← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 94

Sashe 7

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tass yacinye abincin da Alhaji kebashi abaki dan Zayn nadacin abinci sosai ko maybe saisa ma yakeda tsayi oho, tissue Alhaji yasa ya gogemai baki tass sanan ahankali kaman zaiyi magana da jariri yace “ga step Moms dinka sunzo jeku gaisa” wani irin yatsine fuska yama Alhaji ashagwabe kaman baiso yay magana yace “I am tired Papa, I want to sleep, I can’t see them now” gyadamai kai dasauri Alhaji yayi yana shafa fuskanshi yace “to to shikenan, tashi muje kayi baccin ka” Alhaji yamike dasauri yana kama hannunshi zai dagashi, tashi tsaye yayi ahankali duk aka bisu da kallo suka taho falon babu wacce ta isheshi kallo cikinsu, Alhaji dake taredashi yakallesu yace “bacci Zayn yakeji yanzu, yagaji anjima kudawo ku gaidashi idan yatashi daga baccin” yay maganan yana kama hannunshi zasu fice daga dakin, Ummi jitayi ranta ya bala’in sosu no this is the limit dazata dauki iskancin Zayn, budemai kofa Alhaji yayi zai fita cikin kakkausan murya Ummi tace “Zayn!” Chak ya tsaya batare daya juyoba, cikeda fada Alhaji yakalleta yace “wai mekuma baraki barmin yaro yahuta ba”? Cikeda bacin rai Ummi tace “Alhaji enough please! Ba gata kake ma yaron nan ba wlh, iyayenshi ne nan zaune sun taso tundaga various bangare nasu sunzo nan dan sugaida Zayn wanda bahaka yakamata ba ai shine dansu shiya kamata yaje one after the other ya gaidasu iyayenshi ne, yanzu kuma sunzo sun gama jiranshi yace yagaji bacci yakeji su dawo anjima sabida zamanshi suke wani irin rashin da’a da tarbi……” Kul! Alhaji yafadi cikeda bacin rai yana nuna Ummi da yatsa yace “kada kisake ki kira yaro na mara tarbiya kafin kija bakinki yabishi, idan bakison yaron nan ne kigayamin zan daukomai the best Nany in this entire world dazata dinga kulamin dashi, inda ma na iya girki kin zaci zan bari d’ana yadingacin abincin wasu ne konaki ma? Jarabanki, masifanki, korafinki da damuwanki yasa Zayn bayason zaman gidan nan bayason dawowa Nigeria sabida kin tasashi agaba yi wanan bar wanan haba, kinsan irin wahalan danasha kafin nasamu ya yarda yadawo Nigeria, kinsan awa nawa yayi cikin jirgi yanzun nan yadawo yaci abinci yagaji yanajin bacci nace sudawo anjima su gaidashi barasu dawo bane! Akwai wanda ya isa yajadani cikinku ne, dukanku nan zaman mahaifinshi kuke, nace anjima adawo agaida Zayn akwai wanda ya isa yajadahakan ne!” Yabuga uban ihu dasauri Hajiya Hadiza tamike tana yake cikin makirci tace “Ahhh abu yay zafi Alhaji kamata hakuri, babu wanda ya isa yaja dakai, zaman ka mukeyi wlh! kasan Shafa’atu har yanzu yarinya ce, wani zubin gidan dakataso ma yana affecting mutum, kaga muda muka taso gidan masu shi munsan yanda akeji da yara, yaran mu sune number one kome sukeso yazauna, yan gidan talakawa dama haka suke sai hakuri, basusan menene ririta danda suka haifaba saidai su wulakanta shi, bama su iya son yaransu ba sabida basu taso cikin gata ba, Zayn yaje yay bacci abinshi anjima ma dawo, Zayn Son sorry kaji anata bata maka rai daga zuwanka, uwarka sai ahankali, Alhaji ayakuri dan Allah” yanda Alhaji yaji dadin magananta ko baisan lokacin daya tura hannunshi a aljihunshi yaciro key wata Babban jeep nashi that worth 70M yajefa mata yace “nabaki motata Hadiza” wani irin ihu tayi tazube akasa shikuma Alhaji yakama hannun Zayn dayadan saci kallon Ummi datai jugum azaune tana kallonshi suka wuce suka fita zuwa bangaren shi.

Tashi Hajiya Fatima tayi cikeda bakinciki da kishin Hajiya Hadiza tafice fuuu daga dakin, sanan itakuma Hajiya Maryam ta tashi tana dan kakalo murmushi tace “akashe lpy Hajiya Hadiza” sanan takalli Ummi tace “sai anjima Hajiya” Gyadamata kai kawai Ummi tayi takasa magana, saida tagama dariyanta Tsaf sanan tamike tsaye takalli Ummi daga sama har kasa tace “ohh’uhh ni wlh har tausayi kike bani dan banga banbancinki da mu dabamu haihunma Alhaji ba, da wanan haihuwa ai gwara bakayiba, yaro bayajin maganan ki baki isa dashi ba, baki isa ki tofa wani zance kanshi ba ubanshi ya hayayyako miki kina bani tausayi Ummi” tawani kwashe da dariya tana juya key motan hannunta tace “jibi kyautan motan dana samu Allahu Akbar” takara kecewa da dariya sanan takalleta tace “dan da ake mana gadara dashi ana daddaga mana kafada kalleshi, da inhaifi d’a dai irin danki Ummi gwara na mutu bantaba haihuwa ba, wai inata cewa danki, dan mijinki” tasake kecewa da dariya sanan tawuce tafita daga dakin tai waje Ummi jitayi hawaye sun saukomata daga idanu sharrrrr dasauri tasa hannu ta share, duk gidan nan kap itace tafito daga gidan talakawa, bayan tagama secondary school taci scholarship da Alhaji ke bayarwa every year taje takaranci medicine gynecology, ranan da tai graduating a ranan ne tafara ganin Alhaji sabida angayaceshi yazo yaga graduation na yaran dayabama scholarship kuma a ranan yaga Ummi yaji yanaso itace matarshi tabiyu, Hadiza ce babba sai ita sai Fatima sai Maryam ta karshe

💫 FARRAH💫

✍🏻M Shakur

4️⃣
Tadade zaune awajen sanan ta mike tsaye ahankali sama tawuce tana nunama yan aikin dinning alamun su gyara wajen tabude wani daki da cikinshi zaka dauka kana wata duniyan ne ta shiga ciki ta maida kofan tarufe, wayan ta dake kan gado ta dauka ahankali sanan ta zauna taciro number datai saving da Mama tai dialing ringing daya aka dauka daga ta dayan bangaren zaka iyajin murya wacce ta kwan biyu aduniya kaman muryan tsohuwa tace “Jikana ya iso Ummi?” Gyadakai tayi sanan ahankali tace “eh Mama, Zayn ya iso” muryanta kadai Mama taji tasan akwai wani abu dake damunta, cikeda kulawa dakuma damuwa tace “ke likita menene, meya faru”? Dan jim tayi sanan ahankali tace “Mama Allah yasani ina iyakan bakin kokarina wurin bama Zayn tarbiya amman Mama idan kinga Zayn ko saikin firgice, rashin jinshi dakika sani da bakomi bane yanzu ne yake asalin rashin ji, Mama Zayn yadada baci sama da da, Alhaji bayaganin hakan, soyayyan dayakema yaron ya makantar dashi, Mama kinsan ko yanzu kafin yadawo dinan Uncle yatura da bodyguards rututu akaje aka taho dashi da karfi da yaji shi kanshi mahaifin nashi fushi yake dashi, Mama Zayn baya kallon uban kowa da daraja ko mahimmaci hatta ni, Mama Zayn sai wulakanci da rashin da’a da………” “Ummi” Mama takirata cikeda natsuwa hakan yasa ta yanke magananta tace “Na’am Mama” ahankali Mama tace “Ummi nasha gayamiki yaro ba wani abu bane dazaki shiga shago kibada kalan design din dakikeso daza’a keramiki yazo miki ayanda kikeso ba, Yara sai wanda Allah yaga daman baka zai baka, iyawanshi ne, ni nan sama da kowa nasan yanda kike iyakan bakin kokarinki kan Zayn tun yana yaro nasani Ummi, dan haka abu daya zuwa biyu zan fada miki, yanzu dai inaso karki kara zubarmada Zayn hawaye, dan hawayenki zai iya binshi uwa ba abun wasa bane” gyadama Mama kai tayi ahankali Mama tace “ki dage da yima Zayn addu’a karki sake ki gaji, ki tabbatar sallolin dakikeyi na farilla sau biyar arana cikin kowacce saikinma Zayn addu’a, sai shawara ta biyu wanda manya kadai zasu iya baki shawaran nan, Ummi” ahankali tace “Na’am Mama” anatse Mama tace “ki kyautata ma wasu yaran, duk inda zakiga wani yaro dakeda bukatan wani abu na taimako koma wani iri ne inhar kinada shi to ki kyautata musu, sanan kimusu addu’a, duk addu’an dakikama wasu yaran malaiku zasuma naki, dan haka ki rike wanan sirrin da kyau ki kyautatama wasu yaran kisakasu farin ciki Allah zai iya amfani da wanan ya shiryan miki da naki dan kinjini ko” ahankali tace “eh” Mama tace “Allah yamiki Albarka, Allah yacigaba da daukakaki yasamiki albarka a aikin ki, Allah ya shiryarmiki da danki yamai albarka, bari na shiga gidan Safiya ta haihu zanma jariri wanka” murmushi tayi tace “Mama kedai da yima jarirai wanka baki gajiya, to Allah raya” Ameen Mama ta amsa sanan ta katse wayan, ahankali ta ijiye wayan kan gado tana sauke ijiyan zuciya jitayi duk wani nauyi da bakincikin datakeji azuciyanta yabace wato uwa daban ce, ita har mantawa ma take tayi girma wlh. Shiru takarayi tunanin Zayn nakara lullube fuskanta batasan mesa ba Alhaji gani yake ta tsani Zayn tana takuramai bata sonshi zata iya rantsewa da ace za’a tsaga zuciyanta a tsaga na Alhaji za’agani cewa son datakema Zayn yafi na Alhaji sau dubu, Zayn shine farin cikin rayuwanta, shine kadai abinda takedashi aduniya dazata kalla taji dadi, she loves her son a whole lot kawai bazata iya kyale kuskuren shi bane, huhhhh! Ajiyan zuciya ta sauke ahankali sanan tamike ta shiga bayi dan dauro alwala.
Chapter 7 · 0% Book details