← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 94

Sashe 16

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tana zaune acikin dakin nan nata ita kadai dayake da duhu ko fitila babu tana zaune ta idar da sallan isha’i taji muryan Rakiya ta kwalamata kira cikeda bala’i. “Farrah” tashi tsaye tayi da sauri jikinta harya fara rawa hannunta dasauri takai ta taba goran pepper spray da Shafa tamata dake makale gefen zaninta tana numfashi da sauri da sauri. “Wai bakiji ina kiranki ba Shegiya Yar Jaka nazo dakin nan naki na tumakai kashekine kawai bazan yiba” Rakiya tafadi ranta abace, ahankali tasa hannu tabude kofan taramo tafito daidai lokacin itama Inna dake sallan isha’i lokacin da Rakiya tashigo gidan tafito tana kwace hijabin tana daurawa kan igiyan tsakar gidan tace “meya faru Rakiya”? Cikin fushi Rakiya takalli Farrah daya fito tana rabewa abango daga nesa dasu, Rakiya tace “yau kin hadu da Modibbo kobaki hadu dashi ba”? Da bala’in sauri Farrah ta girgiza mata kai tana hadawa da yatsu alamun a’a basu haduba, cikin fushi Rakiya tadubi Inna tace “Inna kinga dai yarinyar nan da Baba yasaka mana agida bata gabana bana shiga harkanta, wlh Inna takiyayan mini Moddibo na, ko ganinshi tayi tama chanza hanya dan banso ko hanya yahadasu, Inna yau ina kawomiki karanta na karshe wlh wlh na rantse da zatin Allah ko magana aka kara zuwa akacemin anga ta tsaya tanayi dashi koko kima hada hanya dashi komenama yarinyan nan ita taja, komenamata ita taja, Modibbo nawa ne nikadai ne matarshi a kap karkaran nan, idan kunne yaji……” Inna tace “gangan jiki ya tsira” Rakiya tajuya tawuce dakinsu itakuma Inna takalli Farrah da kanta ke kasa tanaji kaman ta kasheta tace “in ciyar dake sanan in ciyar da Baffan ki da kudina sanan kice zaki kwacema y’ata Modibbo Farrah wlh wlh zan iya halakaki har lahira ki kiyayeni” tana maganan tajuya fuuuu tai ciki ganin Malam yaleko daga dakin ahankali itakuma tajuya takoma dakinta tasamu gefe daya ta kwanta sai bacci Allah yasota takoshi.

Da asuban fari ta bude ido tana fitowa ta zaga bayangida sanan tadauro alwala, tadawo dakin ita harta saba rayuwa acikin duhu salla tayi na asuba sanan tazauna tana addu’a, mahaifiyarta kafin tarasu takoya musu karatu sosai dan haka ta iya ta iya salla daidai gwargwado sanan bata wasa da addu’a.
Gari nafara haske tafito ita kadai da sanyin safiyan nan nan tadauki tsintsiya ta share gidan tass, sanan tai wanke wanke, saida tagama sanan tabama tumakan gidansu da shanaye abinci daidai lokacin Inna tafito daga daki fitowa tayi daga wajen tumakan ta tsugunna har katsa alamun gaisuwa ko amsata Inna batayiba tawuce bandaki itakuma tadauki tulu dan fita debo ruwa rafi tanada kuzari da zafin nama nan da nan tashiga cike ko’ina, tana cikin tafiya zata koma rafin zuwan karshe kenan zatayi ko’ina yacika agaban rafin taga Modibbo tsaye rikeda wani paranti mai kyau da buredi kekai da kofi babba dayacika da shayi sai cinyan kaza agefe soyayye dakuma soyayyan kwai, kallo daya tamai tawani irin juya, dasauri yabiyota yace “Farrah Farrah tsaya” tana shirin kwasa dagudu yasha gabanta yana kallonta yana murmushi yabi kayan jikinta da kallo sunyi daka daka dan tabe baki yayi yakalli fuskanta dahar wani sheki yake dudda ko wanka ma batayi ba ga uban gashi a goshinta da giranta baki sudik har wani kyalli suke yace “bakiji ina kiranki bane zaki gudu, Kari nakawo miki nasan ba’a baki abinci awanan gidan bani tulun nan kigani” yakai hannunshi zai sauke tulun daga kanta dasauri takoma baya tace “iiiiii” cikin yanayi na kurmanci alamun yabar shi, jiyayi ranshi yabaci daurewa yayi yamika mata tray din yace “to gashi kici” dauke kai tayi takalli gefe dasauri dan bamataso taga abincin ranta yabiya, sosai yaji ranshi yabaci cikin fushi yace “wlh idan baki amsaba zansa akulleki amiki bulala dariya wawiya kawai sabida kinga ina sonk……” “Farrah” wani irin bari jikinta yayi jin muryan Rakiya daga ita har shi Modibbo juyawa sukayi suka kalli Rakiya, kana ganinta zakaga tsantsan bacin rai da kishi a idanunta dan takai minti daya tsaye a wurin amman ta daure dasauri takaraso wajen Farrah tai baya dasauri danta dauka dukanta zatayi Rakiya tasa hannu ta amshi tray dake hannun Modibbo tace “Allah sarki Hamma haka kake sona kabama Farrah takawomin gida, gidan su Atine fa zani nace bari nabiyo tanan, nagode Hamma Modibbo” tai maganan tana amsa tana juyawa dantama Farrah mugun kallo amman harta bace daga gudun, juyawa Modibbo yayi fuuu yawuce batare dayace ma Rakiya uppan ba, saida yabace mata sanan tai kwafa tawuce gida.

Awani irin zuciye Rakiya tashiga gidansu tana ihu. “Farrah, Farrah” Inna datagani na rege shinkafa atsakar gida tace “Inna ina Farrah”? Baki Inna ta tabe tace “kinfasan tunda tagama gyara gida ta debo ruwa sai kwasan awakai da shanaye ta wuce daji kiwo ko Rakiya baki sani bane? Me Wanan ahannunki” ko kallon Inna batayiba tajuya tawuce tashige dakinsu.

💫 FARRAH 💫

✍🏻M SHAKUR

Littafin nan is 500 pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank Saiki turomin evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting.

EPISODE 9️⃣
Tunda aka haifeshi yataso yafara wayau baitaba shiga wani yanayi na azaba dazaisa harya furta sunan mahaifinshi ba sai yau, yanada gatan dakome yakeso basaiya fadi ba za’amai, kafin yay tari anmai providing, baitaba shiga wani yanayi dazai kira mahaifinshi ba dan mahaifinshi has always being there for him kafinma ya nemeshi, yau shine dayaji azaban karya kashin hannu da idanunkashi biyu kuma yana cikin hayyacinshi bawai anmai anesthesia bane kowani abu ba baisan lokacin da bakinshi yafurta. “Paaa….paaa!” Da bala’in karfi hawaye na tsantsan azaba na zubomai, dariya gardawan sukahau yi babu ko alamun imani a tattare dasu sukace “sannu yaron Papa, ko Papaya kakira yau ba Papa ba bazaijika ba” sukai maganan suna haska fuskanshi da tocula dan duhu yasomayi amman tuni yasume sai hawaye dasuke kan fuskanshi nan fresh ganin haka yasa suka koma wajen Boss dinsu dake waya, juyowa yayi ya katse wayan dayake Lamido yace “Oga wai yaya ake ciki ne”? Dan ajiyan zuciya yasauke yace “sunce nabasu awa ashirin da hudu, yisu yisu su ukun sun kasa tantance abinda sukeso na akashe yaron ne koko abarshi da ranshi ne, kuma uban yaron da shine kadai zai iya bada order kudi idan muka kira ya gigice yana asibiti anyi kidnapping rayuwarshi wanan katon banzan dakuke gani, nidai nabasu 24hrs din, inhar basuyi making decision ba suka bani order kiran uban yaron ba dan Billyan dari nakeso yabamu toni kashe yaron zanyi asalin aikina najirana chan, bazan wuce gobe agarin nan ba saina kammala aikin nan, kuma bayan na kashe shi ko sunaso ko basaso saisun biyani kudin aikina da resources dina da akai amfani dashi inba hakaba suma sun sanni shi kidnapper baida amana dan tonamusu asiri zanyi ku yageta kawai” Lamido yace “bakada case Oga kome kace ayi hakan zamuyi bamaja dakai” yay maganan da muryan nan nashi irin na yan wiwi dinnan, murmushi Ogan yayi yanajin dadin aikin Lamido, dan sosa kai dayaga Lamido nayi yasa yace “ya akayi dawata maganan ne” dan yake Lamidon yayi yace “ahhh Oga dama nazo nadan zaga dajin nanne naga kaman akwai rugan fulani kusa sonake naje nasamo mana taba sanan idan akwai bani (yammata) nadan girgije nasa chaji kagane ai Oga eh yane” dariya Ogan yayi yana zare safan fuskanshi yace “dakai da Lamba kuje, Sagir yazauna gadin wanchan yaron kada kubata lokaci” angama Oga yay maganan yana cire tashi safar fuskan shima Lamba da Sagir duk suka cire sanan suka wuce shikuma Sagir yatafi gadin Zayn dake baccin wahala anan kasa kan ciyaye.
Chapter 16 · 0% Book details