← Book details Farrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 94

Sashe 23

Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

EPISODE 1️⃣4️⃣
Sai bayan sallan isha’i Mami da Alhaji suka taho dakin da Farrah keciki, ganin babu Malam adakin yasa Alhaji yace “why is she alone ina Uncle natan yake”? Yay tambayan yana juyawa baya, bodyguard dinshi dake biyedashi yasa kiran security itakuma Mami tai gaban gadon tana duba vitals din Farrah, shigowa security yayi Alhaji yace “ina Uncle dinta yake ko yaje masallaci ne”? Girgiza kai security yayi yace “I think he left” ko ita Mami dake shirin yima Farrah allura saida takalli security dasauri tace “left kuma”? Gyadamusu kai yayi yace “after kince I should keep an eye on him daya fita nabishi, anan gaban asibiti yatare mota yace akaishi tasha” dan murmushi Alhaji yayi yakalli Mami yace “are you sure dan uwanta ne kuwa”? Gyadamai kai Mami tayi tace “eh, I think she’s a burden to them saisa daya sami kudi ya gudu, ko dazu I told the security to keep an eye on him cus I get this feeling kaman baiso tai surviving ba” girgiza kai Alhaji yayi yace “mutane kenan basusan yara rahama bane, Allah ya kyauta, how is she yanzu?” “She is fine, I will stay with her saika tafi gida da Zayn ko” gyadamata kai yayi yace “okay, I will tighten the security here no more taking chance dan kowaye keson hurting dina yanda Allah bai bashi galaba kan Zayn ba bazai taba hutawa ba sai burinshi yacika, be careful okay, if anything come up ki kirani” gyadamai kai tayi tana murmushi shima murmushi yamata sanan yawuce yafita zuwa dakin da Zayn yake, har yay wanka ya chanza kaya zuwa wasu simple top da short masu kyau farare dasuka bala’in amsanshi, yasaka wata dark blue wool hula dayama fuskanshi kyau ka kalleshi saika kara kallonshi, farin designers socks yasaka dawani vintage slippers mara hanci kana ganinshi kasan sanyi yakeji, babu abinda yasami idanunshi amman saida aka wanke idon akai plasta gobe zasu dawo abude idanun, murmushi Alhaji yayi ganinshi yanda yay kyau dudda har yanzu bai dawo daidai ba jikinshi ya bala’in nuna yaci duka sanan ya wahala, hannunshi Alhaji ya kama yace “let’s go home, but first muje kama maman ka sallama ko” cikin Wanan muryan nashi na baison yin magana yace “is she not going home da mu”? Girgizamai kai Alhaji yayi yace “nooo, Uncle na yarinyar yagudu cus I gave him 10M, kasan ur Mom is the most generous woman dana sani aduniyan nan, she offers zata zauna da yarinyar” shiru Zayn yayi bai kara cewa komiba, hannunshi Alhaji yaja yace “muje to” binshi yayi suka fara tafiya tare ahankali har sukakai dakin.

Budemusu kofa bodyguard yayi suka shiga cikin dakin daidai lokacin Farrah ta kwaye baki tafashe da kuka cikin bacci batare data bude idanunta ba, ahankali tadaga hannunta takai inda akai mata aikin aka rufe da plasta tafashe da kuka sosai cikin wani kalan siririyan murya da dakin yake echoing yana amsawa idanunta a lumshe har lokacin tana kokarin sosa wajen da aka mata aikin.

Dawani kalan sauri Mami dake zaune kan kujera ta tashi hannunta tasa da sauri tarike hannun Farrah datakai wajen tace “Allah sarki sorry, sannu kinji yafara mata zafi wajen, alluran yafara sakinta sannu karki taba” kara karfin kukanta tayi dayasa for the first time Zayn Zayn da suna shigowa dakin yanemi waje kan coach na dakin ya zauna yana danna sabuwar wayan da Baban shi ya kawomai dan dayan tabace yadago kanshi, gently kaman wanda bayaso yadaura idonshi akanta, blue operation net cap din da aka samata yadan zame baya haka ya bayyanar da dark curkudadden black hair dinta, gashin goshinta sun kwanta tass tass sunyi wani kyau, kodan sabida kalan hasken wutan dakin ne oho but wani kalan haske tayi sosai kaman baturiya idanunshi a rufe ruf amman lafiyayyun hawaye ne ke fitowa daga cikinsu bana wasa ba, wasu nabin gefe suna hanyan kunnenta wasu na gangarowa kasa, dogon hancinta har kyalli yake sabida maiko, ta tabe baki sosai irin yanda bakin mai kuka keyi, lips dinta sun tattare sun bushe sunyi pink yirrrr, baisan mesa ba tunda yake arayuwanshi baitaba jin urge na kaman yacema mutum sorry ya lallasheshi ba sai yau, kaman tausayi tabashi ne ko she looks innocent ne oho, ganin understand what exactly yakeji is hard for him yasa yadauke kanshi da sauri kaman ance yadaina kallonta yamaida hankalinshi kan sabon wayanshi yana daddannawa.

Dayan hannunta tadaga zatakai kan ciwon jin anrike hannunta tana kuka sosai Mami tasake rikewa hakan yasa da sauri Alhaji yazo gaban gadon yace “mesa takeson ta taba wajen aikin”? Murmushi Mami tayi tamikamai hannunta daya tace “tayani rike hannun nan kaga” karban hannun Alhaji yayi yarike yana kallon Mami, Mami takai hannunta kan fuskanta tashare hawayen dake gangarowa sanan ahankali kaman mai whispering tace “dazafi”? Gyadamata kai Farrah tayi ahankali still idanunta a rufe, satan kallonsu Zayn yayi saikuma yasake dauke kai, ahankali Mami tace “kin tashi”? Gyadamata kai tasakeyi kaman Yar yarinya alamun eh, murmushi Mami tayi tace “meke miki ciwo yanzu to”? Shiru tayi batace komiba cikin lallashi kaman tana magana da Yar yarinya Mami tace “fadamin sunan ki inji” shiru tayi batace komiba still. “She can’t speak” Zayn yafadi ahankali batare daya kallesu ba yana danne danne awayanshi, daga Mami har Alhaji dasauri suka yakalleshi, Alhaji yace “kaman ya she can’t speak”? Dan yatsine fuska Zayn yayi batare daya kallesu ba har lokacin yace “she is dumb Daaaad” yay maganan irin yafara gajiya da tambayan su dinnan, “kurma”? Alhaji yafadi dasauri, gyadamai kai Zayn yayi yadan kallesu yace “the girl that was with her told me she can’t speak at all” maida hannunta Mami tayi da sauri ta ijiye akan gado, sanan tajuya da sauri tafita daga dakin batare datace musu komiba, bata wani jimaba tadawo dawani torchlight karami a hannunta, fuskan Farrah ta taba ahankali tace “Farrah” dan motsi Farrah tayi, murya chan kasa Mami na shafa gefen fuskanta tace “budemin bakin ki nagani” tai maganan tana bubbuga gefen fuskanta dan har yanzu bata gama farfadowa daga alluran ba, ahankali tabude bakinta, haska bakin Mami tayi saida takoma baya hakan yasa da sauri Alhaji dake tsaye kusada ita yace “menene”? Ajiyan zuciya tasauke sanan tama Alhaji alamu da idanu yazo yagani sanan yakoma baya yace “why is her throat that black”? Maida mata bakin Mami tayi tarufe sanan cikin harshen turenci tace “this girl has been suffering, this is clearly a child abuse case, Alhaji kaga tabobin duka ajikinta kuwa? Kaga bakin nan nata garwashi aka samata awuya is not like she can’t speak, ita kanta batasan she can speak ba sabida tsoron azaban datasha lokacin da aka samata garwashin” yanda idanun Alhaji sukaija zakasan ranshi yabaci ainun, cikin fushi sosai yace “me wanan Yar karaman yarinyar tamusu daza amata irin wanan zalincin garwashin wuta a wuyan mutun? Eh? Sunsan menene y’ay’a kuwa sunsan cewa rahama ne su, why will people be so wicked and cruel, wlh wlh saina kullesu, zasu fadamin meta musu aka mata haka, let’s go Zayn” sanan yajuyo yace “make sure taji sauki kinji wife” gyadamai kai tayi sanan suka fice yarufo kofan itakuma Mami ta zauna ahankali kan kujera tai folding hannunta akirji tana kallon Farrah, batasan kodan sabida ta taimaki Zayn bane but hakanan taji she’s growing strong affection for yarinyan, ga yarinyan is so fine, very fine beautiful girl, gata Yar karama duka duka yarinyar nan bazata wuce 17/18 ba,how can you be wicked to this small girl.

Wani kalan kuka Farrah tafashe dashi sosai cikin baccin dayasa Mami takara tashi, hannayenta takama ahankali tana kiran sunanta. “Farrah, Farrah, gani nan” wani kalan yunkurowa Farrah tayi cikin bacci tawani kalan rungume Mami kamkam cikin wata kalan little voice tace “uhnnn Maa….m” wani kalan lumshe idanu Mami tayi ahankali takai hannunwanta tadaura abayanta tana bubbugawa jin takirata da Mama almost 1min sukai ahaka sanan Mami tamaidata ta kwantar da ita, murmushi tayi taja bargo tarufa mata da kyau sanan tawuce bayin dakin alwala ta daurOo tazo tasa hijabi ta shimfida dadduma tai nafila sanan ta kwanta akan lafiyayyen massaging chair dake dakin ta Minat da kafafunta.
Chapter 23 · 0% Book details