← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 94

Sashe 61

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana gama paper ta tafito waje tazo tasamu guri a garden nasu ta zauna ita kadai tai shiru all abubuwan da Zayn yafadi mata dazu suna sake dawo mata akah, idan yana neman fadanta tasani but abubuwan daya fadi dazu tabata da akayi yasa dasauri tajuyo Miemie ne rikeda byro da question paper ta a hannu tace “wai meke damunki Farrah? I am you don’t ever tell me anything, ranan nan haka kikeso achool duk kinyi kuka nayi nayi kifadamin what happen kikace babu komi not until damukazo zamu fita kikaga motan Ya Zayn kikace fushi kike dashi, what’s the point of having a friend idan you cannot share problem dinki with them uhn” lunshe idanunta tayi sannan tabude ahankali bawai batason bama Miemie labari bane but gani kaman tafadama anybody halin Ya Zayn tana tonamai asiri ne, juyawa Miemie tayi tace “you don’t have to tell me anything idan kika gama ina class nidai” dawani kalan sauri Farrah tarike mata hannu ahankali tace “I will tell you everything today Miemie zoki zauna” dawowa Miemie tayi ta zauna tundaga kan haduwanta da Zayn dahau she saves him har zuwa abinda yafaru yau Farrah tafadima Miemie duka, tace “wlh Miemie I hate Ya Zayn sosai banson yanda halinshi yake” girgiza matakai Miemie tayi tace “hate is a strong word Farrah dudda nasan abinda yamiki ranan bai kyauta ba but he was drunk ne daga labarin dakika bani nagane hakan it wasn’t intentional, idan mutum nacikin maye baisan meyakeyi ba, banda hakama are you really blaming him? Look at upbringing nashi so is not entirely his fault, and kinsan mene soyayya na chanza mutum kuma kinsan mutane irinsu Zayn basu iya soyayya ba they use to love with everything dasuke dashi so use that influence and change him” wani kallo Farrah tamata tace “jibi yanda kike magana kaman na gayamiki ina sonshi ne kokuma zan kulashi” tai maganan fuskan Ya Habeeb nafado mata arai, hannunta Miemie takama ahankali tace “loving him or not loving him is entirely your decision to make Fairy, but all I am saying is you are my friend and any abu dakikai choosing I am here for you I will support you okay” murmushi Farrah tamata ta rungumeta ahankali tace “you are the best friend and best sister ever” tureta Miemie tayi tace “kinga gobe zamu gama exam mutafi hutu and is your turn kizo gidan mu kinji” gyadamata kai Farrah tayi tace “naji”, kallonta Miemie ta tsaya tanayi hakan yasa Farrah tace “menene kike kallona haka”? Wani kalan murmushi Miemie tayi tace “kinsan mene wlh Ya Zayn is a very very handsome man, gashi dogo bakin fatanshi kaman na black American, gashi ya iya gayu na yan gayu, gashi dan gata gashi da kudi, kema look at how beautiful you are yaranku ko zasuyi bala’in ky…….” Tureta Farrah tayi tamike tsaye tace “kidaina min maganan shi ni banason shi” tashi Miemie tayi tabiyota dasauri tana kallonta tace “wa to kikeso”? Tsayawa chak Farrah tayi tana tuna how caring Ya Habeeb was to her, da yanda yabata handkerchief ta share fuskanta da yanda ya lallasheta yabari tagama kukan and made her smile kafin ta tafi she just wish deep down inama shine yagayamata yana sonta datafi kowa jin dadi, he’s so caring and so soft towards her, zagayowa Miemie tayi ta gabanta tana kallon yanda yake murmushi tace “wlh kinada wanda kikeso Fairy better tell me, waye shi” akunyace Farrah tawuce tace “bawai ina sonshi bane kuma bawai yace yanasona bane, kawai he’s always in my heart ne sabida he’s so kind and special” hannu Miemie tadaura kan bakinta surprisingly tace “bantabaji kin yabi wani namiji ba Fairy sai yau, ohh my God, this girl is in love with somebody zonan ki gayamin waye” Miemie tabita da gudu hakan yasa suka shiga gudu acikin school suna dariya.

One as usual suka jero itada Miemie zasu gate dan antashi, suna fita hada idanu tayi da Ya Habeeb dake sanye da suit daga gani kasan daga wajen aiki yake idanunshi kur akanta yay folding hannunshi a kirji yana dan zaune gaban motanshi dakenan very clean, wani kalan murmushi tayi tadan dauke kanta tana kallon inda driver ta yake parking ganin bai riga yazoba, hannunta Miemie taja ganin tana murmushi tace “zomuje ki gaida Ya Habeeb tunda ke kunyanshi kullum kikeji” kafinma Farrah tai magana Miemie tajata da karfi sukai wajen motan su suna kaiwa gaban Habeeb dake kallonsu Miemie tace “Ya Habeeb Fairy wai kunyanka takeji” kallon Farrah yayi dake nonnoke kai taki dagokai ta kalleshi tana kokarin kwace hannunta da Miemie tarike yace “let go off her hand Miemie” sakinta Miemie tayi da sauri hakan yasa adan kunyace Farrah ta dago kanta takalleshi hada idanu sukayi dawani kalan sauri ta kauda kanta murya chan kasa tace “ina yini Ya Habeeb” batare daya amsata ba yakalli Miemie dake kallonsu yace “get ice cream from the car” dawani kalan sauri Miemie tai motan shikuma yadan kalli Farrah yace “how you”? Dan dago daradaran fararen idanunta tayi ta kalleshi ahankali tace “fine” yana kallonta still yace “have you cried again bayan ranan nan” akunyace ta langabar mai da kai kaman wata Yar yarinya tareda girgixamai kai alamun a’a, hakan yasa yace “good” daidai lokacin Miemie ta taho dawani paper bag na coldstone ice cream tabashi, karba yayi sannan yabude jakan ahankali yafito da one cup na ice cream yamikama Farrah, dan kallonshi tayi sannan ta kalli ice cream din, gently ta mikamai hannunta ahankali yasa mata ice cream din aciki ta amsa ahankali tace “thanks” sannan yaciro dayan ice cream din dan guda biyu ne yabama Miemie ta amsa da sauri tana budewa tace “thank you Ya Habeeb, ohhh my favorite flavor mint, which flavor is yours Farrah” bude nata Farrah tay ahankali tace “I think is coconut and caramel ko” tadan kalli Ya Habeeb daya gyadamata kai yana kallonta non stop, spoon tasaka aciki tadebo ice cream din zatakai baki kaman yanda Miemie tayi dan tuni ita tafarashan nata kabar da ice cream din akayi daga hannunta, daga cup din ice cream din da spoon din duka suka fadi akasa hakan yasa daga ita har Miemie har Habeeb duka suka dago kansu, Zayn ne yana sanye dawani milk hoodie da dark blue 3quater yasa p-cap dark blue akanshi dawasu dark shade akan idanunshi, lips dinshi sunyi pink yirrr, dudda bata ganin kwayan idanunshi but kasan tsantsan bala’i ne aciki, batare dayace mata kala ba yakama hannunta zai jata dasauri ta fizge hannunta zatai magana yadaka mata wani kalan tsawa da saida ta firgita. “Farrah!” Duka students na wajen da securities kallon wajensu akayi, hakan yasa ya finciki hannunta yajata fuuuu tana binshi abaya da sauri tana waigowa tana kallon Miemie da Ya Habeeb dake tsaye suna kallonsu da sauran yan makaranta, gaban mota yabude Ya wurgata ciki tareda maida kofan yarufe yakoma dayan side din yashiga tareda maida kofan yarufo da karfi sannan yatada motan yawani jaaaa.

Cikin fushi sosai Ya Habeeb yajuya yashiga motanshi hakan yasa dasauri itama Miemie tashiga yaja motan dawani mahaukacin gudu yabi motan Zayn, saida sukai nisa da school sanan Habeeb yawani kalan sha gaban motan Zayn tareda taka burki saura kadan Zayn ya buge motanshi yawani kalan taka burgi saida Farrah tai ihu dataga mutuwa kiri kiri, ahankali ya kashe motan yana kallon Habeeb dake kallonshi shima tagaban motan, Habeeb yakashe tashi motan yabude kofa yafito hakan yasa Zayn shima yabude kofa yafito dukansu biyun suka hadu gaban motocinsu suka tsaya suna kallon juna kaman zasuyi dambe kokarin bude motan daga Farrah har Miemie suke sufito kowannensu yadanna lock a key motocinsu dake hannunsu hakan yahanasu fitowa, cikin kakkausan murya Habeeb yace “what made you think zaka iya duk yanda kaga dama da rayuwan Farrah!” Cikin kakkausan murya Zayn yace “and who do you think you are to her dazaka tareni kanamin tambayan nan”? Dan murmushi Habeeb yayi sannan yakalli Zayn yace “Farrah is my sister’s friend, I take her to be my sister as well, and the way you are treating her is unacceptable, why will you threw away ice cream din datake shirin sha Zayn”? Habeeb yay maganan ranshi abace, hannu Zayn yasa akan idanunshi yazare dark shade din dake kan idanunshi sanan yakalli Habeeb yace “remember what I told you the last time I don’t appreciate when strangers namin magana da kanwa or should I say my wife!” Yay maganan yana kallon Habeeb acikin kwayar idanu ahankali yace “the next time dazan ganka kanama matata magana, ko kallon mini mata I will make sure namaka abu biyu” yay dan shiru sannan yace “first! Saina tabbatar da idanun daka kalleta dasu na tsiyayesu tastas and secondly! I will lock you up in jail for life” yana maganan yajuya zai wuce Habeeb yace “kasan your biggest problem is yarinta Zayn! And yarintar ke deceiving naka yanasa kana tunanin you can mold everybody beneath your feet, don’t mess up with Farrah inba hakaba saina koyamaka hankali” juyowa Zayn yayi yakalleshi from head to toe inda ba bayason yay halin yarintar da Habeeb yagama fadi ba da wlh saiyamai shegen duka akan titin nan, hakan yasa yace “are you that jealous of ka girmeni but I’ve took the gem away, and it belongs to me now? Farrah is mine! Oopsss sorryyy Yaya, hahahah” ya kyalkyace da dariya tareda maida glasses nashi kan idanunshi yasaka sanan yajuya zuwa motanshi yabude yashiga taredayin reverse yawuce Habeeb dake tsaye da mugun gudu, wani kalan dukan gaban motanshi Habeeb yayi zuciyanshi namai zafi, shi he don’t even know exactly meyakeji game da Farrah ko sone ko menene oho, he just hate yanda Zayn keyi, and the last magana da Zayn yagayamai pains him, cikin fushi yajuya yashiga motanshi tareda tada motan batare daya kalli Miemie dake kuka ba ganin Ya Habeeb da Ya Zayn nafada dudda batasan mesuka cewa ba.

5️⃣4️⃣

THIS BOOK IS NOT FREE❌
Wanan littafin FARRAH 500 ne kacal.
Don magana dani M SHAKUR chat me up directly by clicking on this link;
wa.me/+2347012181461

The Wellness by Oriflame routine is designed to support your intake of protein, dietary fibre and micronutrients, in the right proportions, every day.
Chapter 61 · 0% Book details