← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 94

Sashe 6

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

EPISODE 3️⃣
Fizge hannunshi yayi daga hannun Baban nashi yawuce ciki yana tafiya kaman bayaso yayi agadarance Papa yajuya yabishi da kallo kaman baitaba ganin shi aduniya ba. “Yaya” Uncle yakirashi anatse dayasa firgigit yajuyo dasauri yana murmushi yace “kaga yanda Zayn ke kara girma kullum yamafini tsayi fa” dan murmushi Uncle yayi yace “ai tun Zayn na yaro yakeda saurin girma, babu wanda zai ganshi yanzu yabashi asalin shekarun shi 26 saidai adinga bashi 30 sama” sosai Papa yashiga dariya irinta manya yana kara leken Zayn din daya bace musu daga gani, sanan yajuyo yakalli Uncle yace “dan kanina ya akayi”? Yay maganan yana kama hannunshi cikeda so, murmushi Uncle yayi yace “zan wuce gida naje nai wanka nadan kwanta Yaya” cikeda so dakuma damuwa Papa yakai hannunshi kan shoulder nashi yace “you must be extremely tired ai dole ne, stress na Zayn is energy draining, kaje kai wanka kahuta I will see u anjima da daddare kokuma dasafe just take your time kaji idan zakazo ka taho da su Rukayya da yaran suzo su gaida da dan uwansu” gyadamai kai yayi ahankali yana murmushi yace “to Yaya bari naje” gyadamai kai Papa yayi yana sakinshi yace “u can dismiss wayan nan guards suma suje suhuta I will see you later okay” yay maganan Papa yawuce ciki.

Wani gagaruman falo Zayn yashiga yana tafiya kaman bayaso yayi ma’aikatan gidan tundaga nan compound ke zubewa suna gaidashi kaman anga Sarki ko kallonsu bayayi yashige falon abinshi, wata babban mata gatanan fara fat ke tsaye agaban dinning, tana sanye da wani arnen lace dayasha aiki mai suna aiki, idanunta sanye da fararen glasses kar wanda kana ganinsu kasan na kara karfin idanu ne, tana tsaye inda take tanama yan aikin pointing komi da yatsunta dasuka sha jan lalle tana nunamus yanda zasu jera abinci dakenan cikin lafiyayyun kuloli ubansu dakake gani a irin gidajen sarakunan larabawa tabama kofan baya hakan yasa ko kadan bataji shigowan Zayn dinba, kotaji ajikinta ana kallonta ne chak ta tsayar da maganan datakeyi da ma’aikatan sanan ahankali tajuyo kaman wanda wani abu yakirata, chak ta tsaya tana kallon Zayn dashima kallonta yake yana dan murmushi, ance uwa uwace kuma koyaya take dadi ne da ita, ahankali takai hannuwanta ta rungume su a kirji tai jim tana kallonshi daga sama zuwa kasa kaman mai tunanin wani abu tama kasa koda motsi daga inda take tsaye, wani kalan murmushi Zayn yayi dan yasan metake kallo sanan yataho da sauri har zuwa gaban dinning din ya tsaya agabanta yana kallonta yana murmushi ganin yanda tayi yasan fada zatamai hakan yasa kawai yakai hannuwanshi yajawo hannunta dagudu, ware ido tayi tace “mehaka Zayn? Mehaka kake jana”? Saida suka kawo tsakiyan falon sanan ya tsaya yakama dayan hannunta yarike yafara juyata yace “we are dancing Ummi, Ummi I am now taller than you sosai” yanda yashiga juyata yasa idanunta suka fara kadawa dasauri ta fizge kanta tana tangan tangan ta dafa kanta tace “jama’a na shiga uku, sabida kahadiyi kadan jimina kafini tsayi yanzu shine yabaka right kamin juwa juwa” dasauri tazauna akan kujera tana maida ijiyan zuciya, dariya yayi sosai yana kallonta kaman bashine ke kumbure kumbure awaje ba yazo kan kujeran datake yawani kwanta yadaura kanshi kan cinyanta sanan yakama hannuwanta yakai kan fuskanshi yana sauke ijiyan zuciya yace “massage my face Ummi nagaji” yay maganan yana lumshe idanu ahankali tafara massaging face nashi tana kallon gemunshi dayama kala sanan anatse takai hannunta kan gemun takama tarike tana kara tabbatar da kala ne wato tura gemun yayi murya chan kasa tace “Zayn wanan kalan dakama gemunka na menene”? Dan yatsine fuska yayi batare daya bude idanunshi ba yace “Ummi is fashion, bakiga Kenye west ba haka nashi yake” dan jim Ummi tayi sanan tace “Zayn menene abin burgewa anan amatsayinka na dan musulmi, annabi yace duk wanda yaso wasu kokuma yayi koyi dasu to ranan tashin alkiyama tare Za’a tashesu yana cikinsu, waye kuma Kanye west? Zayn haka mukai dakai? Bakamin alkawari zaka dawo yaro mai tsoron Allah ba dakuma koyi da sunnar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi, yanzu when was the last time kadauki Al Qur’ani ka karanta”? Minshari yawani jaaa irin baimasan tanayi ba dinnan kuma tasan sarai yana jinta, ahankali tace “Zayn ina maka magana kana minshar…..” “Why on earth are you disturbing my son Doctor? Daga dawowan shi” sukaji muryan Papa daya shigo dakin afusace hakan yasa tadago kanta dasauri takalli Papa zatai magana yadaga mata hannu alamun tai shiru yakalli Zayn din daya lumshe idanu yace “yaci abinci”? Girgixamai kai Ummi tayi, sosai fa cikeda masifa Papa yace “akan wani dalili zaki tasamin d’a agaba kina damunshi batare dakin ma bashi abinci yaci ba eh Doctor? Kinsan awa nawa yayi cikin jirgi nifa idan bakison yaron nan ni inason d’ana, nakuma san darajan shi, nasan me Zayn yamin, yaron nan yazame mini sila na farin ciki dakuma karin yalwan arziki dan haka kisan yanda zaki dingama d’ana magana, kome yakeso kibarshi yayi yaro ne he’s just 26, nan gaba koda kudi, bama kudi ba kodame zaki hadashi kice yayi shiga haka ko dressing haka wlh bazai yiba komi dakike gani na duniyan nan lokaci ne, Zayn” yakaraso wajen yana bambami yadago kanshi daga jikin Ummin dake kallon Alhaji turus kawai kana ganinta kasan batada tacewa, ahankali Zayn yatashi zaune yana dan bude idanunshi yana kallon Alhaji, dasauri Alhaji ya tallabi fuskanshi yace “kyale Maman ka tacika fitina, ni nasan sabida itane yasa bakasan dawowa Nigeria dan tasamin kai agaba take, yanzu ko zan tsaya tsakin daka babu wacce ta isa tadameka wlh, muje

Muje tabamu abinci kaci, tashi yayi kaman munafuki yabi Papa sukai dinning itakuma Ummi tabisu da kallo baki bude mamakin Alhaji take ba kadan ba, indai kan Zayn ne yiyakeyi kaman wanda akamai asiri, kullum kallon jariri yakema Zayn idan bai bari an tsawatamai yanzu ba yaushe za’ayi. “Zaki bamu abincin Doctor ko muyi serving kanmu”? Alhaji yay maganan rai abace, dan murmushi kadan Ummi tayi sanan tamike tsaye ahankali takaraso wajen dinning din sanan ta zuzzuba musu abincin white rice da fish sauce tun Zayn nakarami yanason abinci, ture nashi Papa yayi zuwa gefe sanan yajawo na Zayn gabanshi yana daukan cokali yace “yauwa lemme feed dan yaro na” tabe baki Ummi tayi idan da sabo tasaba da irin halayen nan na Alhaji, zama tayi anata kujeran ta debi abincinta tafaraci tana satan kallon Zayn din dake yanda yaga dama kafin yaci abincin da Baban nashi ke bashi, kaganshi zaka rantse he’s 10yrs old ne sabida yanda yakeyi, dan girgiza kai kawai tayi aranta tace “Allah ya shirya” Zayn yalalace na karshe mahaifinshi yaki bata daman ta gyara yaron nan tun kafin yakawo haka amman yanzu kam saidai suyi duk fadan dazasuyi zata sakama danta idanu, bude kofan falonsu akayi aka shigo da sallama wasu manyan mata ne su uku gasunan kaman Ummi suma sunci gayu na alfarma suna washe baki, wacce kea gaba ne tace “yau danmu yadawo Zayn andawo laf…..” hannu Alhaji yadaga musu sanan yanuna musu kujerun dake falo yace “ku zauna kujirashi yagama cin abinci sanan ya amsa gaisuwan ku kada kusa ya kware abinci yakeci” yana maganan yajuyo yana kai abinci bakin Zayn din dako nuna alamu baiyiba na yaji matan Babanshi sunzo ana gaidasu ba, Ummi jitayi kaman ta kurma ihu Wanan wani irin wulakanci ne, ko ita akama haka bazata ji dadi ba an shigo da murna Ama danka sannu da zuwa kamusu Wanan wulakancin saikace beggars, ture abincin gabanta tayi tamike tsaye tana kakalo murmushi tana kallonsu sanan tataho falon cikeda mutunci tace “Hajiya Hadiza, Hajiya Fatima, Hajiya Maryam sannun ku da shigowa, bismillan ku kuzo muci abinci please” wacce tafisu kiba duka Hajiya Hadiza ne tai dan yake tace “ahh Alhamdulilah akoshe muke, Sarki mukazo gaidawa daman akace mujira yagama cin abinci” dan murmushi Ummi takara yi sam bataji dadin maganan da Alhaji yagaya musu ba, ahankali ta nemi kujera one sitter ta zauna sanan takalli karaman cikinsu wacce itace amaryan Alhaji bazawara ce ya aureta kusan sa’an Ummi nema ahankali tace “Hajiya Maryam ya zaman kadaici” murmushi tamata dudda yanzu shekarunta biyu da aure amman kowa referring nata Amarya yake duk cikinsu itace mai dan shiri da Ummi, cikeda fara’a tace “lafiya kalau Ummi, Ya patient kuma? Yaushe ne tafiyan dazakiyi na UNICEF”? Dan ajiyan zuciya tayi tace “wlh da badadan aikin taimakon al Umma bane, taimakawa marasa lafiya da magunguna na karkara haka da tuni nafice daga team din UNICEF na Nigeria, aikin nada wahala team dina zamuje kauyuka daban daban guda 10, in 3days time ne tafiyan Allah dai yabamu sa’a” Hajiya Maryam tace “Ameen, Allah ya taimaka” cigaba da hira sukayi dukansu sama sama.
Chapter 6 · 0% Book details