Zayn yayi yana kallon mutumin he’s elderly dan akalla yayi sa’an Uncle kuma malami ne nagidi, at least baitabama kowa magana ba outside parents nashi baida aboki yamai magana ne, yay shiru dan murmushi Imam din yayi yace “you can always talk to Me Zayn dudda nasan I am nobody zan iya taimaka maka da shawarwari” yay maganan anatse hakan yasa Zayn yaji kawai ya yarda dashi ahankali yadan cije lips sanan yasaki lips din murya kasa kasa ta yanda kowani yashigo masallacin bazai jisuba yace “Imam I am a bad boy I know you know that cus you work here” yadanyi shiru sanan yace “my parents are not happy with me, I am trying to change but kasan menene matsala na I don’t think I can leave without women” yadan yatsine fuska dan iyakan gaskiyanshi yake fadi yace “ni baran iya 2-3days without a woman ba before banama iya one day saida nadawo Nigeria ne nazo nafara koya da kyar murya chan kasa yace what do I do”? Anatse Imam yace “kodai ka dunga azumi kokuma kai aure sabida kadinga samin natsuwa daga wajen iyalinka” dan shiru Zayn yayi yana kallonshi batare dayace wani abuba hakan yasa Imam yace “kanada wacce kakeso”? Shiru Zayn yayi saikuma ahankali yadan fuzarda iska Farrah na fadomai arai yace “I don’t know, ni banmasan ko inada wanda nakeso ba all I know is kamin tambayan nan is one person yafado raina Farrah and she hates me cus ta taba ganina da wata” yasake maganan yana yatsine fuska, dan murmushi Imam yayi yasaka hannayenshi biyu yakamo hannayen Zayn anatse yace “yaune rana na farko dana taba zama na magana dakai and all I see was myself lokacin danake da shekarun ka, I was once in your position Zayn duk wani rashinji daka sani nayishi aduniyan nan but rana daya shiriya tazomini sabida question din is menene amfanin been a bad boy can you answer this question Zayn”? Ahankali Zayn ya girgizamai kai, murmushi Imam yayi yace “is not easy kabar komi da komi tashi daya but idan kai niyya kazo kafara bautama Allah da kyau he will help you, and yama baka the greatest reward by giving you the best woman” yasake murmushi yace “ingaya maka ta yanda zaka gane you are in love with someone Zayn”? Dasauri Zayn ya gyadamai kai, dan murmushi Imam yayi yace “when you care for them genuinely, baka iya jure tsana daga wajensu, u can’t stand hurting them kokuma kaga ana hurting nasu, you love seeing them happy, kuma kawai kaji kanamusu wani kulawa na musamman is love, and if this things are abubuwan dakakeji game da yarinyar daka fadimini tom you are in love with her Zayn” sosai Zayn yake kallonshi yama kasa magana, gyadamai kai Imam yayi yace “tashi ka koma aiki” gyadamai kai Zayn yayi yamike tsaye ahankali har lokacin jikinshi yay sanyi yawuce yakoma office koda yashiga kwanciya yayi kujera yay shiru tunanin Farrah kawai yake yana koran tunanin amman yakasa daina ahaka baiyi komiba yaji ankira la’asar hada tarkacenshi yayi yafito saida yafara ijiye jakan laptop din a motanshi sannan yawuce yatafi masallaci &ana idarwa yafito yashiga mota yawuce.

4️⃣8️⃣

Dagudu yake tuki as usual wani boutique yagani agefen titi da mannequin ansa musu kayan mata masu kyau sosai yaga sunmai kyau hakanan Farrah ne tafadomai arai, he’s trying to stop kanshi but gani kawai yayi yay kwana yay parking gaban shagon yashiga ciki, lafiyayyen english wears yashiga kwasan ma Farrah shirts da wanduna da gowns, yabiya kudi almost 300k masu shagon sai godiya sukemai yashiga motanshi yajawo motan zuwa gida.

Yauma kaman kullum exam din yau yamata dadi, zaune take a falo rikeda iPad din Mami wanda yanzu kusan koda yaushe yana tareda ita tana karatu dashi, Mami na kitchen dudda Farrah taso ta tayata girki kadota tayi tajetai karatun exam, hakan yasa tadawo falo tana zaune ta sanya wata Yar rigan kanti mai dogon hannu baka tanada zanen flowers farare ya tsayamata kasan gwuwanta kanta babu dan kwali sai kalaban data tufke da ribbon baki mai kyau, kaganta zaka dauka wata balarabiya ce zaune akatafaren falon, tana zaune ita kadai akan kujera da iPad din Mami a hannunta tana zane tana kallon zanen Amoeba 🦠 a iPad din tana zanawa da pencil a book din tana koyan lebelling dan gobe biology garesu gabaki daya hankalinta yay nisa a zanen, ahankali aka bude kofan falo aka shigo, Zayn ne yana rikeda katuwan ledan a hannunshi idanunshi akanta saikace tsafi ganinta kawai dayayi dudda ma bata ganshi ba jiyayi zuciyanshi tamai wani kalan sanyi tamai wani wasai now all he needs is tadan kalleshi and get all those her expression akan fuskanta.

Kamshin dataji yadaki hancinta wanda tasan kanshin Zayn kadaine yasa kaman wata Yar bera tadaina zanen datakeyi, duwawun pencil din hannunta takai bakinta sanan ahankali tadago kanta tareda juyowa hada idanu tayida Zayn daya tsaya yana kallonta kaman baitaba ganintaba ga katon jaka a hannunshi ga jakan laptop a dayan hannunshi yana kallonta, hakanan jitayi gabanta yadan fadi hakan yasa tadauke kanta daga kallonshi dasauri tana zare pencil din daga bakinta cikin kunkuni tace “mutum ko sallama bai iyabama” karasowa gabanta yayi ya tsaya dab da ita dan yanda ya tsaya akanta kafafunta nataba Yadin wandon jikinshi wani iri taji tanaji gabanta nafaduwa hakan yasa taki kallonshi drawing datake yabida kallo yace “look at abinda take zanawa kaman fuskanta” dawani sauri takalleshi zatai magana ya watsa mata mugun kallo yace “kawomin abinci I am hungry” hararanshi tayi ahankali tace “bara’a kawob…….” Daidai Mami nafitowa daga kitchen hakan yasa dasauri tabi ta gefenshi tai hanyar kitchen din tana kara budema Mami kofa da kyau tace “Mami sannu da aiki kawo nakai miki” kafin Mami tahanata ta karbe kulan takai dinning Mami takalli Zayn dayake shirin zama inda Farrah ta tashi tabari tace “kadawo” zama yayi ahankali yana daukan iPad din yace “yes Mami” “kaci abinci” dan yatsine fuska yayi yace “no” tasan dama baicika cin abinci ba hakan yasa takalli Farrah tace “kawomin serving spoon da tray a kitchen” dasauri Farrah tai kitchen ta dauko, seafood pasta da Mami tadafa lafiyayye tazubamai tahada a tray tasama Farrah a hannu tace “gashi kaimai kizo kidauki juice kikaimai ” karba Farrah tayi tawuce tazo ganin yawani kwanta kan kujeran data bari daga iPad dinta harda book dinta yajefar akasa yasa taji ranta yabaci ko kadan Zayn baida manners.
Ijiye tray abincin tayi akasa saida tray yay kara hakan yasa Zayn yadan bude idanu kadan yakalleta yanda tai da manyan idanunta kaman zata cije shi yasa yanuna mata small coffee stool nasu da yatsa in a very lazy voice yace “put the tray on that stool” hararanshi tayi tamike tsaye tana kwashe iPad din da book dinta daya Yar akasa sanan takalleshi cikedajin haushi tace “ina pencil dina”? Lumshe idanunshi yayi ahankali muryanta namai wani sanyi azuciya yana neman sakashi jin bacci, zatai magana daga kitchen Mami tace “idan kin bashi juice din kizo nan Farrah” dawani kalan sauri ta tashi ta ijiye iPad da littafin akan kujera tai dinning fresh juice din da Mami tahada ta dauko da cup suma a tray takawomai har lokacin yana kwance kan kujeran idanunshi a lumshe shima ijiyewa tayi akasa saida tray yay kara tamike tsaye jin baimata magana ba yasa tadan saci kallonshi idanunshi a lumshe kaman ma yay bacci wani irin bacci ne cikin 1min haka. “Did u put the food on the stool ko u are still looking at a fine boy” wani kalan ballamai harara tayi tana nadaman tsayawa ma kallonshi datayi sabida kawai Mami na kitchen yasa tajawo stool din tadauki tray tadaura mai abincin akai sanan tawuce batare data kalleshi ba zuwa kitchen.
Chapter 55 · 0% Book details