Sashe 2
Farrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Shigowa gidan yayi bayan yay sallan la’asar, Farrah dake kwance asume inda take a kitchen yabida kallo yana tafiyan nan kaman iska zai kwasheshi yafadi tsabagen rama sanan yashiga dakin, Inna dake zaune atsakar falon ta bishi da mugun kallo dan kaman tashakeshi takeji, wata Yar karaman radio dake kan Yar kodaddiyar tv su yadauka yana jawo antenna radio waje sanan ya kunna yana murza tasha yana kokarin kamo tashar BBC, Inna dake ballamai harara tace “tirrr wlh kayi asara arayuwanka mai mataccen zuciya kawai” sake tabe baki yayi sanan yadauki taburman dake nannade an jinginar dashi a tsaye gefenta yawuce yafito cikeda cin zarafi da mugun son yakulata tace “nagadai tabarman ma tawace nina saya mara zuciya” shimfida tabarman yayi agaban dakin sanan ya ijiye radio yamike tsaye yasake kallon Farrah a inda take sanan yawuce butanshi dakenan inda yabarta anan tsakar gida dazun dayay alwala yakarasa yadauka dayake da ragowan ruwa aciki yana kara girgiza butan dan gane iya ragowan ruwan dayake ciki sanan yawuce inda take ya tsaya a kanta dan kallonta ya tsaya yanayi yay jim kaman mai tunanin wani abu rabon da yadaura idanunshi akanta wlh yama manta hakanan ganin fuskan marigayiya kanwarshi yayi kaman ita lokacin datana sa’an Farrah, girgiza kanshi kawai yayi sanan yadaga butan yashiga tsiyaya mata ruwan ciki kan fuskanta yana kiranta. “Ke, Farra’u, ke!” Yakirata da karfi ahankali tashiga motsi tana yatsine fuska jin ruwa akanta saikuma kaman wacce aka tsungula tawani mugun zabura tamike tana kara wargaza tukwanen dake wajen tana ihun kurame dayar muryanta, Malam daya bita da kallo yace “zakici gidan ku ne, da idanuwanki kaman na shaidanun ruwa, ko agidan wa kika koyo sata kije ki zubar dashi gidan nan kasheki zasuyi kikace sata zaki dinga musu, yo ke bakima tausayin kanki Iyye, jibi jikinki babu nama kodaya, bakida suturan arziki, tsabagen bakin wahala abinci sai wanda aka yammiki kuma kice zaki dingawa masu ciyar dake sata, Farrah anya kinason kanki kuwa da zaman lafiya”? Gyadamai kai tayi ahankali tana goge hawayen dasuka zubomata da bayan hannu kanta akasa dan itama bata iya kallon Malam, binta yayi da kallo daga sama har kasa yace “wuce ni ki zubamin abincin naci kirufe tukunyar dakika yadda marfin akasa” kaman jira Inna take azuciye tafito daga dakin tazo kitchen din tana tafi tace “wlh bazaka cishi ba Malam, mai tauraro kasayamin koko ajino moto eh? Sule biyar dinka babu a abincin nan dan haka wlh barakaci shi ba, kekuma dan ubanki kwarto dahar yau baki sani ba idan kin isa kitaba abincin nan kiga idan ban guntule wayan nan fararen hannuwan naki ba” dukawa Farrah tayi tana sunnar da kanta kasa tana kulle idanu jikinta na kyarma bala’in tsoron Inna take, inhar tana gidan batada kwanciyan hankali, dan kallon Inna Malam yayi sanan yadan saci kallon tukunyar yanda yaga shinkafar tai jajir yaji ranshi yakara biyawa bazai iya mata zuciya ba cikinshi yashiga kugi, dan murmushi yayi yakalli Inna yace “wai Kodai yau matan mai gari basu biyaki kudin aikatau bane naga ranki abace ne Basirata” harara ta ballamai tace “kanka akeji munafuki” tajuya zata wuce dasauri ya chapke hannunta cikeda muryan lallashi da lallabawa yace “yakuri dan Allah ki zubamin shinkafar nan wallahi yunwar tsiya nikeji” fizge hannunta tayi tace “bakariga kajita ba, bani kazauna kake gaggayama maganganu ba sabida wanan shegiyar kurman beben yarinyan dabata da amfanin duniya balle nalahira yanzu ai saikaci babu kokuma ita taje tanemo tadafa tabaka kaci” gabanta yasha dasauri yakalleta cikeda so yace “haba mana Basira, naface kiyakuri fa, kizubamin naci fita zanyi naje wajen Luku zandawo da kudi kinji” dauke kai tayi tareda rungume hannayenta aciki, washe baki yayi ganin yasoma shawo kanta yace “haba surukan Mai Gari, Maman mai farin jini ke bakiga yanda akema yarmu Rakiya layi ba, saisa nima nai na’am da dan Mai Gari zata aura kaman yanda kika fadi, yarinyar ki saidai mahassadi eh Yar matata, bakiga Rakiya ba jajur da ita uwa hurun ini” wani kalan washe hakora Inna tayi tace “yo ai har yanzu batakai Farrah ja ba saisa nasayo mata wani mai akasuwan gabari nasa tana shafawa, ance idan ta shafa zata kara haske fatar nan tai jazur, wanchan Yar kam saisa nake tabbatar data wuni aikatau arana sabida ta dafe tai baki, bata isa ta kwacema y’ata farin jini ba, bebiya kawai” takarashe maganan tana zubawa Farrah dake tattare tukwanen wajen harara, sanan tai wani irin murmushi tayi tana juya idanu, Malam dake kallonta kaman solobiyo yakara make murya yace “to adan zubo min” juyawa tayi tana murmushi tace “gobe ma ka karamin rashin kunya zanga mai baka abinci Malam” tawuce kitchen din ko kallon Farrah batayiba tadauki kwano a kwando tadeboma Malam shinkafar ranta nakara baci sabida yanda Farrah taci shinkafar sanan tarufe tukunyar tajuyo tace “kitashi kiwuce ki debo ruwa kicike kowani tulu na gidan nan inba hakaba nalahira saiya fiki jin dadi Al Qur’anin ubangiji” sanan tawuce takaima Malam abincin tazauna kusa dashi suna zance.
Ahankali tamike tsaye wani babban tulu tadauka tadaura aka sanan tafito daga kitchen din wani cinyayyen sidadden silipas wari daban daban tadauka a tsakar gidan tasaka sanan tawuce tafita daga gidan, daga Malam har Inna babu wanda yadagakai yakalleta.
Dasauri take tafiya abinta as usual dan sotake tagama cika ko’ina kafin mangariba tayi dan ba’a zuwa rafin idan Magrib yayi kuma rafin yamafi rafin wankinsu nisa, tayi tafiya mai tsawo kaman daga sama taji ankirata. “Ke Kurma” chak ta tsaya tana kalle kallen ko’ina babu kowa a hanyar, wani kalan murmushi tayi dayawani irin kawo cikakken annuri fuskanta cikeda kokarin son tai magana dan ga dukkan alamu tasan waye yakirata tace “taaaaaa…ffff….fa” wani irin dirkowa wata yarinya Yar matashiya tayi daga bishiyan mangwaro dake gefen hanyan da Farrah ke tsaye tana sanye da zani da riga na fulani kanta da dankwali baki na silk kana ganinsu kansu daya itada Farrah saidai tadanfi Farrah tsayi kadan itama farace sol kana ganinta kaga cikakkiyar yar fulani, wani kalan murmushi tayi takaraso gaban Farrah dake kallonta tamikamata mangwaro daya itama tarike dayan na hannunta tace “waike Kurman nan nace dole saikin kira sunana ne, barakije kiji da Kurmancin kiba iyye, sunana Shafa, ba Taaaa….ffff…..fa ba koyayama kike kiran sunan oho miki yar rainin wayau kawai” wani kalan murmushi Farrah tayi da saida ita kanta Shafa ta tsaya tana kallonta hakan yasa Farrah tahadiye murmushi da hannu tamata alamun me?, girgiza matakai Shafa tayi sanan ta tabe baki tasa hannunta daya takarbe tulun daga saman kanta tamaida nata kan tace “ni tausayi kike bani, muje naraka ki debo ruwan, rikemin mangwaro na nidai” tabata mangwaron dasauri takarba tana murmushi suka wuce, Shafa tace “Modibbo yakara tsareki a hanya”? Girgiza mata kai tayi dasauri alamun a’a, Shafa tace “yawwa, duk randa yakara tsareki karki nuna kina tsoronshi kawai kice yakiyayeki bakison matsalan su Rakiya, kindaisan yanda Rakiya keson Modibbo, ki kiyaye su” Gyadamata kai tayi alamun to tana murmushi duk kauyen nan Shafa kadai ce kawarta ita kadaice mai sonta, Shafa akwai baki kaman reza, gata da karfi tasha shiganma Farrah fada, har Rakiya tama duka akan Farrah dan ta tsani yanda ake wulakanta yarinyar sabida ita Kurma ce batada uwa da uba akauyen, son datake mata ne ma yasa bata taba kiranta da asalin sunanta Farrah saidai takirata da Kurma dan kowa yaji yes Kurman kauyensu ce kawarta. “Ke Kurma” Farrah taji ankirata dasauri takalli Shafa dataga tana kallon gabansu, ganin wasu maza su kusan shidda gaban rafin suna zazzaune sun zagaye murhu suna dafa shayi yasa Farrah ta tsaya chak batare data kara tafiya ba kanta akasa, binsu da kallo itama Shafa tayi su Modibbo ne da abokanenshi suna dafa shayi gashinan farare dogaye kana ganinsu kaga yan fulani duk sun dago suna binsu da kallo suma, dauke kai Shafa tayi tajuyo takalli Farrah, hannunta tasa takama hannun Farrah tace “muje kinji Kurma” binta Farrah tayi gabanta nafaduwa dan ko hada hanya tayi da Modibbo bala’i yake zaman mata agida.